Sashe 15
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta ce mini "A'a su kaÉ—ai baban ya kawo ya ce Haliman ba ta jin daÉ—i"
Sai na ce Allah ya sauwake, sai da na ji Hauwa na faɗin ƙila ma Haihuwa ce.
Baki na saki domin ni har ga Allah ban san tana da ciki ba, har sai da na furta ma Hauwa. Ta na dariya ta ce" Kin daÉ—e baki ganta ba ne? Ni mun haÉ—u a walimar sabon gidan Anty Suwaiba, a can ne na ganta da cikin".
Kai na jinjina kafin na ce" Ni kin san ban samu zuwa ba."
Sai ta gyaÉ—a min kai, hira muka cigaba yi, amman hankalin Hauwa na ga yara, ita yayanta huÉ—u, sauran ta ce suna gida tare da babansu da Sahla kawai ta zo amman sai wahala take yi da yayan Halima da ba sa jin mgana.
Muna zaune muna hira Walid da wayonsa ya fi shekara biyar ya yi fitsari a cafet, mamaki ya isheni ganin Hauwa ta miƙe jikinta na rawa ta na masa faɗan me ya sa ya yi fitsari a zaune bai zai yi magana ba?
 Sai kawai yaron nan ya fasa kuka ya nufi bedroom ɗin Nene, na saki baki galala ina kallon abin mamaki.
Ina kallo Hauwa ta je ta diɓo ruwa ta zo da towel tana tsane fitsarin ina zaune ko motsi ban yi ba, na yi wannan wahalar a baya amman ban yi wahalan ƴaƴan ƙannen miji da yayyensa ba, na yi dai na uwar mijina a baya amman a yanzu wallahi na daina, in ba a gode na baya ba a barshi.
 Falon duk sun yi kaca kaca dashi sai da ta share, sannan ta dawo ta zauna Walid dai tun da ya shiga bai fito ba, Salha da Afra kuma Hauwa ta ce su sauka kasa su je wajen Anty Jawahir.
 Sai da suka bar falon sannan na kalleta kafin na ce"Wai sannu da aiki."
Mirmishi ta yi mini ba ta yi magana ba..ni kuma da ban iya shuru na ce"Ke wai har yanzu ba ki daina wannan wahalan ba? Uwarsu na can gida tana hutawa, ke kin baro na ki yayan wajen ubansu, kuma kin zo nan kina hidiman na wasu."
 Dariya ta yi kafin ta ce"Kai Anty Sadiya ba ki da dama."
Daman haka ta kan kirani, kai na girgiza kafin na ce"Tab. Wallahi Hauwa ba ƙanwar miji ko y'ar mijin da zan yi ma bauta, na yi ma mahaifiyarsa ita ce dole na, ko ita na yi a baya yanzun ma sai abin da ba a rasa ba."
 Cewa ta yi" Allah ko? Na ɗaga mata gira sai muka yi dariya har da tafawa ƙasa ƙasa ta ce"Nene ce kafin ta shiga ta kwanta tace mini na kula da su, gwara ke Sadiya haɗuwan juction kuka yi da Yaya Tafida, ni fa yar uwa ce abu kaɗan zan yi a taso min shi ya sa."
 Taɓe baki na yi kafin na ce"Kina da aiki. Ni fa sanin da na yi ko na yi ko ban yi ba sai an yi sururtu shi ya sa da gangan na ke ƙin yin abin,tun da ko ka yi ba godewa suke yi ba su yi ta bin ka da ƙananun maganganu. Ballatana ni da na yi ƙaurin suna."
 Dariya muka saka har muna ƙara tafawa, bajewa muka yi a falon Nene muna ta hira kiran sallar la'asar ne ya tashe mu, ni ce na leka ɗakin Nene ta na barci ga Walid a gefenta sai na bubbuga gefen gado ba ta da nauyin barci ta buɗe ido, sai ta ganni.
"Lokacin sallah ya yi Nene."
Kafafunta ta sauko ƙasa ta na faɗin"Sadiya? Yaushe kika zo?
Rankwafa na yi cikin ladabi kafin na ce"Tun dazu, Hauwa ta ce kin kwanta."
Sai ta mike, É—ankwalinta ya zame kanta cike da furfura, ni na É—auko mata É—ankwalin na bata ta É—aura lokaci daya tana fadin"Ina su Hauwa'un na ki? Ko sun je gidan Maimunan ne yau?
Da e, na amsa mata sai ta jinjina kai kafin ta ce"Tafida ya je Rano ko? Ko ya dawo ne?
 "A'a Nene, sai ya dawo zai biyo ta nan mu koma gida."
A sanyaye ta ce Allah ya maido su lafiya.
Nene dattijuwa ce ce za ta haura 60 da huÉ—u haka, jikinta ya yi tubus saboda hutu da jin daÉ—i amman tana da hawan jini ga sugar, amman da ka ganta ka ga Æ´a'Æ´anta saboda da ita suke kama barin ma Mazan, matan ne su ka É—an É—auko kamanin mutanen Rano.
 Ni na riƙeta har Tiolet sai da ta shiga sannan na fito, a ɗakin da muke sauka na falon Nene muka shiga muka yi alwala ni da Hauwa, muka yi salla, muna zaune muna ɗan taba hira haka sama sama ni da Hauwa.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿ï¸05*
Ni da Hauwa muna Gwammaja gidansu Nene har bayan sallar isha'i. Maman Farko ba ta dawo ba, Nene ta ce daman ta ce sai an yi uku za ta dawo wani kawunta ne ya rasu, sauran Æ´a'Æ´an nata ma da surukanta suna can gidan gaisuwan tare da ita. Hajiya Iya kuma na shiga mun gaisa bayan ta tashi.
Akwai wata Æ´ar dattijuwa Dije mai yi musu aikace aikace da girki amman ba kwana take yi ba zuwa take yi ta tafi, ranar ma ko da na zo ba ta nan an kira ta a waya jikanta ba lafiya.
 Ni da Hauwa muka gyara shashen Nene muka yi girki, saboda yara ne sannan ga Nene ga su Jawahir da daman kamar a ɗakin Nenen suke duk da ita Jawahir a bangarensu ta ke kwana in ta zo gida hutu a School of Nursing na ABU kongo take karatunta tana Aji biyu.
 Sai wajen tara na dare Yusuf suka shigo gidan tare da Muttaƙa, da Musabahu, ko kafin su shigo ina ta kiran Yusuf ban samu ba, dare ya yi sannan ni na gaji da zaman hankalina ya koma gida ga yaran Halima ba sa jin mgana Hauwa ce ke ta fama da su, ni dai ina zaune nima fama na ke da kaina, girki dai na ta ya Hauwa muka yi saboda Nene.
  Gaisawa kawai muka yi da su Muttaƙa, na ce ma Yallaɓai ya zo mu wuce gida sai ya ce bari ya shiga ciki su gaisa da Nene, saboda ita ta na ciki mu kaɗai ne a falon muna bidiri, sai da mangariba ne ma Jawahir ta shigo nan muna tare da ita.
 Sai da muka ƙara ɓata lokaci sannan mu ka yi shirin tafiya, Hauwa Mijinta mashin gare shi, su suka fara ma tafiya mun rabu akan cewa zata shigo gidana sati na sama, bayan sun miƙa ma nima na shiga na yi ma Nene sallama sannan muka tafi. Yaran Halima aka bar Jawahir da jage jagen su tunda uwar ta su ba lafiya.
 Musbahu ne ya rakomu har wajen mota ina yi masa tsiyan yaushe rabon da ya zo gidana? Ya na dariya ya ce ayyuka ne suka yi yawa shi ya sa ba ya samun zama. Da ya ke shi ya ke zama a gidan bulo ɗin Yusuf, shima gidan bulo ɗin duk ya yi ƙasa ya fi aiki in har an samu babban kwangila na ginin makaranta haka ko kamfani. Kuma sannan yana zama a can ma office ɗin Yallaɓai in baya nan.
 Muna hanya na kalli Yallaɓai ina faɗin" Ya Ranon? An dace?
Hankalinsa na kan tuƙi kafin ya ce" Alhamdulillah."
Ganin ya yi shuru bai yi magana ba ya sa na gyara zama ina faÉ—in" Ka samu kwangilan ne?
Sai ya gyaÉ—a kai kafin ya ce"Muna saka ran haka, wani gidan buredi za a gina shi ne ana neman enginear sai Abba ya yi musu magana. Na je na ga wajen yanzu dai har zanen ni zan yi sai in har an gama zanen sai mu ga in har kwangilan za ta faÉ—a."
Kai na girgiza kafin na ce"To Allah ya tabbatar. Ya kuma ba da sa'a."
Ya amsa da Amin. Kafin ya ce" Su Jidda na gidan Anty Maimuna ko? Kin kira su?
Sai na girgiza kai kafin na ce" Ban kira ba."
 Da sauri ya juyo ya na kallona cikin mamaki kafin ya ce" Me ya sa? Ba za ki kira ki ji ko sun isa lafiya ba?
Ido na sakar masa ban yi magana ba.
Yallaɓai na da mantuwa ne, ya manta abin da ya taɓa faruwa a can baya? Su Jidda sun taɓa zuwa gidanta na kira na ji sun isa lafiya Anty Maimuna ta yi min kaca kaca wai saboda sun zo gidanta shi ne na kasa sukuni to kar na manta ƴaƴa ba nawa ba ne ni kaɗai balle na ƙwallafa rai da su, in ina son zama da yara na saki jiki na yi ta haihuwa ko wasu sun tafi, ba zan damu ba tunda wasu na nan. Tun daga lokacin ko sun tafi wallahi ba na kira na kama mutumcin kaina ba zan kai kaina in da za a gaya min ba daɗi ba sannan na zo na yi ta faman da ɓacin rai ba.
 Ganin yadda na yi shuru ya sa ya ƙyaleni bai ƙara mini mgana ba, har muka isa gida shi ya tsaya rufe get ni kuma shiga ciki ina buɗe ƙofar falo.
 Bai ƙara tada maganar ba har sai da muka yi wanka muka yi shirin barci, har na kwanta kawai na ji sa yana faɗin"Ba ki kyauta ba, ko ma me ya faru ya kamata ki kira ki ji in sun isa lafiya, karki sake irin haka Sadiya."