Sashe 48
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 A bangaren ɗakin Nene Zuwaira ce Babba sai Maimuna. Sannan ta yi Bahijja. Sai da ta yi mata uku sannan ta samu namiji sai Alhaji Inuwa ya cika burinsa ya sanya masa sunan Amininsa Yusuf suna kiran shi( Tafida) a kuma a tsukin Hajiyar tafida itama ta sauka an samu namiji itama sai kawai shima Alhaji Yusuf ya saka masa sunan Amininsa Inuwa suna kiran shi(,Tariq) a kuma lokacin a gidan su Nene mahaifinta matan shi biyu mahaifiyar su Nene Innayi ta daina haihuwa amman abokiyar zamanta Hannatu( Inna) ta haifi ɗan ta Namiji sai ya ci sunan mahaifinsu Abdulmu'iz sai suna kiran shi da Abba shi ne kuma auta a gidan su Nene sai ya kasance waɗanan mazan guda uku sun tashi tare sun girma tare sun kuma ba da misalin kyakyawan zumunci juna a tsakanin su.
Bayan Yusuf sai Muttaƙa sai auta Halimatu.
Sai Maman Farko(Hajiya Saliha) ita yar kano ce ita ta ɗan fi Nene yawan ƴa'ƴa domin ƴaƴanta bakwai ne.
Usman shine Babba wanda Zuwaira da Maimuna ne ke gaban shi a tsarin manyan gidan sai shi. Bayan shi sai Nasaratu ita sa'ar Tafida ne sai Nasir sai Jafar sai Suwaiba da Jamila autar ta mai suna Hindatu. Daga ita sai Hajiya Zaliha(Hajiya iya) ita Æ´aÆ´anta huÉ—u ne.
Hafsat ce babba sai Saffiya sai Muhammad kabir sai Musbahu.
Sai ta huɗun da ta rasu Hajiya karima ita ƴaƴanta uku ne. Ummu Salama sai Adnan Jawahir ce ƙaramar su. Kuma bayan rasuwarta riƙon su Jawahir ya koma ya koma ƙarkashin kulawar Nene.
Kaf ƴaƴan Marigayi Alhaji Inuwa kamar shi sun yi ilimi sun kuma tsaya da kafafun su. Ba matan ba sannan ba mazan ba wasu sai sun gama karatun suke auren wasu kuma suna cikin yi suke auren sai su ƙarisa a gidan mazajen su. Yusuf dai ya yi karatunsa na fimari kaf a garin Rano ne a gidan Alhaji Yusuf Tafida tare da Tariq da kuma Abba. Sannan bayan sun gama ya nema musu makarantar kwana a kaduna mai suna. Federal Sceince and tecnical collage (FSTC) Kafacan Kaduna. Su uku tare suka yi makaranta tun daga matakin fimari har matakin gama babban sakandiri daga nan sai Yusuf ya tafi Abu zaria. Tariq ya tafi jami'ar Ibadan shi kuma Abba ya tsaya anan BUK ya yi karatun shi.
 Sun gama degree farko kuma kowanne ya zaɓi in da ya ke so ya cigaba da karatunsa. Shi Tariq Jami'ar lagos ya koma ya yi masters ɗinsa shi kuma Yusuf ya dawo kano ya yin da Abba bai cigaba ba ya koma Rano ya fara kasuwanci da noma tunda abin da ya karanta kenan. Yawancin zaman Yusuf ba a kano ba ne ya fi zaman Rano shi ya sa akwai sabo na musamman tsakaninsa da yaran gidan Marigayi Tafida, kuma a gidan ba a kiran sunan shi sai dai Baaba. Ita kuma Hajiyar Tafida ta ce Tafida mutun ɗaya ce ke kiran shi da Daddy Saudatu(Gimbiya) ƙanwar Tariq ce. Kuma ta ci sunan gimbiya ce matar sarkin Rano a wancan lokacin.
Mganar aurena da Yusuf ta yi barazana domin yan'uwansa sun ce ba zai yi ba ya yi gaggawa sannan bai gama karatu ba kuma ba shi da sana'a mai ƙarfi sai buge buge. Kuma shi Yusuf Mutun ne da ba ya son zama a ƙarkashin wani ya fi son ya zauna in his on. Ban taɓa ganin mutun mai tsari irin Yusuf ba ya karanta abin da ya shafi zane zane amman kuma ya na da sani kan abin da ya shafi gini da sauran su. Tun kafin mu yi aure ya sha faɗa mini so ya ke yi ya buɗe kamfanin shi na kan shi ba ya ƙaunar aiki a ƙarkashin wani ya fi so ya cika burinsa na yadda zai gina kansa domin ƙara ma matasa karfin gwiwan kan dogaro da kansu. Bai taɓa faɗa mini yan'uwansa sun ƙi auran mu da farko ba sai daga baya saboda lokacin da suka ƙi sai ya kai su ƙara wajen kawun nan na su sna bangaren babansu da ke Rano su suka shige masa gaba akan mganar auran mu. Daga karshe da suka ga ya dage sai suka hakura suka bar shi ya yi. An saka rana ba lokaci mai tsawo ba sai aka sanya shi lokaci ɗaya da na su Rahila. Abu kamar wasa kamar mafarki sai ga shi abu ya tabbata kowa ya ji zan yi aure sai ya yi mamaki kamar irin su Ma'u da ba haka ta so ba sannan da ta ga Yusuf sai ta fahimci na tsere mata ko ba ta fada mini ba a fuskarta na ga hassada da kishina. Duk da rasuwar Mama ta saka an ƙara wata ɗaya kafin auran mu mutuwar da ta gigitamu har Alhajinmu da har gobe ya kasa manta rashin Mama. Da Gwaggo da ta daɗe cikin jimami shi ya sa a sha'anin bikin ba a yi wani taro sosai ba. Amma dai kayan ɗaki komai iri ɗaya ni da Rahila babu in da aka bambamta mu ni a anguwar Dakata muka fara zama ita kuma Rahila nan cikin anguwan Ɗorayi ne tana kusa da gida.
A tsarina ban taɓa tsara ma kaina fara rayuwa a gidan Haya ba. Amman sai gashi nan ne muka fara shimfiɗa rayuwarmu ni da Yusuf. Ya san ina karatu kuma ya yi alƙwarin barina har na gama karatuna. Mun sha amarcin mu sosai na ke jin daɗin zama da Yusuf in zan je makaranta wani lokacin har rakani yake yi in bai da wajen zuwa in shima yana da shiga makaranta sai mu jira juna mu koma tare. Yana samun kira haka in ana son zane sannan tun lokacin yana karambanin karɓan kwangila gini sai ya nemo ma'ikata da injiniya.
In na ce a zamana da Yusuf bai gatanta ni ba na yi ƙarya. Ya yi mini hidima da jikinsa da Aljuhunsa. Nene ta karɓe ni a matsayin surukarta. Amman ban da yayyen Yusuf da suke uwa ɗaya barin ma Anty Bahijjan sai bayan auran na ke sanin sun so hana auran mu a cewar su ya bari zuwa gaba sai ya auri Gimbiya. Sai daga baya na fahimci Gimbiya na son Yusuf soyayyar da ba ta iya ɓoye shi. Shi kuma ba ta gan shi a ƙanwa ma ya ɗauke ta. Suna son haɗa auren ne saboda amincin iyayensu amman kuma hakan bai yuyu ba. Farkon auran na yi musu biyayya kamar zan bauta musu saboda dai ina auran ɗan'uwansu. Kuskurena na farko shi ne na yi tunanin yin tsarin iyali saboda karatuna sai dai cikin Jidda shi ya zo ya shammace ni. Watanni tara da kwana huɗu da aurenmu na haifi Jidda da ta ci sunan Nene Hauwa'u.
lokacin ina aji biyu ne zan shiga uku na sha matukar wahala ga ciki ga karatu ga aure shi ya sa ina yaye ta na nemi shawaran Yusuf akan ina son in yi tsarin iyali shi kuma sai ya ba ni goyon baya muka je wani asibitin kuɗi na fara karɓan allura duk bayan 6 months har na shekara biyar. Daga wannan alluran sai ta zame mini matsala. Na gama karatun kuma ina son na ƙara haihuwa amman shuru ko domin goron su Anty Bahijja tunda suna ganin na daɗe ban ƙara haihuwa ba bayan Jidda sun ta zargin ko planning na ke yi amman ban faɗa musu ba tunda kamar na tona asirin kaina ne.
 A kuma lokacin muka shiga rayuwa na halin babu. Yusuf ba aiki yake yi ba. Sannan aikin da ya kan samu ya ragu sai jifa jifa. Duk wani abin da na ke dashi sai da ya kare na zo da ɗan kunnen gold wanda na siya da sadakina amman sai dai na siyar da shi. Da cewar Yusuf in ya samu anam gaba zai siya mini. Saboda haka ya sa na nemi aiki a makaranta kuɗi anan kusa damu na fara koyarwa saboda mu rufa kan mu asiri. Ba zan raina ba in Yusuf ya samu na samu to amman yanayin aikinsa kafin ya samu fa? Kuma na yi na yi ya nemi aiki shi yaƙi a dole sai ya tsaya da kafafunsa. Ta ina za ka iya samar da kamfani baka da kuɗi?
Zan iya cewa renon jidda ma tare muka yi tun lokacin ina makaranta tare muke zuwa ya rike mini Jidda har mu fito daga karatu ko ya kai ta gida wajen Nene. Da na fara Koyarwa shi na ke barin ma a gida kafin na dawo ya gama duka aikin gida har girki ma ya yi. Kuma albashina ba na iya cin komai dashi ɓukatunmu na ke yi mana dashi. Sai dai yan'uwan shi duk ba su ga haka ba a tunaninsu na tsaida haihuwa ne saboda Yusuf bai dashi ni ma na fara damuwa sai na fara yawon private hospital ana ce mini ba matsala zan ƙara haihuwa sai da Jidda ta kai shekara Takwas da wattani na ƙara haihuwan y'a mace sai ta ci sunan Anty Maimuna muna kiran ta Baby zuwa lokacin kuma Yusuf ya samu buɗi tunda har ya siya fili ya fara gini muma kuma Alhamdulillah muna cikin ni'imarsa.
Na sha wahala a haihuwan Baby C.S ma aka yi mini daga nan kuma sai na yi ta samu matsaloli na zubar jini da kasala sai juwwa. Daga baya sai na fara ramewa sannan haihuwa ta zo ta tsaya mini cak sai na fara jelen gen zuwa ganin likitoci a asibitocin kuɗi suna cin kuɗina suna gaya mini ba matsala in sha Allahu zan ƙara haihuwa. Tun ina ɓoye lamarin har ya fallasa ga dangin Yusuf tsarin iyali na yi ya ba ni matsala shi dai ya ce bashi ba ne ya faɗa sai na yi tunanin Ma'u tunda itama bayan ta gama karatu ta dawo gida ba daɗewa ta haɗu da Alhaji Mustapha cikin wattani kaɗan suka yi aure sai wayan gari na yi na ga Ma'u tsudum a cikin dangin mijina.