← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 76

Sashe 7

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ina nan zaune ina ɗan duba wayata amman ban shiga group ɗin gidanmu ba sannan ban shiga na ɗaiɗaikun su da suka yi min magana ta private ba saboda nasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Fita na yi zuwa Instergram ina kallon kwalliya domin  ni Allah ya yi da son abu fashion. Domin har certificate gare ni akam koyon kwalliya ba ma ɗaya ba sannan ina da na koyon saloon da gyaran jiki, shi ya sa wayata cike suke da ire iren su.  Ban san na ɗau lokaci haka ba sai da Saude ta zo ta ce mini ta gama da ciki za ta gyara falo sannan na ba ta waje, bayan na ce in ta gama ta ɗora min ruwa a gas ta dafa taliya fara tunda ina da miya a firiza.

  Bedroom na koma na yi zama ma ina ta kallon Videos ɗin yadda ake kwalliya da na ɗaurin ɗan kwalli a istergram daman ni can na fi auki, kiran sallar azahar ya tada ni na ijiye wayar na je na yi sallah lokacin har Saude ta tsane taliyan da na ce ta dafa guda biyu, ni na karɓe ta na ce ta shiga ɗakin su Jidda ta yi sallah ni kuma sai na fito da miyar na ɗumama.
Na saka ma kaina sauran kuma na bar shi a cooler.  Ƙaramin falo na koma na kunna kallo sai na sauya tasha zuwa Mb2 na iske a wani film mai kyau sai na barshi, filet ɗin abincin na kan jikina ni kuma na miƙe kafata saman cafet ina cin abinci ina kallo har Saude ta fito sai na ce ta ɗauko kofin ta tsiyayo mini ruwa a Dispenser.

  Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta."
Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi.

"Babanku ya dawo?

Sai ta ce min a'a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala.
Ni na riga ta tashi, na tafi da filet É—in hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink É—in wanke wanke.
Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa.

    Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo.
Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faÉ—in" Ga ni Anty"
Ledan na tura mata gabanta lokaci É—aya ina mika mata kuÉ—in hannuna ina faÉ—in"Ki kaima mamanku kin ji ko?
Ta karɓa tana faɗin"An gode Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin ina faɗin"Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa."
Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film É—in horror ne ya É—auki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 É—in shi.
Uku na rana na koma É—aki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huÉ—u da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huÉ—u ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar É—ina.

  Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba.
Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform É—in Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe

  Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha'i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai.

  A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick .  Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba.
Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne.
Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa.

  Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin"Barka da dawowa Yallaɓai na."
Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce" Uhm. I like it."
  Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce'Me? Yana mini wani kallo ya ce"ƙamshin ki mana."
Far na yi masa da ido kafin na ce"All is yours"
Kumatuna ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin.
Ruwan wanka na ce zan haÉ—a masa ya yi wanka sai ya ci abinci.
Shi kuma sai ya ce"E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba"

  Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo
Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana.

  Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya.
Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get É—in
Sannan ya dawo muka kama hanya mun É—auki hanya kenan na kalle shi kafin na ce" Na gwada kiran ka yau ban same ka ba."

Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Nima na kira ki ban same ki ba."
Sai ya kalleni kafin ya ce"Me ya faru?
Kai tsaye na ce"Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba?
Sai a lokacin ya tuna ya ce"Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi."

  Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

"Kawu barka da dare."

Shuru bai yi mgana ba.

"Uncle Abba barka da dare"

Wata murya a dakushe ya ce"Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina."

  Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya.
Ni ce na ce"Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC?
Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce" Sadiya?  daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi.
Shi kuma sai ya bige da faɗin"Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi."

Yusuf na dariya ya ce" Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba." Kai tsye ya ce"Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuÉ—ina sai ta biyani ballatana kai."

Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin"Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin?
Kawu Abba dagacan bangaren ya ce"Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka."
 
  Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin" Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa?
Sai na gyaɗa mai kai ina fadin"E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin."
Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faÉ—in"In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo."
Chapter 7 · 0% Book details