← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 76

Sashe 23

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Mayafi na ja na saka, sai na haɗa da bakar jaka da takalmi mai saukaƙƙen tudu.
Atm É—ina daman yana tare da ni da duka takarduna. Sai na saka 5k É—in da Yaya Hamza ya ba ni a cikin jaka, ina shirin fitowa Khaleesat ta sanyo kanta É—akin sai muka haÉ—u a kofar É—akin..
 
"Har kin shirya wai?

  Ina nuna mata jakata na ce" Ga shi ma kin gani. Gwara na tafi da wuri tun da kin san da ɗan tafiya."

  "Haka ne. Amman a ina kika san asibitin?

Mun fita falo tare da ita lokaci É—aya ina faÉ—in" Kin manta can Tasleem ta kwanta lokacin da kika haife ta?

  "Oh! Kin ga har na manta kuwa."

  Ta rakani har ƙofar gida ta na jaddadamin na samu Adaidaita zuwa pizzet daga nan sai na hau na Shika ɗin. Sai na amsa mata da toh, ta in ban gane wani abu ba na kira ta, ina dariya nan ma na ce mata in sha Allahu.

  Haka ko aka yi na samu Adaidaita zuwa pizzet, daga can akwai ƴan sahun da suke yi lodin samaru har Shika ita na hau, ta cika da wuri, mu uku ma duk shikan za mu je, sauran ne za su tsaya a samaru.

  Muna hanya Yallaɓai ya sake kirana na ce masa ina hanya in mun isa zan kira shi. Na sauka Main get na asibitin Shika na duba agogon da ke ɗaure a tsitsiyan hannuna tara da mintina sha biyar, bayan na sallami mai adaidaita na shiga ta babban get ɗin.

  Ban kira Yallaɓai ba sai da na kira lambar Dr Fadil kamar yadda muka yi alkwari sai dai bai ɗaga kiran ba, sai na wuce ta can babban falon da ke kusa da main get, na samu waje na zauna asibitin ta cika da zirga zirgan mutane ballatana yau ɗin monday ne, ga marasa lafiya nan birjit ana ciwo Allah dai ya bamu lafiya.

  Na sake kiran Yallaɓai na ce masa na sauka ina cikin asibitin amman na kira Dr Fadil bai ɗauka ba, sai ya ce na ƙara kiran shi tun da ma ya ga da sauran lokaci ƙila bai shigo asibitin ba ne.

  Mun gama waya da Yallabai kenan Uncle Abba shima ya kirani bayan mun gaisa ya tambayeni ko ina cikin asibitin ne? Sai na amsa masa sannan na gaya masa na kira wayar shi ta shiga amman bai ɗauka ba sai ya ce bari ya kira shi.

  Na ɗan yi zaman sama da mintina ashirin, data na buɗe ina duba istergram na wata Hamida makeup , ina following ɗin ta sosai saboda ta iya kwalliya so na ke yi ma na shiga class ɗin ta za ta fara farkon wata gaba anan kano ne na wata ɗaya akan kwalliya, na rage Volume ina ta kallon Videos ɗin kwalliya daman ni duk sune na ke following a wayata,  ina cikin duba dube na sai ga kiran Dr Fadil da sauri na ɗaga kiran gaisawa muka yi sai ya ce yana hanya yanzu zai ƙariso ina ina ne? Sai na gaya masa sai ya ce na jira sa ga shi nan zuwa.

  Bayan nan kuma na sake wani zama na tsawon mintina goma sha biyar sai ga kiran shi Again ina ɗauka ya ce" Ga ni a babban falon, ko za ki iya miƙewa ko zan gane ki?

Ina jin haka na mike na juya daman a kujerun baya na zauna duk an ma cika na gaba gaba, waige waige nake yi saboda akwai mutane sosai kuma na ga masu waya sama da mutane goma.

  "Wani kalan kaya ki ka saka?

  Sai na amsa da ina sanye da jan mayafi, sai ya ce kawai ya ganni daga nan ya kashe wayarsa, har ga Allah ni ban gan shi ba sai da na ga wani baki dogo sanye da suit da rigan likitoci a hannunsa tare da briefcase, fuskarsa sanye da wani siririn gilashin, ganin ya na min mirmishi ya sa na fahimci wannan ne Dr Fadil.

  "Sadiya Right?

  Haka ya faɗa bayan ya tsaya a gabana da sauri na amsa masa sai ya yi gaba yana faɗin"Biyo ni, sunana Dr Fadil. Ni ne Abdulmu'iz ya ce zan taimaka miki.'"

  Ina bin sa a baya na ce"Ina kwana"

Ya na yar dariya ya ce ai mun gaisa a waya, sai ya dan tsaya har na karoso mu ka jera yana min bayani zan siya domin na buɗe fayel, agogon hannunsa ya duba kafin ya ce"Da fari na so ki ga Dr Nayama ne amman ta ɗauki Annual leave ɗinta last week amman na samo miki appoitment da Dr Fatima Tasiu, ba ki da matsala na ce ke ƙanwata ce saboda haka mu je a siya katin sai na raka ki can in da za ki gan ta."

  Muna tafe ina yi masa godiya, Ban sha wahala ba muna zuwa wajen biyan kudin kati bai ma karɓi kuɗina ba ya siya mini sannan muka je ya nuna recip ya karɓo mini kati aka buɗe min fayel, kuma ya ce a bashi Fayel ɗin da ƙaramin katin a hannunsa shi zai kai ma Dr Fatima, daga nan mu ka fara tafiya zuwa bangaren Gyea ɗin ni kuma ina tambayansa nawa ne aka kashe da niyyar na bashi kuɗin sa?

  Sai ya kalleni ya na dariya kafin ya ce"Haba, ke ba ƙanwar Abdulmu'iz ba ne?
Kallonsa na yi saboda ina so na tuna da sunan da ya ambata.
Sai na tuna da Uncle Abba ya ke mgana.

Sai na rausayar da kai kafin na ce" E. Amman ina auran yaron Yayarsa ne. Sannan aminaine tare suka tashi da mijina."

  Sai ya ɗan juyo yana kallona kafin ya ce"Oh. Nima Babana ɗan Rano ne, amman kaduna muka tashi mun haɗu da Abdulmu'iz a BUK ne kafin na samu scholarship zuwa Singpore."
 
  Sai na jinjina kai alamun gamsuwa, muna tafe yana gaiswa da mutane sannan jefi jefi ana kiransa a waya, mun isa shashen Gyea ɗin akwai likitoci da mutane suna ta layi, amman da ya tambayi Dr Fatima sai a ka ce ba ta riga ta iso ba, sai ya ce na zauna na jirata bayan ya ba ni fayel dina ya ce na riƙe zai mata waya ya faɗa mata in ta iso ni za ta fara gani, na yi ta masa godiya ya ce in akwai wata matsala na kira shi, shima zai wuce bangarensa ne akwai patient na jiran sa.

  Aka ce mai nema baya fushi, mun yi zama sama da awa ɗaya, wasu ana ta kiran sunan su suna shiga wasu offices ɗin. Ni dai ina zaune mun yi magana da Yallabai na faɗa masa yadda ake ciki gani dai ina jiranta, ban gaji saboda na saba sama da shekaru bakwai ina zuwa ganin likita zaman bai wani dame ni ba  tun da ga waya a hannuna ina ta latsawa.

  Hankalina ya tafi kan waya har ga Allah ban san ta ina likitan nan ta zo ta wuce ba, ni dai kawai na ga wata mace da fararen kaya ta fito tana kiran sunana.

"Wacece Sadiya anan?

Ina shirin na ce ni ce, sai na ga wajen mutane uku sun É—aga hannu, sai ta tsaya tana kallonsu kafin ta yi tsam sai kuma ta ce" Wacce Dr Fadil ya kawo?

  Sai na yi saurin miƙewa ina faɗin" Yes Ma.".
Sai ta kalleni akwai fayels a hannunta, kafin ta ce na biyo ta, da sauri na É—auki jakata da Fayel É—ina na bi bayanta har zuwa wani office dake gefenta tana gaba ina bin ta a baya.

  Likitar na zaune a saman kujeranta, kanta na kasa tana rubuce rubuce akan wata takarda.

Wacce ta shigo dani ta bani izinin zama sannan ta fice ba tare da ta yi magana ba, zama na yi a kan kujera na zaman marasa lafiya, Office É—an daidai akwai wani kato a ciki sai wata kofa ina tunanin kamar Tiolet ne.

  "Fayel na ki."

  Haka kawai ta ce mini har lokacin ba ta ɗago ba, sai na miƙa ma ta ta saka hannu ta karɓa lokaci ɗaya tana gyara zaman gilashin da ke idanuwanta.

  Ta duba sannan ta fara rubutu a jikin Fayel ɗin kafin ta ce"Kin zo da Report ɗin ki na baya?
Kaina na gyaÉ—a kafin na yi saurin buÉ—e jakata na É—auko su na tura mata gabanta ta É—auka ta fara dubawa É—aya bayan É—aya sama da mintina goma.

"HalimatusSadiya Sulaiman Yashe"

Na amsa mata da Yes Mah."

  "Ke ƴar Yashe ce?

  Sai na amsa da eh kafin na ce"Alhajinmu ɗan can ne."
Na faÉ—a ina kallonta sai a lokacin ta É—ago na ganta da kyau fara ce tar, a shekaru sai dai mu zo tsara ko za ta girmeni da kaÉ—an ne, tana sanye da rigar likitoci ta yane kanta da mayafi baki sai siririn gilashin da ke saman fuskarta.

  Sai na ji gabaɗaya ta burgeni. Har na shagala da kallonta.

"Haihuwanki nawa kafin ki yi planning?

"ÆŠaya."

Da hausa take yi mini magana nima ina maida mata da hausa, kanta na ƙasa tana ta rubuce rubuce.

"Na how many month kika yi alluran?

"Five years"

"Amma na 6 months na riƙa yi"

Sai ta É—ago ta kalleni kafin ta maida kanta ta cigaba da rubutu a saman fayel É—ina.

"Bayan haka, kin sake haihuwa?

Na amsa da E. Sai ta ce When, sai na ce bayan first born É—ina ta shekara tara.

"Wani symptoms ki ka samu kafin ki sami ciki da kuma bayan kin samu?

"Na samu matsalan zubar jini, sannan ga juwwa da ciwom mara, daga baya na fara ramewa sannan bayan nan na daÉ—e ban samu ciki ba sai bayan shekara tara ga rikicewar al'adata."

"Bayan kin samu cikin fa?

  "Bayan na samu ciki na wahala, domin har lokacin ban daina zubar jini, sai da na je asibiti aka ɗora a kan mgani. Na sha wahala da ban ma iya haihuwa da kaina ba sai da aka yi min C.S."

"Na gani a rubuce an É—ora ki kan magani domin tsaida jinin ko?
Chapter 23 · 0% Book details