← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 76

Sashe 35

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai na amsa masa shi kuma sai ya yi masa fatan samun sauƙi na amsa da Amin Amin nan falon na bar su na koma ciki Ina ce ma Jidda in sun gama karyawan ta gyara ɗakin su kafin ta yi ma Baby wanka.

   Da ya ke miyar ba ta da yawa sosai ba ta ɗau lokaci ba tunda agushin ma soya shi kawai na yi. Naman kuma na rago ne akwai ƙashi ƙashi a jiki sai da na tafasa sannan na yi amfani dashi kafin ka ce me gida ya ɗau kamshi miya. Na gama ɗiban ma Alhajinmu miya na saka a kula har na haɗa shi cikin kwandon da za mu tafi dashi sai ga Yallaɓai ya shigo kitchen ɗin.

"Ni fa an gama cika mini ciki da ƙamshi. Me muka samu ne?

Ya faɗa ya na tsaye a ƙofar kitchen ɗin. Kallonsa na yi kafin na juya ina goge jikin gas ɗin da miya ya ɗan ɓata.  Mirmishi na yi kafin na ce"Sai anjuma za ka ci na ka fa Yallaɓai."
Koƙarin shigowa ya ke yi na wurgar da abin hannuna na nufe shi ina turashi waje lokaci ɗaya ina faɗin" Mu je ka yi wanka lokaci na tafiya."
  Ba shi da mafita haka na riƙa tura shi har cikin bedroom ɗin mu. Takardun hannunsa na karɓe ina faɗin" Mai wankin bai zo ba?
Ya na saɓule dogon wandom jikinsa ya ce"Sakarai ne. Na fa kira shi ya riƙa ce mini yana hanya amman sama da awa ɗaya bai zo ba"

Ina dariya na ce"Kai da Sabitu ba" saboda suna shan dirama shi Sabitu karya da saɓa alƙwari shi kuma Yallaɓai ba ya son mutum mai ƙarya da saɓa alƙwari. Su yi ta samun matsala kuma ko ya ce ba zai ƙara bashi wanki ba sai Sabitu ya yi ta magiya domin ya na samun alheri a wajen Yallaɓai.

Cikin side drower na ijiye masa takardunsa ina juyowa muka ci karo da Yallaɓai fuska na kwabe kafin in yi mgana ya rumgumeni ni kuma ina ture sa na ce"Ban yi wanka ba Yallaɓai."
  "Nima ai ban yi ba. Kawai yau mu bar ta ranar tsami na duniya ne."

  Ina dariya na rumgume shi ta baya ina ɗan dukan bayan shi mun daɗe a haka kafin mu saki juna hammatar shi na ɗaga tunda bashi da riga ina rufe baki kafin na ce"Yallaɓai na na bukatar shaving gaskiya."

  Hannuwansa ya ijiye saman kafaɗata yana faɗin" Sadiya ta sangarta Yallaɓanta. Ki zo kawai ki yi aikin ki Madame.'"
Dafa kafaÉ—ansa na yi shima ya dafani muka fara tafiya ina faÉ—in" Muje Tiolet na gyara mijina."
Kallona ya yi ƙasa ƙasa kafin ya ce"To wai da na ce ko ni na fara gyara ki anan ne a ciki kuma ke sai ki gyara ni?
Ina jin haka na sake shi na yi gaba ina faÉ—in" bar shi kawai. Na gode Cafinter"

  Sai ya biyo ni yana dariya har ya na cewa" Wai kada mu yi ta asaran ruwa. Gwara mu haɗa aikin."
Ko juyawa ban yi ba na buɗe kofar tiolet na shiga bayan na yi addu'a shima sai ya biyo bayana zai shigo na ce" Yallaɓai addu'ar fa"
Sai ya koma da sauri ya yi sannan ya shigo ya maida ƙofa ya rufe zai yi mgana na masa alama da bakina na ja zif alamun ya yi shuru sai shima ya yi haka alamun ya kama bakin shi mirmishi na yi masa kawai Towel na zaro daga hanger dake sama na mika masa sai ya karɓa ya juya yazare gajeren wandon da ke jikinsa ya ɗaura towel ni kuma sai na ciro veet din a saman wajen ɗan dirowan ajiye su kayan wanka a cikin sink na ce ya shiga ya zauna kamar dai yadda muka saba.

  Ni na shafa masa a ƙasan sa da hammatarsa sannan bayan minti biyar ya yi na kwashe na goge wajen sannan na wanke masa. Tare muka yi wanka ranar bayan na chuɗasa nima sai ya chuɗani muna yi muna ɗan wasannin mu da muka saba cike da so da ƙauna muka fito dukkanmu ɗaure towel shi a kugunsa ni kuma asaman ƙirjina.

  Yallaɓai na fara tayawa ya shirya cikin shadda mai ruwan ƙasa domin ya ce min suna da ɗaure aure na wani abokinsu da suka yi secondary tare zai ƙara aure.
Ina saka masa link ina faÉ—in" Har da Uncle Abba zai zo daurin auran?
"E. Har da ma Tariq. Muhammad Bello ai ajin su É—aya ma da Tariq lokacin muna makaranta."

  Sai na jinjina kai kafin na ce"Abokan ku sun fara biyu kuma kuna hanya kenan"
Ya na yar dariya ya ce"Wasu ma ko É—ayan ba su ijiye ba. Irin su kawu ba. Da wani Salihu bala wallahi sun zame mana tazuran kawai. Yau ina ga yau sai sun sha caccaka tun da kaf mate É—in mu za su zo wajen É—aurin auran nan "
Ina dariya na ce"Kar a taɓa min kawunaa. Ina nan ina nema masa mata."
Yallaɓai na kallona ya ce"Allah ya sa kar kawun naki ya baki kunya. Tun da kika har Nene ta ƙyale Abba da mganar aure kin san lamarin ya fi karfin kowa"

"Bai fi ƙarfin Allah ba. Muna addu'a in sha Allahu in lokaci ya yi zai yi."

Sai ya amsa min da cewa" Allah ya sa muna da rabon gani." Agogo na ɗauko masa wani ɓaki na fatar damisa na saka masa.
Turare na fesa masa sannan ya ce na zaba masa takalmin da zai saka. Wani baƙin takalmi na zaɓar masa ni na siya masa kwanki lokacin ina da ɗan kuɗina na ga wata mate ɗina a BUK na tallarsu suka yi mini kyau na ce ina so 18k na siye shi Yallaɓai na son takalmin nan fiye da sauran takalmansa duk da ya na ma cikin masu saukin kuɗi amman saboda ni ce na yi masa kyautarsa ya sa ya ke ji da shi.

Sai da na gama shirya shi tsaɓ sannan nima na ce ya ta ya ni zaɓan kayan da zan saka. Mun daɗe gaban wardrop duk wanda na nuna sai ya ce a'a. Daga karshe dai ya tsaya kan wata super shi ya siya mini ita mai kalan green na ciro ta ina faɗin" Amman Yallaɓai mayafi zan saka ko?
Hararata ya yi kafin ya ce" Asibiti gidan biki ne?
Na marairaice ina faÉ—in" Don Allah fa. Atamfar nan ba ta kyau da Hijabi."

  Jan gefen hannun rigansa na ke yi sai ya kalleni sai na marairaice ina faɗin" Haba My Yallaɓai na. "
Wani kallo ya yi mini kafin ya duƙa ya na faɗin" In kin yarda mu sabunta wanka."
Da sauri na ce" Bar shi na saka Hijabin."
Na faÉ—a ina tura baki shi kuma yana mini dariya.
HaÉ—e rai na yi ina faÉ—in" Ni ko? Ni ko ai shike nan."

Sai ya ce to na saka mayafin amman sai na yi alƙwarin amjuna akwai ɓarnan ruwa ya na iya sai na ce na yarda sannan ya bari na ɗauko mayafin kayan takalmi ma shi ya zaɓa min wani flat mai ruwan ƙasa irin kayan shi ya na da jaka sai na ɗauki jakar ina jin Yallaɓai na faɗin" Wai ko dai ba Alhaji za ki je gaisarwa ba. Biki za ki je?

  Ina dariya na ce" Kai Yallaɓai na. Wani biki kuma! Jinya zan je."
"To ma su jinya."

Share shi kawai na yi domin na san yanzu in na yi magana sai ya iya ɓata mini shiri shi ya sa na yi shuru ina bin sa da mirmishi.
Muna nan sai ga Sabitu ya kira ya ce ya na waje sai ya ɗau kayan ya fita dashi ni kuma fita zuwa ɗakin su Jidda na ga sun shirya dogayen riguna suka saka na Abaya saboda halin Yallaɓai na ce su cire mayafan su saka Hijabi yanzu nan zai ce yara ma ƙanana ina koya musu saka mayafi. Yallaɓai ba wai yana da tsanani ba ne amman fa ya na da saka ido kan iyalansa. Wani lokaci zai yi mini tsanani wani lokacin kuma sauƙin kanshi har ya na yi mini yawa.

  Jidda na ce ta ɗau kwandon abinci zuwa mota ni kuma na koma ciki ina fesa turare. Har na ɗan fesa kaɗan sai na tuna da Yallaɓai yanzu raina zai ɓaci. Da sauri na ijiye na koma ina shinshina kaina in ƙamshin ya fito na shiga uku da faɗan Yallaɓai.
Hon kawai ya yi ta mini daga haraba ni kuma sai da na kashe duka wutar gidan sannan na fito na kulle ƙofar falo.
Su Jidda na gidan baya ya na hira da su ina buÉ—e gaban mota na shiga ya juya ya na kallona kafin ya ce" Alhaji ki ka fesa ma turare ko likitocin ?
Ya faÉ—a cikin haÉ—e rai. Da sauri na ce" A'a. Turaren kayan ne ina ga."
Ƙura mini ido ya yi da sauri na ce" Da gaske ban fesa turare ba."

Bai ce mini komai ba ya yi ma motar key sai na koma na jingina da kujeren mota ina maida numfashi. Mun É—au hanya na ji ya na faÉ—in" Mu fara zuwa asibiti in na duba Alhaji sai na kai su gwammaja É—in"
Ni dai na amsa masa domin na ga ya wani haÉ—e rai ne.

Mun isa asibitin wajen sha ɗaya saura ne. Amman na iske har Ma'u ta zo ni da Rahila ne kawai ba mu iso ba amman har su Yaya Auwal da matansu da Amina ma ta iso daga kaduna. Mun gaggaisa da su har da Yaya Murja Baaba ta na nan ita da Gwaggo suma na gaishe su Baaba a dakune ta amsa ban damu ba. Yallaɓai kuma ya fara musabaha da mazan matan ma suka gaisa ga duka har ƙasa ya gaida Gwaggo da Baaba.
Chapter 35 · 0% Book details