Sashe 10
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ƙarishe faɗa tana shesshekan kuka sai kuma ta kalli Alhaji tana cigaba da faɗin"Alhaji wallahi Allah ɗaya kenan ba ni da wani mugun nufi kan Sadiya. Ina son ta kamar yadda na ke kaunar yar uwata Zainab, ina son ta ƙwatankwacin yadda nake son su Rahila. Amman ban san me ya sa Sadiya ta kasa fahimtata ba, Alhajinmu ko rashin fahimtar da ta faru a baya ta maganar aurena da Yaya Hamza tabbas raina ya ɓaci kuma na ji haushin Sadiya amman har ga Allah daga baya na cire abin a raina ban taɓa kallon Sadiya dashi ba. Ni ko me ya sa zan yi haka? Alhaji Sadiya ce ba ta sona ban kuma san me na yi mata ta tsane ni ba tana hulɗa da kowa Alhaji ban da ni in dai abu ya shafe ni Sadiya tsame hannunta ta ke yi a ciki ba ta zuwa gidana ni in na je wallahi ko bare Sadiya ba ta yi masu abin da ta ke yi mini, in muka haɗu a gida ko gidajen ƴan'uwa Alhaji ko na yi ma Sadiya magana ba ta yi mini ta yi ta gaba da ni. Na zauna ta yi ta tunanin abin da na yi ma Sadiya ta tsane ni amman na kasa ganewa, daga baya sai na fara tunanin ƙila saboda Alhaji ka ɗauke ni ka sanyani cikin Iyalanka ne, ita kuma Sadiya ba ta so wani daga waje ya raɓe ta, sai kuma daga baya na kwaɓi kaina da cewa ai ni ba bare ba ce Alhajinmu ni ma ƴarka ce kamar Sadiya"
 Ta faɗa har ta na riƙe kafar Alhaji, tana kuka, gabaɗaya na san ta gama cika zuciyar Alhaji da tausasa kalamanta.
Ni ko a raina ban ji na yi nadama ba, kallonta na ke yi ina mamakinta har ta manta mganganun da ta gaya mini a lokacin da aka fasa auranta da Yaya Hamza? Har ta manta?
 "Tashi. Tashi Asma'u. Ke kam ba bare ba ce ke ƴa ce kamar Sadiya. Ta shi daina kuka kin ji bari kuka nan"
 Ya faɗa cikin sigan lallashi, Alhaji Mustapha har da mika mata wani farin hanky, ya na faɗin"Ki share hawayen ki Ma'u"
Ba wanda ya fi baƙanta min rai irin Yusuf har da shi a masu ba ma Ma'u hakuri daman halinta ne ta shirya makirci a raja'a a kanta.
 Tsaki na ja mai ƙara kafin na ce" Ke dai Ma'u wallahi an yi baƙar munafuka kuma makira, ke wai kina kuka saboda ki zama abin yarda ni kuma na zama victim kamar ko yaushe ko? Har kin manta? Har kin manta maganar da kika faɗa mini lokacin da aka rushe maganar auran ki da Yaya Hamza? Na ce kin manta? To wallahi kamar yadda baki ƙaunata nima abada ba..'
 "HALIMA..."
Alhajinmu ya katseni tare da kiran sunana a tsawa ce, ban kalle shi ba na cigaba da faɗin"Alhajinmu cewa ta yi fa sai ta rama abin na yi mata sai ta kun samini kwatankwacin baƙin cikin da na kunsa mata kuma.."
 "Na ce ya isa ko Halima? Ko so kike yi na saɓa miki?
 Alhaji ya faɗa ransa ɓace, sai na yi sansarai rai, ganin ya koma ya ba ma Ma'u haƙuri tana shessheƙan kuka.
Baƙin ciki da ya tokare mini zuciya ya ta so mini ba kasafai na ke kuka kan abu ba amman daman Ma'u ta saba cin nasara a kaina akan kowa ko da yaushe ni ce victim ita kuma mai gaskiya.
 Ban san nima na fashe da kuka ba, sai kawai na miƙe zan fita daga falon ina faɗin" Shike nan ai daman ita mai gaskiya ce ita ce ba ta laifi ni ce fitananniya. Alhajinmu ni fa ƴar ka ce Ma'u fa? Bai kai kamar ni da ka haifa da gudan jinin ka ba."
"Ke ke Sadiya ina za ki je?
Alhajinmu ya fada saboda na juya ina kuka zan fita ne.
 "Wallahi zan saɓa miki in kika fita Halima."
 Shi ya sa na fasa fita amman sai na coge a tsaye ina sharan kwalla. Ran Alhaji ya ɓaci ya ɗaga murya ya na kiran sunan Gwaggo.
Sai gata ta shigo da sauri ta na sanye da Hijabi a jikinta. Gani na tsaye ina goge idanuwana sannan ga Ma'u na ta shesshekan kuka Alhajinmu na faman ba ta haƙuri.
Cikin mamaki da damuwa a saman fuskarta har kuma ya bayanna a muryanta ta ce"Subhanallah. Alhaji lafiya? Me ya faru ne?
Duk da ta san dalilin zaman amman shi dailin koken koken namu ne ba ta sani ba.
 Yusuf ne ya tashi daga in da ya ke zai iso in da na ke tsaye amman Alhajinmu sai ya dakatar dashi.
"Dawo ka yi zaman ka Yusufa ƙyaleni da ita."
 Sai ya koma ya zauna a inda ya tashi amman gabaɗaya hankalinsa na kaina kamar yadda hankalin Alhaji Mustapha ke kan matarsa.
 "Taho min da Halima nan gaba na Maimuna."
 Umarnin da Alhajinmu ya ba ma Gwaggo kenan sai ta riƙo ni lokaci ɗaya ta na faɗin" Mu je Sadiya. Mu je Alhaji na kiran ki."
 Ban isa na yi musu ba sai na bita har gaban Alhaji ta kuma zaunar da ni a gabansa a kuma in da na tashi, jan majina na ke yi ina ƙokarin shanye takaicina.
Gwaggo ta kalli Alhajinmu kafin ta ce"Daga sulhun ne suka fara koke koke kuma Alhaji?
 Â
 Bai amsa mata tambayarta ba, sai ma kallonta da ya yi kafin ya ce" Samu waje ki zama, saboda abin da zan faɗa ina so kema ki zama shaida."
 Sai Gwaggo ta koma ta zauna a kujeran mai zaman mutum biyu dai dai lokacin da ta ke kallon Ma'u wacce ke ta faman tsane hawayenta da hanky ɗin da ke hannunta. Sannan lokaci ɗaya ta na cigaba da shessheƙan kukanta.
"Ke ma Ma'u ki bar kukan ya isa haka nan."
Ta fada cikin wani yanayi, a cikin ranta tana tunanin komai Alhaji zai yi ba za a taɓa samun daidaito ta bangaran Ma'u da Sadiya ba.
"Halima.."
 Kamar daga sama na ji Alhajinmu ya kira sunana a kausashe kuma da karfi jikina da zuciyata suna rawa na ɗaga kai ina kallonsa cikin ɓacin ran da ya bayyana har a saman fuskarsa na ga ya nuna ni da yatsar sa manuniya da ya hana ni ma iya amsa masa kiran sunana da ya yi.
 "Yau ce rana ta farko kuma ta karshe da zan ji ƙin ƙara kiran Ma'u da bare, yau ce rana ta ƙarshe da za ki ƙara yi mata kallon wata ba ƴar uwanki ba. Na san halin ki saboda ni na haifeki da gaske ki na da fitina da rashin haƙuri sannan ba ki da yafiya da barin abu ya wuce, sannan kina da nacin faɗa, kowa sai ya manta amman ke zuciyarki ba ta iya mantuwa. "
 Ya ƙarishe faɗa da karfi, kamar zai kai mini duka daman Alhajinmu akwai faɗa in ran shi ya ɓaci. Kuma ka da ka ba ri faɗan shi ya faɗo ta kanka domin ba za ka taba jin daɗi ba.
 Shi ya sa na ji zuciyata ta karye na fara kuka, kenan har a yau ma Ma'u ce za ta sake yin nasara a kaina?
 "Kar na kuskura na kara jin kin danganta Ma'u da bare, ita ba bare ba ce. Jinin ki ce domin in aka tsaga jininta za a ga na ki jinin haka itama in aka tsaka na ta jinin za a ga naki, bari na tunasar da ke abin da nasan ba ki manta ba, ni na saki nono mahaifiyar Asma'u ta kama Asiya ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya. Me ya sa kike da tunanin banza ne? Me ta yi miki? Tana bin ki amman kina ƙara nuna mata tsana? Ina ce har hakuri Murja ta ce ta yi ta ba ki kika tafi kina ta cin mutumci? Ke sheɗan ce da ba ki jin bari Halima ko so kike ki zama sheɗaniya a cikin mutane?
 Kuka kawai na ke yi, wannan karon kukan da na ke yi ya fi na wanda Ma'u ta yi fidda amon sauti, falon ya yi tsit sai tashin faɗan Alhaji kawai ake ji har Gwaggo tana zaune ne amman ba ta iya dakatar da Alhaji ba.
 Ma'u ce ta ɗago kanta tana kallon Alhaji kafin ta ce" Alhajinmu har a waya na kira ta bata ɗauka ba sai na yi mata saƙon murya ta WhatApps bari ma ka ji."
Nan da nan ta É—auko wayarta ta shiga ta duba sai ga shi ta kunna muryanta tarwai ta na fadin"Ki yi hakuri Sadiya da abin da Shema'u ta yi miki. Har ga Allah ban san a ina ji maganar ba. Na nuna mata ban ji daÉ—i ba na kuma ce sai ta ba ki hakuri saboda haka zan tura mata lambarki sai ta kira ki ta baki hakuri."
 Alhajinmu ya girgiza kai kafin ya kalleni ya na faɗin"Ta yi ta ba ki hakuri akan laifin da ba ita ta yi miki ba amman kin kasa hakura. Tabbas na fahimce ke ce sheɗaniya sannan ke ce ke hassada duk abun da ke faruwa."
 Ina rawan muryan kuka na kwashi rantsuwa ina faɗin"Wallahi Alhajinmu..."