Sashe 36
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ma'u har da cewa" Yallaɓai barka da safiya.'
Ya juya suna gaisawa su Jidda ma suka bi kowa ɗaya ɗaya suka gaishe su. Suna waje Alhaji na ciki ya na barci Yallaɓai ne ya shiga tare da su Jidda. Ba daɗewa ya fito ya ce za su tafi ni na raka shi har bakin mota muka rabu akan cewa sai anjuma za su zo tare da su kawu ina ɗaga musu hannu suka bar haraban asibitin Baby sarkin rigima jin wajen Nene za a kaita sai ta fara murna.
Abincin da na zo da shi Gwaggo na ba ta karɓa ta na ta saka albarka.
"Ba wacce ta zo hannu rabbana. Yadda kuke jin ƙan mu kuma Allah ya jiƙan ku wata rana."
Aka amsa da Amin Amin Baaba ta na ta wani taɓe ba ki ni ko ba ta isheni kallo ba
Mun gaisa da Ma'u da tambaya ya jiki daga nan na karisa saman darduman da Amina ke zaune ita da Laila da Khaleesat suna hira. Sai bayan na natsa ne na tambayi Baba Aminu aka ce ya koma tun safe Baba Sani kuma ya koma gida ya huta sai anjuma zai dawo.
Na kira wayar Rahila ta ce min ga su nan a kan hanya ba daÉ—ewa ta iso itama da kwandon abincin ta.
Kowa da wanda ya saba dashi ya zauna su Yaya Murja yan wajen Ma'u suna zaune waje ɗaya har da Zaitunan Yaya Abubakar. Yaya Aina ce ma ta ɗan zauna a wajen Rahila kuma daman kowa ya san kaf gidanmu na fi shaƙuwa da ita shi ya sa ko an gamu tare muna hira ba wanda zai bi ta kai.
Â
 Muna nan har bayan azahar Laila Yaya Auwal ya ɗauke ta zuwa gidan su. Alhaji ya farka wajajen biyu duk mun shiga mun gaishe shi da jiki ya ce ya ji sauƙi yau ma ya ce likita ya sallame shi.
 Yaya Hamza ya ce ya bari ko zuwa gobe in ya ƙara jin sauƙi.
Baaba na gefe ta ce"Gaskiyar Hamza ka ƙara kwana ka samu hutu sosai Yaya Sule."
Shi dai Alhaji an fi ƙarfinsa kawai ne kawai shi ya sa ya yi shuru. Sai ya koma ya kishigiɗa bayan Gwaggo ta kara mai filo
"Yara nan fa duk sun taho maka da abinci me za ka ci?
Gwaggo ta faÉ—a ta na kallon shi.
"Allah ya saka muku da alheri. Allah ya yi musu albarka na gode."
Dukkanmu muka amsa da Amin Amin
Abincin ya ce sai anjuma amma ya sha ruwa. Ni ya kallah kafin ya ce"Dubu yau ke kaÉ—ai kika zo? Ina kika baro min uwargidana Hauwa'u?
Ina dariya na ce"Ta zo ka na barci Alhajinmu. Yallaɓai ma ya zo amma anjuma zai dawo in sha Allahu."
Sai ya jinjina kai kafin ya kalli Ma'u ya na faɗin" Asma'u ki yi ma megidanki godiya maimuna ta faɗa mini bai bar yaran nan sun kashe komai ba. Allah ya ƙara ma arziƙin sa albarka Amin."
Ma'u ta amsa da Amin Baaba har ta amsawa da Amin Amin da karfi na kalle ta lokaci ɗaya ina taɓe baki. Ba mu daɗe a dakin ba muka fita waje saboda dokar likita. Muna asibitin nan har la'asar sai ga kiran Hauwa ta na ce min ga su a asibitin ita da Mutaƙƙa ina ne barayin ɗakin da aka kwantar da Alhajin? Ina jin haka ni na fita haraban asibitin na taho da su.
  Shi ya sa na ke son Hauwa in dai abu ya same ni ita ke fara zuwa ta yi mini jaje ko murna ita da mijinta. Mutaƙƙa ya shiga ya gaida Alhaji duk da ba lokacin dubiya ba ne na faɗa ma Alhaji ƙanin mijina ne ya na ta saka albarka. Mutaƙƙa ya zo da kayan marmari Hauwa kuma har abinci ta zo dashi kuma nan ya bar min ita karfe shidda ya ce ta koma gida. Na ji daɗi matuka ko da ganin sauran yan'uwana dangin mazajensu na ta zuwa gaida Alhaji. Ma'u har uwargidanta Hajiya Zainab ta zo da sauran ƙanensa.
 Hauwa ta zo ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ni na yi mamakin ganinta har a cikin zuciyata na san ba domin ni ta zo ba illai Ma'u ce ta je ta taro ta. Hauwa ta saki baki ta na kallon su har da rumgume juna muna ji ta na faɗa ma Baaba matar Yayan mahaifiyar Alhaji Mustspha ne. Sai ta ɗago ta ga ina kallonta sannan ta ce"Kuma Yayar mijin Sadiya ne.".
 Gwaggo na ta saka albarka da godiya ina ji Ma'u ta nuna Baaba ta na faɗin ga mahaifiyarta. Anty Bahijja har ƙasa ta duka suna gaisawa Rahila na in da muke Khaleesat ta shiga cikin gari gidan ƙanwarta Anty Aina ma ta koma gida Amina ma ta je gida ta huta. Yaya Murja ma dazu ta koma mu da Yaya Balki ne kawai mu ke asibitin.
Daga zaunen da na ke na gaisar da Anty Bahijja sai lokacin ta kallemu ni da Hauwa.
"To su Hauwa ashe a nan nan?
Cikin rawan jiki ta ce" E. Ban daÉ—e da zuwa ba. Tare da Baban Sahla mu ke ya kawo ni sai ya wuce."
Sai kawai ta wuce tana faÉ—in" Hakan na da kyau."
Shiga ciki ta yi Ma'u na gefenta domin ta duba Alhaji.
Sai da ta shige ne sannan Hauwa ta kalleni nima sai na kalleta amman ba mu yi mgana ba muna nan zaune ta fito har ta na ba ma Gwaggo 10k. Wai sai ga Ma'u ta juyo ta na ce min" Sadiya kalli Anty Bahijja da ɗawaniya."
 Mirmishi na yi kafin na ce" Allah ya ba da lada."
Ma'u ce za ta rakata ni dai ko kafata ban É—aga daga daga na ke zaune ba.
Sai ta juya ta na kallon Hauwa kafin ta ce" Yanzu za ki tafi gida na yi miki lift?
Da sauri na ce"Mutaƙƙa karfe shidda ya ce ta koma gidan"
Sai ta wani kalleni kafin ta ce" Ya yi. Allah ya ƙara lafiya."
Na amsa mata da Amin Amin har da Baaba a masu rako. Sai da suka bar wajen Rahila ta kalleni kafin ta ce" Ku ba ku yi rakon ba Sadiya"
Kai tsaye na ce" Saboda mene! Ai ni ba na neman suna. Wacce ta zo domin ta ba ki ga har da uwarta arakon ba?
Sai Rahila ta kasa mgana. Saboda ta san halina ta na ƙara mgana zan saki wata mgana kuma ga Hauwa a wajen sai ta tashi tsam da goyon yarta ta wuce wajen Gwaggo itama na rakata da harara.
 Hauwa ce ta kalleni cikin mamaki kafin ta ce" Wai ya kuke da Ma'un nan ne Anty Sadiya?.
Kai tsaye na ce" Ina wanan tsohuwar da kika ga sun fita tare? Sai ta ɗaga mini kai. Kau tsaye na ce" Ita ce mamanta. Ita ɗin Baabar mu ce ƙanwar Alhajinmu ce da suka haɗa uwa ɗaya uba ɗaya."
 Sai ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara mata da cewa" Baban Ma'u ya rasu tun tana ƙarama sai da Baaba ta yi wani auran Alhajinmu ya ɗauketa shi ya sa ta tashi a gidanmu."
Hauwa ta yi sakate kafin ta ce" Ikon Allah."
Sai na kalli Hauwa domin na san akwai mgana a bakinta.
Cikin sauri na ce"Me kika gani hala! Ko na ce kin ji wani abu ne a kaina daga bakin ta?
Shuru ta yi ni kuma da sauri na ce" Don Allah ki faÉ—a mini Hauwa. Ba lalle kin san ba shiri tsakanina da Ma'u ba kina gani da idon ki yadda take shigema Anty Bahijja kuma dalilina ne tunda ai ba Musbahu ta ke aure ba. Balle kusan ta yi musu yawa haka."
 Ƙasa ƙasa Hauwa ta ce" Ranar sunan Halima na ji suna mganarki."
Sai na yi kwafa kafin na ce" Ai ba za ta sauya ba. Munafuka ce makira."
Sai Hauwa ta riƙe min hannu tana faɗin" Ta so mu je ki ji wata mgana"
Barayin muka bari gabaÉ—aya mun haÉ—u da su Ma'u a hanya za su dawo. Har ta na ce mini Hauwa za ta tafi ne na ce mata a'a da gayya na ce mata za mu yi mgana ne ina gani ta yi tsam daga ita har uwarta ni ko na ja Hauwa muka wuce abin mu.
 Can haraba muka fita a babban falo muka samu kujeru muka zauna ina mai kallon Hauwa na ce"Me kika ji munafukar ta ce akaina?
Hauwa ta ce" Ni fa ina ta mamaki na san Æ´ar uwanki ce amman me ya sa za ta biye ma su Anty Bahijja suna kushe ki?
 Raina har ya fara ɓaci da sauri na ce"Me ta ce wai?
Hauwa tasauke numfashi kafin ta ce" ita da Anty Bahijja da wata ban san ta ba tare da Ma'un suka zo."
Kai tsaye na ce" Shema' u ce ƙawarta ce."
Hauwa ta cigaba da faɗin" da Anty Maimuna ma awajen ana mganar haihuwa Anty Bahijja na ta faɗan wai kamar Tafida zai ƙare rayuwa da ƴaƴa biyu. "Buɗe bakinta sai cewa ta yi" wai daman tun farko ke ba ki da burin tara ƴa'ƴa da yawa. "
 Ido na har wani ƙyalli bala'i ya haska a fusace na ce" Ita Ma'un ta ce haka don ubanta?
Da sauri Hauwa ta ce" Ni fa ba na faÉ—a miki saboda na haÉ—a faÉ—a ba ne. Na gaya miki ne saboda ki sani ne"