Sashe 6
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Sai ta bige da yin mirmishi kafin ta ce"kin samu dai kan Yallaɓai ta bakin ki kina yadda kika ga dama, to tunda ya yi miki gida saura mota ko?
Ina riƙe baki na ce"Ni Sadiya? Ai ko kuɗin ya samu kuka ji zai siya mino mota hana shi za ku yi Anty Bahijja"
Kai tsaye Ta ce"Tabbas. Gwara ya yi aure shima ya tara zura'a kar ki manta a gidasu mata huɗu cif ne da kimanin ƴaƴa 21 ban da waɗanda suka rasu."
Ni ko da gayya na ce"Allah ya bashi kuÉ—in da zai wadatamu. Sannan sai ya yo auran miye a ciki?
 Anty Bahijja ta san halina ko Hajiya Maimuna ba na raga mawa, in suka faɗa min cuta zan faɗa musu mutuwa, duk da suna yayyen mijina, saboda suna da ƙananun maganganu sannan sun sakama rayuwata ido, a wasa ne za su yi ta faɗa minI magana
Nima ko a wasa na ke maida musu martani. Anty Zuwaira ce kaɗai ba haka a tsakanin mu saboda ita tana kama girmanta, da yake yar boko ce ga isa da gadara ba ta da ma lokacin tsayawa ƙananun maganganu. Har makaranta private nata na kanta gare ta, sannan ita ma ta kai matsayin Principal a wata makaranta ƴan mata ta cikin gari, sannan uwa uba mijinta a Mininsty of education reshen jihar kano ya ke aiki.
 Ban bar jikin get ba sai da Anty Bahijja ta shiga motar ta ta tafi, ina ɗaga mata hannu bayan na ce ta gaida su Suhailat, sannan na rufe get ɗin na koma cikin gida a falon da muka zauna na koma na sake zama.
Duk a cikin maganganun Anty Bahijja magana É—aya ta fi tsayamin a rai.
Wai da ta ce ni na tsaida haihuwa da kaina, tuni na ji kaina ya fara sarawa abin nan mai ɗaci ya tokaremin a cikin kirjina ya kasa wucewa, wani tuƙiƙi kawai na ke ji kamar zan shiɗe.
Har yau na kasa aminta da ba Yusuf ba ne ya je ya kwance min zani a kasuwa a gaban ƴan'uwan shi ba, tunda ya na da wani hali na faɗi ba a tambayeka ba, sai sai Ma'u ita ce abin zargina na biyu saboda tana auran yaron mai bi ma Mijin Anty Bahijja ma'ana suna aure a dangi ɗaya duk wasu maganganu da suke samu a kaina ta bakin Anty Bahijja ne, ko sunan Sadiya yar laushi da ke bakinta ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba daga baƙin Ma'u ne.
 Wannan yarinyar tun zuwanta gidanmu na san annoba ya zo cikin zuru'armu, idanuwan kowa ya rufe sun kasa gane tsabar makircin Ma'u da ta yi gadon shi wajen uwarta Baaba Asiya ta tsotsa a nono, ban san ina hawaye ba sai da na ji danshin saman kumatuna. Baƙin ciki ya cika min zuciya, me ya sa mutane suke kasa gane wani abu. Mace da Namiji waɗanda ke zaune ƙarkashin inuwa ɗaya ta ma'aurata tsakaninsu sai Allah, ba za ka ji bangare ɗaya ka yankema bangare ɗaya hukunci ba saboda Ubangiji ne kaɗai ya san mai ya ke faruwa tsakaninsu. Ƴan'uwan Yusuf suna ganin kamar komai na ke da shi sanadin ɗan'uwansu na samu Allah na tuba ba kyau tone tone in har da abin da nake dashi ya zauna a hannuna da yanzu na wuce matsayin da nake a yanzu, sun manta a yadda na auri ɗan'uwansu bashi da komai sai kwalin Degree da Masters sun manta gwagwarmayan da muka shafe shekaru sama da goma muna yi tare dashi rana tsaka saboda ya ɗan samu rufin asiri har ana tunanin ya ba ni duniya ina kwance a gida ina hutawa.
 Hawayena na share ina jan ƙaramin tsaki, ni ba domin Yallaɓai ya hana ni aiki ba da tuni ba su ganni ina zaman gidan ba, amman in har ya biyani kuɗina da nake bin shi ina nan da tunanin buɗe shagon Saloon kamar yadda na ke buri. Suna alfahari da wannan gidan su a tunanim kamar ya gama mini komai tunda ya gina min wannan gidan sun manta tsawon shekarun da na kwashe ina zaman haya. Maganar auran sa ba ta gaba na ta lafiyata na ke, na riga na shafa faɗama Yallaɓai cewa ba zan taɓa baƙin ciki domin zai ƙara aure ba amman ya sani kafin ya yi tunanin ƙara aure ya yi tunanin mu ya wadatamu da komai na rayuwa da ni da ƴaƴansa ba kuma mu ba mu wadatatu ba, ya je ya ɗauko mata ta zo ita a wahale mu a wahale.
 Jikina ya yi sanyin da na ƙasa tashi daga kan kujeran da nake zaune. Yallaɓai na kira domin na tuna masa maganar da muka yi na komawata ganin Gynea Asibitin ABU SHIKA.
Ya sake kiran Uncle Abba mu ji yadda suka yi da wani abokin shi da ya ce zai kira a can Zaria zai taimaka mini.
Amman ban same shi ba daman wani lokacin wajajen office ɗin sa ba Network a yi ta neman wayarsa ba a samu.
A shekarun baya wani babban asibitin kuɗi ma'ana private Hospital na yi ta wahala da jelangen zuwa ba wani cigaba sai cin uban kuɗi sai aka bani shawara na koma babban asibiti ko Aminu kano ko ABU Shika da ke Zariya. Yallaɓai ya so na zaɓi Aminu kano, ban san me ya sa tunani na ya fi karkata da gwara na fara ganin likita a Asibitin Shika ba. Shi kuma daman Yallaɓai ya na girmama ra'ayina da buƙatuna shi ya sa bai hana ni ba.
Daga nan sai na sake buɗe data Group ɗin mu na BUK ya fara ɗaukan Hankalina saboda na ga ana ta massages da yawa kuma ni dai nasan tun da muka gama makaranta ba wani mgana ake yi sosai ba. In magana ta yi yawa to ɗayan biyu ne ko rasuwa ko an samu ƙaruwan aure ko na haihuwa.
Â
 Ina shiga ko sai na ga Hauwa Jamilu ce ta haihu ƴ'a mace, ƙawarta Samira Aliyu ne ma ta tura hoton Baby da sanarwan haihuwan, na ƙurama hoton Baby ido mai kyau da ita. Ina son haihuwa ina son na ƙara haihuwa har a cikin raina, ko a ina naga an yi haihuwa sai na ji dama ni ce ko da ace daga shi in na yi ba zan ƙara haihuwan ba.
 Tagging na yi sai na yi mata barka a ƙasa kuma nace zan kira wayar ita Hauwan, duk da ban da wata ƙawa sanda muka yi BUK amman kuma ina gaisawa da mutane. Daga baya ma bayan mun gama makaranta na fi zumunci tun da in aka yi rashi ko ƙaruwa ko ban je na kan kira waya in kuma za a haɗa gudummuwa na kan tura nawa. Ina yin maganar Samira na Online ta yi min Reply.
"Amin Amin. S Yashe ku kam dai kun gama ko?
Â
Sai na ba ta amsa da cewa" Mun gama me Samira Aliyu?
"Haihuwan mana, kin daɗe fa ba ki ƙara haihuwa ba ina jin"
Emojin mirmishi na tura mata ban yi magana ba. Ina gani Maijidda Bala, ta yi tagging ɗin maganar Samira da cewa" Ƴan boko ne matar Injiniya guda ko matar Yallaɓai zan ce?
Sai da na yi dariyan Sarari saboda ko username ɗina Sadiyar Yallaɓai ce a rubuce.
 Kuma Maijidda Bala anguwanmu ɗaya, ta san gidanmu na san na su , duk halina na rashin son sakewa da mutane amman Maijidda na zuwa gidanmu saboda Rahila, to daman duk wanda ya zo gidanmu saboda Rahila ce ko Ma'u su ne masu jama'a. Ba zan taɓa mantawa da maganar Mama tun muna ƴan mata ta sha ce mini" Ke kam Sadiya da wuya ki ta shi aure ki ga jama'a. A yi mutum ba shi da son shiga jama' a kwata kwata."
A lokacin dariya na kan yi kafin na ce"Shike nan sai ke da Gwaggo ku ci min ƙawayen amarya."
 Allah Sarki Mama Allah ya sa kina aljannah. Ban biye ma mangaganunsu ba na sauka saboda kar na manta nan take na kira Hauwa na yi mata barka, har tana mini tsiyan ni na gama na ji daɗi na. Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba. Saboda ko me zan ce ba za ta gane ba sai da na ji tana faɗin"Nima daga wannan na faɗa ma Baban Afnan na gama wallahi. Allura zan je a yi min na shekara biyar."
Da sauri na ce"Kul ɗin ki Hauwa. Karki yi wannan gangancin, in kika tsaida haihuwa na shekara biyar to za ki yi ta nadama har na shekaru ashirin ba ki daina ba. Saboda lokacin da kike son ki ƙara haihuwan ba za ki samu wannan damar ba."
Â
 Na faɗa ina jin raɗadin abin a cikin raina Hauwa ko cewa ta yi" Ko Sadiya? Sai kawai na rausayar dakai kamar tana ganina kafin na ce" Ku yi na gargajiya ko na musulunci Hauwa. Saboda haka ina gargaɗin ki in ba so kike yi ki ƙare a zuwa gaban Gynea ba."
Hauwa na jin haka sai ta ce to shike nan za ta yi magana da Daddyn Afnan duk yadda ta so na yi mata wata mgana ban yi ba saboda ba close na ke da ita ba, rayuwa ai darasi ne amman da zan buɗe mata cikina sai ta ji tunanin da ke cikin ranta ya fita ba domin komai ba sai tsira daga faɗawa irin halin da ni na faɗa.