← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 76

Sashe 73

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  na marairacewa na ce" Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana."
Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faÉ—in" Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne.
"Da gaske take yi."
In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi.

"To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne?

Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce" Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana."

"Oh."

Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa" Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya."
Rahila ma ta amsa da cewa" Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba."
Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce" Shike nan ma an kashe boss ɗin."

Muna ta dariyan mu cikin nishaÉ—i. Daman fa ko haÉ—uwa aka yi waje É—aya Ma'u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waÉ—anda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana É—akin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma'u ta kwashe da dariya ta na faÉ—in" Kuma kamar kin san ta yi yaye ba."
Ya Aina ta ce" Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe."

Ni kuma sai na kada baki na ce" Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. "
Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin" Su Anti an zama yan mata."

Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce" Anty Sadiya ina goron sallah na."
Kai tsaye na ce" Gorom sallah kike so?
Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce" Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye."

Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce" Kai Anty Sadiya."
Nima ina mata dariyan na ce" Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi."
Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba.
"To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma'u na yi shi ya sa."
Ina mata mirmishi na ce" To ai shiken nan na ma san Ma'u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko?
Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri.
Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga É—akinta.

"Ke Sadiya.."

Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaÉ—ai ba hadda Gwaggo.

"Me ya faru Ya Murja?

Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin" Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa' ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya."
Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa" Murja me kuma ya kawo wannan mganar?

A fusace ta ce" Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma'u ba. Duk na fahimci mganganunta."
Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce" To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da Æ´a."
Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce" Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma'u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma'u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa'ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma'u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya"

"Murja me ye haka don Allah.?

Ya Aina bayan ta fito daga É—akin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma'u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana.
"Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba."
A fusace Ya Murja ta ce" Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je."

Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta É—oramin karan tsana.
Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma'u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma'u  duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci."

  Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce" Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa."
Ganin ban kulata ba ya sa ta koma É—aki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na É—auro alwala na shigo cikin É—akin ne Ma'u ta ke ce min" ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.'

Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma'u ne ban gani ba sai kawai na ce" Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni."
Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne?
Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce"Kai. A ina aka samo abinci nau'i nau'i haka kamar an samu sabon restaurant?

Rahila ce ta faÉ—a masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faÉ—in" To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family"
Ya Balki ta ce" Mun É—auka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida"
Chapter 73 · 0% Book details