Sashe 47
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙuramin ido ya yi kafin ya ce" Sadiya kin tabbata zan same ki in naje?
Sai na samu kaina da É—aga masa kai kafin na ce" In sha Allahu." Mirmishi ya yi mini nima sai na maida masa martanin mirmishi.
Shi ya taran min motar haya na hau sannan ya ɗaga mini hannu kafin ya ce"Bye. See you "
Ina so na É—aga masa hannu amman sai na fasa sai dai na gyaÉ—a masa kai ina É—an mirmishi.
Na koma gida a ranar cikin farinciki har sai da Rahila ta fahimci yanayina.
"Sadiya karatun yau hala ya fi miki daÉ—i ne?
Sai na kalleta lokacin ina tsaye ne a tsakar É—akin mu ina mirmishi ni kaÉ—ai ban sani ba har Rahila ta shigo ta kama ni ina ta mirmishi ni kaÉ—ai.
"Me kika gani?
Na faɗa ina kallonta sai ta ƙara matsowa kusa da ni cikin raɗa ta ce"Ko dai?
Da sauri na matsa baya ina faÉ—in" Ko dai me! Ni matsa ki ban waje."
Na faÉ—a ina tureta ina mata dariya. Daga tsakar muka ji Gwaggo na gaisawa da Ya Muntari. Sai na ga Rahila na mirmishi a raina na ce daman haka ake ji in ka haÉ—u da wanda kake so. Sai na daina ganin laifin Rahila akan Yaya Muntari saboda na fahimci haÉ—uwar jini ce.
"Uhm kin ji muryan Yaya Muntari kin kasa sukuni."
Sai ta harareni tana faÉ—in" Ya Muktar dai ko Sadiya?
Ta faɗa ƙasa ƙasa. Ni ko ina ta dariya da gayya na fita tsakar gida dai dai zai koma can waje in da ɗakunsa suke da sauri na ce" Ya Muntari ina yini."
Sai ya juyo yana amsawa kafin ya ce" Sadiya yan makaranta an dawo."
Sai na amsa masa ina kallon Rahila ta cikin É—akin mu tana faman harara ta. Ni kuma ina dariya. Yanzu saboda makaranta an É—auke mini aikin gida sai in ranar weekend ne. Rahila ce da Amina ke yi tun da Ma'u na Minna sai an yi hutu ta ke zuwa ganin gida.
Haɗuwata da saurayin da ban san sunan shi ba sama da sati ɗaya bai zo ba kuma ban ƙara ganin shi ba. Har in na fito daga cikin Jami'a. Na yi ta tsayawa ko da yaushe ina hasashen zan ƙara ganinsa amman shuru sai na fara damuwa. Ko ya zo ne bai gane gidan ba? Ko kuma dai! Na kasa iya fassara yanayin da na ke ji amman na rage walwala da fara'a kamar dai ina so na bayyana damuwar haka. In na kwanta sai na riƙa mafarkin shi tabbacin dai ya samu matsugunni a cikin zuciyata.
 Har na fara fidda rai domin an fi kwana goma da haɗuwarmu . Kamar wasa ranar da ya fara zuwa kofar gidanmu muka san juna sosai ranar laraba ne da yamma da wuri na dawo daga makaranta bayan na yi sallar la'asar na ci abinci sai na ɗan kwanta amma ba barci na ke yi ba. Na ji dai yaro ya yi sallama amman ban maida hankalina a wajen ba.
"Wai Sadiya ta zo in ji wani a waje"
Haka na ji an faÉ—a. Kamar an jeho ne sai gani a tsakar gida ina faÉ—in" Waye?
Haka na faɗa ina kallon yaron Rahila na kan kujeran tsakar gida tana gyaran wake Gwaggo da Mama suna can ƙofar shashen Alhajinmu suna hira Amina na bakin ma zubar ruwa ta na wanke wanke. Gabaɗaya suka juyo suna kallona cikin mamaki.
"Ni ma ban san shi ba."
Sai da na juya ina kallon su Gwaggo sannan na dawo hayyacina. Sai kuma na yi sanyi na kasa motsi.
"Je ka ce tana zuwa."
Mama ta faÉ—a tana kallon yaron. Ya juya ya fita amman ni na kasa motsi daga in da na ke tsaye..
Rahila na dariya ta kalleni ta na faÉ—in" ki koma ciki ki É—an gyara mana! Ko haka za ki fita?
Sai na dawo hayyacina na koma É—aki da sauri na sauya hijabina na duba madubi na gyara fuskata duk ina tunanin shi ne ko ba shi ba ne? Sai dai zuciyata na ta rawa. Na saka takalmina na fito tsakar gida bakina na rawa na ce" Zan je waje."
Gwaggo ce ta tanka ni Mama ba ta ma a wajen ta shiga É—aki.
"To Sadiya. Amma kar ki daÉ—e saboda Alhaji."
Sai na amsa mata na juya na fita Rahila na yi mini dariya ganin yadda na yi wani sanyi ina tafe kamar ba na son tafiyar.
Lokacin da na fita na ci karo da shi a tsaye a ƙofar gidanmu yau ya yi shigar manyan kaya ne. Yana tsaye ya na fuskantar ƙofar gidanmu hannayensa harɗe ƙirjinsa. Na ji lokacin da zuciyata ta ta yi tsalle ta dawo waje ɗaya lokacin da na ganshi. Sannan farinciki ya bayyana a saman fuskata lokacin da muka haɗa ido ya sakar min mirmishi nima na maida masa martanin mirmishinsa lokacin da na ke tafiya zuwa in da ya ke tsaye ya na kallona.
Bayan mun gaisa ina noƙewa kai tsaye ya fara faɗin" Sunana Yusuf Muhammad Inuwa. Ni anan garin aka haife ni amman mahaifina da mahaifiyata mutanen Rano ne. Na yi karatuna har matakin Masters ranar da kika ganni ma a Buk na je ganin supervisor ɗina ne akan project ɗina. Sadiya da gaske na ganki kuma sonki sannan ina son in mun gama fahimtar juna iyaye su shiga ciki domin maganar aure."
Bayan takaitaccen bayanin da ya yi min ban ja aji ba na bashi dama mun É—an jima muna hira har Yaya Abubakar ya dawo ya ganmu suka gaisa da juna. Daga wannan lokacin ba a É—auki wata biyu ba hatta Alhajinmu ya san da Yusuf sannan in ya zo zence a wajena a cikin gida muke yi. Zuwa lokacin kuma ni da shi mun gama shaida muna son juna sannan mun aminta mu zauna kan inuwa É—aya ta aure. Na gama mutuwa a kansa kamar yadda shima ya gama mutuwa a kaina, kowa dake gidanmu na gidajen auran su da mazan gabaÉ—aya su san labarin YALLAÆAI da tun a lokacin na laÆ™aba masa wannan sunann tuni na watsar da tunanin sai na gama Jami'a zan yi aure ba zan iya jira ba gwara na yi auren sai na cigaba da karatuna a É—akin miji.
Ban taba sanin daga ɓarayin Yusuf zamu fuskanci barazana daga dangin sa ba. Duk da ya sha bani labarin gidansu da yan uwan shi na san suna da yawa tunda mata huɗu babanshi ya yi kafin rasuwarsa. Lokacin da muka haɗu da Yusuf a shekaru iyakarsa 27 to 28 ni kuma ina cikin shekarata ta ashirin na kuma san ya karanta Architecture ne masanin zane zane bai samu aiki ba amma yana buga buga. Mutum ne mai sabgogi da yawa da kuma ƙoƙarin neman na kansa.
Yusuf ya turo magabatansa daga Rano. Ya ce mini ƙanin mahaifiyarsa ne da ƙanin mahaifinsa sun zo sun gana da su Baba Aminu an ba su damar dawowata ta gaba za a tsaida mgana. A wannan gabar ne Alhajinmu ya gudanar da bincike a hakan Yusuf har na samu cikakken bayanin waye shi da asalin shi.
*****
Marigayi Alhaji Muhammad Inuwa kafin rasuwarsa ya yi aiki a Ministry of Agriculture and natural resources. Ya rasu a shekaran 1999. Ya bar mata huÉ—u da tarin ya'ya guda 21. A kimanin Æ´aÆ´an da haifa ashirin da takwas ne bakwai sun rasu.
Sannan bayan rasuwarsa da wattani matarsa ta huÉ—u ta bi bayan shi Hajiya karima.
Ɗan boko ne da ya yi shura tun a zamanin baya da boko bai yawaita ba. Sannan sun shiga gwamnati an dama da su sosai ta sanadin wani amininsa Alhaji Yusuf wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Rano. Shima ya rasu tsakanin shi da abokin nashi shekara ɗaya ne shima ya rasu ya bar mata biyu da yaya maza da mata.
Alhaji Muhammad Inuwa da Alhaji Yusuf Tafidan Rano sun fito daga jiha ɗaya ne. Wato Rano sai kuma suka haɗu a makarantar kwana ta Barewa collage dake zariya. Ajin su ɗaya sannan ɗakin kwanan sy ma ɗaya ne. Daga lokacin suka fara aminta bayan sun gama sun nemi jami'a ɗaya ta Usman ɗan fodiyo University. Kowanne ya karanta bangaren da ya zaɓa shi Alhaji Inuwa sai ya yi karatunsa kan harkan Noma da tattalin ƙasa shi kuma Alhaji Yusuf Tafida sai ya kan harkan sanin Siyasa. Bayan sun gama karatun su sun samu manya ayyuka. Shi Yusuf a matsayinsa na jinin sarauta na Tafidan Rano yana da hanyoyin isa ga Gwammatin kano a lokacin. Dukkansu kowanen su ya je ya ƙaro karatu kuma dalilin Alhaji Yusuf Tafida rano Alhaji Inuwa ya tsinci kansa a Ministry of Agriculture na gwammatin Jihar kano a wancan zamanin.
Alhaji Muhammad Inuwa ya fara aure da Hauwa'u(Nene) wacce haifaffiyar Rano ce kuma duk an san juna. Kuma a sha'anin bikin ne Alhaji Yusuf Tafida ya haɗu da ƙawar Nene Aminiyarta Fatima Binta(Hajiyar Tafida)
Sai Aminan junan suka aure ƙawayen junan. Dalilin haka sai zumumcin su ya ƙullu a tsakaninsu mai ƙarfi. Kuma ya samu kafuwa har zamanin ƴaƴan su.
Shi dai Alhaji Yusuf Tafida kafin rasuwar ya ƙara mace ɗaya Hajiya kaltume. Ita ce ke da jibi da masautar kano kuma har ya rasu ƙaton gidan shi na nan a Rano. Amman dai yana da gida a cikin garin kano shi kuma Alhaji Inuwa a cikin garin kano ya gina ƙaton gida a gwammaja mai shashe da yawa daga nan Nene ta fahimci Mijin nata yana da ra'ayin zama da mace sama da ɗaya. Ya kuma tabbatar mata tun da sai da ya yi mata huɗu jeras sannan kuma dukkansu matan sun haifa masa zuru'a.