← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 76

Sashe 59

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin sati ukun da suka gabata lamarin Gimbiya ya fara ba ni mamaki har na fara tunanin ko ba ta da tawakalli ne kuma har sai da na furta ma Yallaɓai har ya ji haushina. Haba abun nata ya yi yawa ba kanta farau rashin miji ba Allah na tuba sauran matan shi da suka yi shekaru aru  aru da shi ma sun ɗau dangana haka ma ƴa'ƴan shi da suka rasa uba suma sun dangana amman ita ba alamun dangana a lamarinta.

Na tuna ni kaina fa uwata ba ta a duniya nan na ɗau tawakalli Yallaɓai ba shi da uba shima ya ɗau dangana. Har wani lokacin in na jin masa shaƙiyanci ko ina son ya yi min wani abu ya ce ba zai yi ba sai na marairai ce ina faɗin." Yallaɓai ka tausaya mini ka ga ni fa marainiya ce.'

In na ce haka a lokacin sai ya yi dariyan nishaÉ—i kafin ya ce" Au ke sai yanzu kika san ke marainiya ce? Mu ai mun daÉ—e cikin maraici kuma ba mu mutu ba."
Ko kuma ya ce" Ke ba marainiya ba ce Alhaji ai bai mutu ba ko kin kashe shi ne? In ya faɗi haka daga ni har shi sai mun ƙyalƙyace da dariya. Saboda mun yi shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma Annabi muhammdu manzonsa ne, sannan rayuwa da mutuwa duk ta na hannun shi ne.

Sai dai ta bangaren Gimbiya ba ta san wannan ba, tun da a ka yi rasuwar nan saboda ba ta jin mganar kowa sai na Yallabai a rana ban san adadin sai nawa ya ke kiran waya a ba ta ba, yana lallashinta ta samu ta ci wani abu. Ko in ta fara kuka sai su kira shi su ba ta ya yi ta mata nasiha, duk wannan ƙokarin da ya ke yi mata ba ta dangana ba. Bayan wanda yan'uwa ke yi mata shima duk bai sa ta dangana ba. Tun ina tausayinta har ta koma ba ni haushi. Na yi ta tunanin ita ko wani irin so ta ke yi masa haka. ko dai garken yaya ta tara da shi sai haka amman aure duka duka wata ashirin ba ciki ba goyo haba lamarin nata ya yi yawa har na fara gajiya da jin labarin halin da ta ke ciki a bakin Yallaɓai in yana faɗa min Daughter ta zama abin tausayi, tun in yana faɗa ina nuna jimami har na daina saboda lamarinta ya wuce na musulma mai tawakalli ya koma hauka da jayayya da ubangiji.

Nan  ko sati ba a yi ba sai da Yallaɓai ya koma Abuja ya kwana ɗaya sannan ya dawo. Wai ta shige ɗaki tun safe ta rufe kanta tana kuka kuma tun daren jiya ba ta ci komai ba su Nene sun yi sun yi da ita ta buɗe ta ƙi har azahar shi ne Nene ta kira Yallaɓai a waya ta ce ya bar duk abin da ya ke yi ya zo Abuja. Shi ne fa ya na ma office ya dawo gida ya na faɗa min tare da cewa na haɗa masa kayan tafiya na kwana ɗaya tun da ba zai yuyu ya je a yau ya kuma dawo ba.

A lokacin ne na furta masa abin da ke zuciya ta.

"Haba kamar dai ba ta da tawakkalli. Wai kanta farau mutuwar miji?

Na faɗa ina mai sakin  tsaki tun da shima yana kan aikinsa ne amman an wani ta da shi zuwa Abuja. Ni ina ganin gulma ne ace duk cikin yan'uwanta da suke uwa daya uba ɗaya mata da maza ba ta ga wanda za ta riƙa jin mganarsa ba sai Yallaɓai da zaman da ya yi a gidansu na ɗan lokaci ne, za a ce ya fi mata yan'uwanta da suka fito ciki ɗaya ne?

Tsawa Yallaɓai ya daka mini kafin cikin ɓacin rai ya kalleni ya na faɗin" Sadiya wannan wani irin mgana ne?

Kallonsa na tsaya yi saboda sai na ga kamar ban faÉ—i wani abu mara kyau ba.

"Me na ce? Gasikiya na faÉ—a hakuri ake yi. In ta na wannan abun kamar tana faÉ—a da Allah ne."

Kawai sai Yallaɓai ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Wai na san zafin mutuwan miji kuwa.?
Ni ko kai tsaye na ce" Ban san na miji ba. Amman ai na san zafin mutuwar uwa ko?

Na faɗa ina kallon shi saboda na ga zai wani hau kaina daga faɗin gaskiya saboda ma na ƙara kunsa ma sa kai tsaye na sake faɗin" Kuma na tabbata ba yau aka saba mata rashi ba. Ai ta rasa uba da yan'uwata me ya sa ba ta yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ku yi mata faɗan ta zama mai tawakkalli kuka ko rufe kai a ɗaki ba shi zai kawo mafita ba."

Ni kaina tsaye na ke mgana kuma shi kan shi Yallaɓan ya san ni.
Amman a mamakina kai tsaye ya kalleni kafin ya girgiza kai ya na faÉ—in" Na yi miki uziru saboda ba ki san zafin mutuwar miji ba. Amman ba shi zai hana na ce ba ki da tausayi ba Sadiya."

Baki buɗe na kalli Yallaɓai ya na sauya kaya cikin nuna kaina na ce" Ni ce ba ni da tausayi Yallaɓai?
Kai tsaye ya ce" Ƙwarai da gaske. Domin duk mai tausayi tausaya ma halin da Daughter ta ke ciki zai yi ba maganganun banza marasa tushe ballantana makama ba. Shirme kawai."

"Daga faÉ—in gaskiya?

"Ki riƙe gaskiyan ta ki ba a so."

Haka ya maida mini amsa a fusace.

Ajiyar zuciya kawai na sauke domiin na ji raina na tafarfasa zan iya maida masa martani amman sai na ƙyale shi, ɗakin na bar mishi kayan na shi ma ban gama haɗawa ba na ce ya haɗa da kan shi tun da da ga faɗin gaskiya sai na yi laifi ya je can ya tare saboda kula da ita. Da zai tafi ko sallaman da muka saba ba mu yi ba, shima fuska a haɗe nima na haɗe nawa ko haraba ban raka shi ba, daga falo na yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya.

Amman Yallaɓai ya ba ni mamaki, yadda ya wani ɗau zafi daga fafin gaskiya. Wani abu ke tsaya min a maƙogwaro in na ji yana ambaton ta da Daughter ƙatuwar mace shima ya na namiji  magidanci da wani sanabe da iyayi.

Har ya je ya yi kwanan É—ayansa ya dawo ba mu yi waya ba. Ya san halina yadda bai kirani ba nima ban neme shi ba su Jidda suna ta tambayan Abba na ce ya ta fi Abuja.
Da ya dawo ban yi masa tarban da na saba ba. Ni ban haɗe rai ba sannan ban sakar masa ba, sai dai lokacin da ya dawo sai bai dawo da fushin ba. Shi ya fara saki sai nima na saki amman na so ya cigaba ya sanni ni sai na iya gaba dashi ba wani abu mai wahala ba ne a wajena. Amman kalmar ba ni da tausayi da ya kirani da shi ya taɓa ni kuma sai da na yi masa mgana sai ya ce na yi hakuri amman nima ai bai dace na ce haka ba, kenan har a lokacin bai ga gaskiyan abin da na faɗa ba to ai shike nan ni kuma na saka a raina ba zan kara mgana ba.

Abin da ma ya faru a can ɗin ban tambaye shi ba shi da bakin shi ya ke faɗa mini Ulcer ta kama Gimbiya sannan kuma jininta ya hau sai da likita ya zo gida ya duba ta. Bakina ƙanin kafata na ce Allah ya ba ta lafiya domin na fahimci Yallaɓai kiris ya ke jira da ni ya yaɓa mini mgana.

Bayan arba'in da kwana uku Gimbiya ta dawo Rano. Mimisco ta je tare da ita ma aka maida ta rano. Sai yayyenta maza da suka je saboda sun gana da yan uwan marigayin da yaran shi. Farko sun nuna ba su so tafiyar ta ba sun nuna gwara ta zauna a gidanta ta gama takaba sai su kuma ƴan uwanta su kawo dalilin halin da ta ke ciki in ta koma gida ta na ganin mutane za ta samu ta dawo dai dai ba kamar zamanta anan ba, da haka suka amince ta koma gida amman sai da aka kai ta duka gidajen matan ta yi sallama da su. Suna kuka tana kuka  an kwashe mata duka kayanta a ka rufe gidan aka mika makullin ga iyalanshi tunda sun ce suna kan tatrara abin da ya bari ne bayan an gama za a bincika in da baahi a biya in babu kuma in lokaci ya yi za su nemesu domin rabon gado.

Gimbiya ta yi sallama da garin Abuja, aikin nata ba mganar shi daman tun da aka yi rasuwar ba ta je ba. Ana tunanin in komai ya lafa a yi mata transfer ko zuwa cikin garin kano ne. Kwana biyu tsakani da dawowarta na je yi ma Nene bangajiya tun da sai da ta ƙara kwana a Reno sanman ta dawo gida ita ce ma ta ke bani labarin abin da ya faru kafin ta tahowar su.

"Allah sarki. Allah ya yi mishi Rahama ita kuma Allah ya ba ta dangana."

Nene ta amsa da Amin kafin t ce" Ai an fara karɓa mata rubutu wajen wani malami a can rano. Da safen nan mun yi mgana da Hajiya ta ce ta fara sha da safe. To Saudatu ta rame ta lalace ta fita hayyacinta. Rayuwarta akwai tausayi sosai."

Nene ta ke faɗa cikin rawan murya.   Ni kuma sai na ce" Har yanzu ba ta fara dangana ba Nene? Sai ta ce a hankali dai amma in na ga Saudatu sai na tausaya mata.

A gidan na yini ina nan Hauwa da Munirra suka zo da su Suwaiba domin yi ma Nene gaisuwa da barka da zuwa kaf ahalin gidan nan Yaya Usman ne kawai bai zo ba da Anty Zabba amman dai sun yi gaisuwa ta waya, har Muhammad Kabir da Nafisa sun zo gaisuwa daga katsina.
Chapter 59 · 0% Book details