Sashe 49
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saboda sanin Yusuf a harkan kwangilan gine gine sunan shi ya ɓace daga Yusuf zuwa Injiniyan da ya yi ma haye. Sannan da tsarina da shawarata mu ka samar da sunan kamfanin shi. HM TAFIDA AND SON LIMITED." Hauwa' u and Maimuna kenan da sunana ya so ya saka saboda gudun mgana na ce mu saka na ƴaƴanmu.
A can zariya road ya kama office ɗin kuma ya yi ma kamfanin sa rigister. Ya taimaka kwarai wajen samun kwangiloli masu tarin yawa. Kuma balle ya san jama'a connenction ɗin shi da mutane yasa har Gwamnati na bashi aikin kwangila. Akwai kwangilan da ya samu na gina wata makarantan koyon aikin Jinya ta ƙanin marigayi Alhaji Yusuf Tafida. Wanda shi ne yanzu a matsayin Tafidan rano yana aiki a ministry of education. Yusuf ya samu alheri sosai da shi ya ƙarisa mana gini sannan na bashi shawaran ya buɗe gidan buɗo saboda yanayin aikin shi. kuma ya yi na'am cikin lokaci kaɗan ya buɗe gidan Buɗo. Mun tare a sabon gida bayan ɗaukan shekaru sama da biyar ana ginin shi. Tsarin gidan da komai tsarina ne Yusuf kuma ya yi zanen sanan yan kwangilanshi suka gina gidan da jagorancin.
Tarewarmu a anguwan lodge road. Yusuf ya hana ni aiki ya ce na zauna a gida na huta. Duk da ina da ra'ayin fashion na shiga makarantar koyon kwalliya da gyaran kai. Har zanen shagon da Yusuf zai buɗe mini ya zana amman har yau bai tabbata ba. Amman hidimdimu ba za su bari hakan ya samu ba. Tun da muka koma wannan gidan ƴan'uwansa suke tunanin ina can na samu daula kuma ban haihuwa sai kwanciya ina cin daula sun manta irin gwagwarmayan da muka sha a baya komai Yusuf ya samu ko ya mallaka tare da ni aka mallake shi. Ko bayan tarewarmu a sabon gida sun so ya ƙara aure domin Gimbiya ba ta yi aure ba har Masters ta yi. Da ta ga dai Yallaɓai na Sadiya ne ita kaɗai sai ta hakura ta auri wani tsohon sanata matansa uku ita ce ta huɗu. Ta na can Abuja kuma har ta samu aiki da NGO.
A shekaru sama da goma sha huɗu da wattani da aurena da Yusuf na san me ake kira aure da gwagwamarya. Ba zan ce ba mu taba samun matsala ba mun sha samu tun da ni ina da saurin fushi ga baki shi kuma yana da sanyi wani lokacin amma in ya yi fushi ba shi da kyau. Mun sha samun matsala akan ƴan uwan shi mussaman Anty Bahijja da Anty Maimuna. Daga karshe shi sai ya bi bayan ƴan uwan shi ya bani rashin gaskiya. Nene dai ba na ce ta taɓa nuna mini kiyayya ba. Ban taɓa samun matsala da ita ba shi ya sa na ke yi mata biyayya iya iyawata. Sannan akan zamantakewa ma muna samun matsala amma sai mu shirya kan mu a tsakaninmu. Amman matsalan da muka sha samu da ya yi ƙamari shi ne akan Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure. Yusuf ya samu kusanci sosai da Gimbiya itama kuma ba ta sakin jiki da kowa sai shi in na nuna fushi ko kishi sai ya ce ina da matsala ina da zargi. Kuma sai ta zo gidan Nene shi kuma in ya je ya biye mata ya kai dare har kwalliyan da na yi sai ya lalace in na yi mgana sai ya ce bai san lokaci ya tafi ba suna can suna hira da Gimbiya. Ban samu salama ba sai da ta yi aure sannan na ji hankalina ya kwanta amman fa da in na ji zai je Rano yini na ke yi zullumi.
Da shekaru suka gangara haka sai nima na fahimci an gogi jigida. Na daina matsa ma kaina kan wasu abubuwan tun da na fahimci ni ba zan ga karshen su ba nima ba za su ga karshe na ba. Sannan irin wannan matsalolin ana samun su a kowani dangi. Sai dai na wata ta fi wata. Nene ce dole ne ita ne kawai ban daina yi ma biyayya ba amman sauran duk abin da na ga zan yi shi na ke yi. Na daina tsoron a ce na yi ko ban yi ba saboda shekaru sun gungura nima wuyana ya isa kaurin da na isa ga kaina. Shi ya sa na ke tafiyar da rayuwata da ga ni sai mijina sai ƴaƴa na. Sauran abin da ya fi ƙarfina na bar ma Allah ni yanzu abu ɗaya ne a gaba na. Ina son na ƙara haihuwa ko domin Yallaɓai mai son yara sosai.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWAR GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿ï¸14*
Present.
Da safen tea muka sha gabaɗayan mu amman ban da Yallaɓai saboda kamar akwai gajiya a tare dashi. Tun bayan da ya dawo daga sallar asuba ya kwanta yana ta barci sai na ƙyale shi tun da na ga har wayarsa ma sai da ya kashe.
Da wuri Saude ta zo na saka Jidda ta fito da kayan na su. Daga kitchen ɗina akwai wata kofa dake fidda mutum ta can baya in da muke yin wanki ko shanya. Ko tara ruwan sama can na ce su je su yi wankin har da Baby da ta saka rigiman sai ta yi na ce a ƙyaleta ta yi.
"Umma ba fa wanki ta iya ba. Æata jikinta kawai za ta yi da ruwa."
Ina É—akin na su ne a lokacin ina gyarawa saboda Saude ba za ta samu lokaci ba gwara ni na gyara gidan.
Kallon jidda na yi da ta shigo kawo min karan Baby.
"Bar ta yi. In ta jiƙa jikinta ai shike nan ta huta."
Haka na faÉ—a ina mirmishi saboda ni dai na san ina kamar ta ban so aiki ba amman tunda tana so ai ba zan hana ta ba. Wucewa Jidda ta yi amman ranta bai so ba sai na bi ta da kallo ina dariya.
Jidda akwai son aiki da karambani in da ta biyo ni da na shiga uku. Har yanzu da shekaru suka tura ba na son aiki barin ma girki, ko anan domin ya zame mini dole ne na ga ba mai yi mini. Saude daman in ta zo sai dai na saka ta yi ma yara. In da Allah ya so ni da Rahama Yallaɓaina bai da tsirfan cewa ga abin da zai ci duk abin da na kwaɓa na bashi yana maraba.
A baya kafin na samu Saude na wahala sai dai in Marwa ta zo mini hutu. Marwa babbar ɗiyar Yaya Aina ce. Lokacin da ta ke gida kafin ta samu makarantar koyin aikin jinya a garin tsafe na more ta saboda yarinyar tana matuƙar sona. Shi ya sa nima na ke son ta ina kuma kyautata mata. Ba ta zuwa gidan kowa hutu sai gidana in ta zo ba na komai sai dai na ci na kwanta Yallaɓai ya yi ta mini tsiyan daman haka na ke so na kwanta na yi ta laushi ni kuma na ce na ji ba komai.
Marwa ba ta da ƙiyuwa. In ta zo har wankin kayana da guguna tana yi min kayan su Jidda sai dai na fito na ga ta wanke ta shanya, budurwa ce mai kimanin shekaru 20 zuwa da ɗaya.
Duk da ni da uwarta ba sosai muke yi ba amman kuma Allah ya haɗa jinina da Marwa kuma ina daraja haka saboda yaran Yaya Murja ba sa zuwa gida na amman gidan Ma'u kam suna zuwa mata hutu. Har gwarama Firdausi ta wajen Yaya Balki ta kan zo wajena ban da su Anti. (Aina) sunan Yaya Aina a ka sanya mata sai ake kiran ta da Anti ita ce babba a ɗakin Yaya Murja ƙannenta huɗu duk maza ne. Ni bai dame ni ba domin kowa ya san halina ka yi da ni, ya ka ƙare ballantana ma ba ka yi da ni ma gabaɗaya.
Allah na tuba gari da yawa ai maye ba ya ci kansa ba shi ya sa ina yi ma Marwa abin alheri har ɗinkuna ina yi mata lokacin da ta samu makaranta tsafe siyayya na yi mata mai yawa kuma har da ni a masu rakata, sannan in dai ta zo gida hutu ko da ba za ta daɗe ba sai ta zo gidana ba ta daɗe ba ta yi mini sati ɗaya. Sau tari in zan siya abin mata na kwalliya uku na kan siya saboda Marwa. Ita tunda ta fara amfani da su bra da pad in dai na fita kasuwa siyayya ina siya mata na ijiye in ta zo hutu ko ba ta zo gidana ba ina aika mata dashi na ce Yaya Aina ta iijiye mata. Ban taɓa jin na damu da ta gode mini ba koma me na yi nima ai uwar Marwa na ke, kuma abin da ke tsakanina da mahaifiyarta ba zai taɓa shafanta ba.
Ko kafin in gama gyara gidan har sun gama wankin duk da bai da wani yawa daga uniforms ɗin su sai kayan barcin su. Ko daman ita Saude akwai ƙokari a shekaru iyakarta 17 ko ta gota da kaɗan ne. Na ɗan taya su shanya wajen sharce kayan. Bayan mun gama na ce Saude ta yi ma Baby tsifa ita ma Jidda ta kwance kan ta in wanke musu. Tun da ba su samu zuwa kitso ba sai in yi musu da kaina.