← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 76

Sashe 44

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haushin aikin dake gabana ya sa ban ko yi ma Gwaggo magana Hajiya ce ta kashe radiyon ta na faɗin" Me ya faru ne? Ke Dubu ina kallabin ki? Sai a lokacin na taɓa kaina ba ɗankwali ina tura baki na koma na ɗauko a saman gadonta da ya saɓule na ɗaura na fito dai dai Hajiya na faɗin" Dare ya yi ina su Asma'u ne? Su kama mata su yi girkin tare.'

Jin haka sai na washe baki amman sai Mama ta ce" ƙyalata ta Hajiya. In na su aikin ne tana ɗaki kwance kauda kara ba za yi musu ba. Sai su ne za a ce su yi mata na ta aikin? Sai murnata ta koma ciki sai dai Hajiya ta sake ƙwatana da ta ce"Ita ai ba yanayin su ɗaya ba. Tun da sun fita zafin nama ai ba a zauna a zama ɗaya ba."

Jin haka yasa na miƙe da karsashina saboda na san in su Rahila suka dawo sai Hajiya ta yi musu mgana sun tayani. Icce na haɗa na ɗora Tuwo Mama na ta faɗan in ina girki har jajjage ita ke yi mini kawai na fito na ɗora ina jin ƙyashi na duba har wanke wanke da sharan tsakar gida da Amina ce ke yi sai da ta yi kafin ta fita sai ni da in dai ina da aiki sai ran kowa ya ɓaci ina cikin madafi ina tura baki amman raina fes domin na samu raran kuɗin cefane Alhajimu 2k ya ba ni kayan Miya kawai na siya kashi daman yaya Muntari ya kan tura ma kuɗi in dai za a yi miya ya siyo. Kuɗin cefane ke saka ni farinciki in ranar aikina ya zagayo amman bayan haka yini na ke yi cikin baƙin ciki sai na ji gabaɗaya duk na gaji kamar mahaukaciya haka nake komawa a irin yanayin ana takata sai na yi sati ina gaba da mutum.

  Ana kiran sallar mangariba su Rahila suka shigo. Gwaggo sai da ta yi musu faɗan da Alhaji ya shigo fa. Ma'u ce da yanayin mganarta ta ce" Mun taso da wuri Gwaggo rashin abun hawa ne."
Ina madafi ina talge da fitila a hannuna ba wuta. Na gama kenan na rufe na fito nepa suka kawo wuta. Miya ta isa kaɗi har na kwashe ƙashin ina fitowa Rahila ta kalleni yadda na yi kaca kaca kafin ta ce" Wai ke ba ki gama tuwon ba daman?

  Wani kallon tara saura kwata na yi mata na wuce ta. Ba domin ta matsa ba sai na bangajeta. Ma'u  wajen rijiya ta nufa bayan ta miƙa ma Amina Hijabinta ta kai mata cikin ɗaki wajen Hajiya na nufa ta miƙe tana kwashe tabarma tun da an kira mangariba raɗa na yi mata a kunne.

"Hajiya ga su Rahila nan."

Sai ta kalleni kafin ta juya ta na kallon Rahila wacce ke mgana da Ma'u.

"Rahila da Asma'u in kun yi sallah ku kama ma Dubu aikin nan ta gama kafin Sule ya shigo."
Rahila ta amsa da to amman Ma'u sai da ta kalleni nima na kalleta gwalo ta yi minibni kuma na ɗauke mata kai na koma kitchen. Gwara na kaɗa miyar da kaina na bar musu su ƙarisa tuwon. Sai da na kaɗa miyar na sauke sai na saka ruwan wanka ni kuma na je na yi alwala saboda ma ba na son mgana a ɗakin Hajiya na yi sallar mangariba na kuma yi zama na ƙarshenta dai Rahila da Ma'u suka ƙarisa tuwon Alhajinmu ya shigo gida bayan isha'i lokacin ina wanka a bayi daman ina ta Allah Allah na gama na fito kar ya dawo.

  Ina fitowa yana tsakar gida an baza masa tabarma. Na so na yi saɗaf na shige ɗaki amman hakan bai samu ba sai da ya ganni.

  "Dubu"

Dole na amsa ina kallon shi faɗa ya fara min na wankan dare wannan karon ma Hajiya ce ta fito ta ƙwace ni.

  "Sule ka ƙyale yarinyar nan. Yau fa a tsaye ta yini tana aiki har daren nan gwara ta yi wanka ko ta ji daɗin barci."

  Alhajinmu ya yi shuru amma Mama sai da ta ce" To ta riƙa yin aikin ta da wuri mana. Sadiya son jikinta har bani tsoro ya ke in ta yi aure ban san ya za ta yi ba "

Alhajinmu sai da ya yi dariya kafin ya ce" In ta ga ta samu É—akin kanta za ta yi ne Rukayya. Nan saboda ta ga akwai su Asma'u ne in ba ta yi ba su za su yi."

Ni dai na samu na shige É—akinmu tunda nan ya fi kusa ina shiga na ga Rahila da Ma'u ana ta hiran bikin da suka je. Na yi kamar ban gan su ba mai na É—auka na shafa ina da sauran kaya a É—akin na buÉ—e jakar Rahila na É—auko wata rigata na saka kafar Ma'u na wajen da gangan na taka ta saboda na ga ita ba makauniya ba ce ta na ganina a wajen ba ta janye ba.

"Dutse kika taka hala?

A sakarce na kalleta kafin na ce"Wataƙila."
Ta yunƙuro za ta yi mgana Rahila ta hana ta da cewa" Kyale ta Ma'u. Ke kuma Sadiya don Allah ki koyi zaman lafiya."
Na kalli Rahila kafin na taɓe baki ina faɗin" Sannu yar koran gimbiya."
Haka na ke ce mata in na ga tana haƙiƙancewa akan lamarin Ma'u. Wani lokacin Rahila ba ta cika ban mamaki ba irin Yaya Abubakar bai ɗaukan lamarin Ma'u da sauƙi amman ina masa uzuri makauniyar soyayya ce ke damun shi.

   Tun bayan dawowar Hajiya kano rabon mu da garin Yashe amman dai su Baba Aminu suna zuwa duba Hajiya in kuma wani sha'ani ya tashi ƙwansu da ƙwarƙwatan su. Ma'u dai ta manta da gidan tsoho ba zuwa take yi ba. Kuma ni dai ban taɓa ganin wani daga cikin dangin babanta ya zo nemanta ba. Amman tana zuwa kura wajen Baaba itama Baban na yawan zuwa kuma duk saboda Ma'un ne. In ta tashi zuwa tare da Rahila suke zuwa ni ko in yi zamana a gida ban taɓa marmarin zuwa ba. Tun da na fahimci Baaba ba ta ƙaunar uwata nima daga ita har yarta ba na som su tun ballatana da na fahimci Baaba na da son abin duniya.

  Ko irin a makaranta ƙawaye an sha zama kowa na faɗin irin ra'ayin mijin da zai aura ni ba na mgana saboda ra'ayi na ya bambamta da na kowa. A lokacin maza ba sa gabana duk da an sha tare ni a hanya ban taɓa maida kai ba saboda har a lokacin ban sami irin zaɓina ba.
Rahila kuma daman na fara zargin suna soyayya da Yaya Muntari. Na daɗe ina mamakin shi so daman haka yake? Saboda Ya Muntari gajeren namiji ne kuma baki sannan yana da barkwanci ni dai ban ga abin so a wajen shi ba anawa tunanin kenan Ma'u ko an taɓa tare ta a hanya muna tare ta ce ita ta na da miji. Buɗe bakin Rahila tana dariya sai ta ce.

"Yaya Abubakar ba. Na sani kun dace kwarai Ma'u."
A lokacin Ma'u ta kasa yin gaddama amman yanayinta ya sauya ni kuma ina gefe ban ce komai ba a raina na ce maji ma gani an tura uwar amarya biko. Kuma gashi Ma'u da jinin masu kuÉ—i amman ba ta sauraran kowa ni dai masu cewa suna sona daga malaman islamiyamu sai na boko ita kuma Rahila gajerun maza kamar Yaya Muntari da ta sauya ma suna zuwa Yaya Muktar.

Shekara ɗaya ta shafe tuni har mun zana jarabawar fita babban sakandiri a ƙarshen shekaran  2000 sai dai dukkanmu ba wacce ta ci sai mu ka dawo zaman gida. Lokacin Yaya Abubakar da Yaya Hamza sun gama karatun su suna hidimar ƙasa. Shi Yaya Hamza can sokoto ya yi zamansa yana hidimar ƙasarsa. shi kuma Yaya Abubakar nan kano wani ƙaramin asibiti na dabbobi kuma ya gamawa suka riƙe shi duk da yana ta cewa zai ƙaro karatu shi kuma Yaya Hamza bai tsaya ba tuni ya nemi gurbin masters a University of Ibadan. Sai dai in ya zo gida hutu bai ma cika zuwa ba bai wuce a shekara sau uku haka ba.

Mun sake zana jarabawa a 2001 shima dai ba a dace ba. Ga shi su Baba Aminu sun fara mganar ya kamata Alhaji ya aurar damu. Tun da lokacin 15 16 ake aurarwa mu gamu sha tara muna shirin shi ga ta ashirin amman ba mgana ƙwaƙƙwara gwara ma Rahila mganarta da Ya Muntari ya kai gaban Alhajinmu kuma ya yi murna ƙwarai. Kowa kuma ya yaba da haɗin tunda su suka haɗa kansu. Ni ce dai haɗin ke ban dariya in ta yi ma Rahila dariya in na ga ta na rawan jiki akan Ya Muntari. To gwara shi ana son shi. Shi fa Yaya Abubakar yana yi ne amman kwata kwata kamar ba a son yana yi ba.
Chapter 44 · 0% Book details