← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 76

Sashe 53

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin" To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. "
Cikin nuna mamakin na ce"Wai har yanzu ba ta koma ba?
Munnira ta ce" Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman É—in zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma"
Ina mata dariya na ce" Wallahi haka za ta ce."

Munnira ta kama haɓa kafin ta ce" Shi ya sa ban kira ba. "
Na ce gwara hakan itama Munira ta na faÉ—in ba ta ji daÉ—i ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba.

"Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su."
Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran.

"Yallaɓai ka taho ne?

Cikin wani irin murya ya ce min" Sadiya ta congratulation."
Ina yar dariya na ce" Yallaɓai ka biya mini makka ne?
Shima dariyan ya yi kafin ya ce" In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faÉ—a miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano."
Cikin murna na ce" Don Allah fa Yallaɓai"
"Allah Sadiya ta. Yanzu kuÉ—in suka shigo sun kuma kirani sun faÉ—a mini."

ÆŠakin Mama na faÉ—a ina faÉ—in" Alhamdulillah mun yi kuÉ—i"
Ya na yar dariya ya ce" In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare"
Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi.

Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma'u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha'i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama  muka tafi gida.
Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce" Yanzu da me zamu fara Hajiya ta?
Ina dariya na ce" Mu je gida mana Alhajina."

Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce" Ranka ya daɗe  mai girma Tafida."
Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari
"Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya"

Ya na dariya ya ce" Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce" Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so."
Gira ya ɗaga min kafin ya ce" Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa."
Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka.

Baki sake na kalle shi kafin na ce" Au ban iya ba ko?
Ya na kallona ya ce" To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba"
Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haÉ—a mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuÉ—i, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuÉ—in makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa.

"A'a ki bari sai zuwa lokacin ai da sauran lokaci."
Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda na san wataƙila zuwa lokacin ya zo babu, mun yi mgana ya cire wasu kuɗi saboda Gidan bulo da office sai na yi masa mganar Halima ta haihu ba a yi mata komai ba sai ya ce zai turamin 20k ya ce a siyi abin da ya kamata ina so na ce ya rage min ko kaɗan a cikin kuɗina amman ban yi ba kamar ya san me na ke tunani sai ya ce

"Zan ba ki 50k ki rike a hannunki. KuÉ—in ki kuma in gwammati ta biya mu sai na baki duka in sha Allahu."

Ina yar shagwaɓa na ce" Yallaɓai buɗe saloon ɗin fa?
Da sauri ya ce" Wannan ni na ce zan buɗe miki, kuɗin ki kuma haƙƙn ki ne zan biya ki in sha Allahu."
Sai ya ga na yi shuru sai ya shafa kumatuna kafin ya ce" Kar ki damu. In sha Allahu duk za a yi."

Sai na gyaɗa masa kaina. Mun cigaba da lissafi ya ce 30k na kayan maggi da kayan tea, sai na ce ai ya haɗa gabaɗaya cikin na kayan abinci tunda tare muke siya a kasuwa a wani babban shago yana da lambar wayarsa list ɗin kawai zan rubuta ya tura masa da ƙudin har gida za a kawo mana kayan abinci.
Har da sabule da omo, ni kuma sai ya ce zai ƙara mini 30k saboda siyayyarmu ni da yara su Unders da sauran kayan kwalliyan mata.
Kuɗin asibiti kuma ya ce zai ware mini 50k saboda bamu san nawa za a nema ba sai dai goben in mun je mun gani. Sauran kuma ya ce zai yi amfani zai sallami sauran ma'aikata da shi ko da rabi rabi ne, ni na san har da kyatttuka sai ya yi in dai Yallaɓai ya samu kudi kamar suna masa kwaiƙwayi ni na yi masa mganar Nene, daman in za mu yi siyayya kayan abinci har da ita da kayan tea sai sabulan wanka sai ya ce na rubuta list ɗin gabaɗaya sai ya tura babban shago za a kawo kayan zuwa gobe in sha Allahu.

Sai na ce to a daran na rubuta abin da na manta na ce zuwa da safe zan tuna. Saboda zuwana asibiti tun asuba na tashi na yi ma yara shirin makaranta Yallaɓai jiya ya siyo indomie da kwai , sai buredi sai na soya musu buredin da tea ɗin suka tafi da shi makaranta, ni kuma muka shirya daman tun safe na tura ma Dr Fatima saƙo sai ta dawo min da amsar za ta ƙara kiran Dr Aisha ɗin amman na je asibitin na siya kati za a kai ni gynea unit ɗin in ce dai Dr. Aisha na zo gani a shigar mata da Fayel ɗina za ta duba ni in sha Allahu.

Tare muka fita da su Jidda muka kai su makaranta daga nan muka wuce Aminu kano. Da taimakon Yallaɓai nan da nan muka siya kati har aka yi mana hanya zuwa Gyea Unit da taimako  irin masu zirga zirga rarraba katina Yallaɓai ya yi ma ihsani, ya faɗa mai mun zo ganin wata Dr Aisha bukar ne. Wajen ta zai kai mini Fayel ɗina sai ya ce ba matsala ba ta ƙariso ba amman tana hanya.

Sai wajen tara da wani abu likitocin suka fara zuwa. Muna zaune da Yallaɓai bangaren yan jira aka shigar da Fayel ɗin mu, Saboda ihsanin da Yallaɓai ya yi mishi sai ya shiga ciki ya yi ma Dr Aishan bayani sai ta ce eh ta na sane fayel ɗina daman a sama ya saka min ni ce ta farkon da aka fara kira na shiga ganin Dr Aisha Bukar kamar yadda ke rubuce jikin Office ɗinta.

*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

Eaman ScholarSphere.
Where ideas Take Shape.

WHAT WE DO.
ASSIGNMENT
PRESENTATIONS.
ARTICLES
PROJECTS.
BOOK

AND MANY MORE.

CANTACT US THROUGH.
02347067793152

MOTTO:
"Pathways of Knowlodge Academy, Nurturing minds, illuminating Futures"

*🅿️15*

Aminu kano Teaching Hospital.
Gynecologist Unit.

Ina zaune a kan kujeran da ke fuskarta wajen zaman likita. Idanuwana kir a kan Dr Aisha Bukar ina ƙare mata kallo. Ta fi Dr Fatima shekaru ita babbar mace ce gaskiya a kallah in ba ta haura 40 ba za ta tsaya a hakan ta na da kaurin jiki, ga tsawo ga kiba sannan ba ta da wani haske sosai.

Tana zaune tana duba fayel ɗin gabanta gefe ɗaya kuma hankalinta na kan system ɗin dake gabanta da alama dai akwai abin da ta ke dubawa a ciki. Fuskarta da gilashi siriri sannan sanye take da rigan likitoci kanta kuma ta sanya ƙaramin breziya Hijab fari.

"Sadiya Sulaiman Yashe"

"Maa."

Ba ta kalle ni ba hankalinta na kan system É—in gabanta ta ce" Ke ce wacce Dr Fatima ta yi transfer É—in ki daga ABU KO?

Sai na gyaɗa mata kai lokaci ɗaya da cewa" Yes"  Saboda da turanci ta yi maganar.

Tsayin mintina goma sannan ta ce" Ga Report ɗin ki da ta tura mini  ina kan dubawa."

Da hausa ta yi mganar wannan karon kafin ta dawo da hankalinta kaina.

"Sunana Dr Aisha Bukar. Zan cigaba da jagorantar matsalarki har zuwa lokacin da za ki samu waraka in sha Allahu."

Ba ta jira jin ta bakina ba kawai ta cigaba ta faÉ—in.

" A yadda na ga É—an brief na matslar ki, kafin mu je kan matakan da muke É—auka ga masu irin laluran ki, kin san abin da ke damun ki? Ko dalilin da ya sa ba ki sake haihuwa ba?

Na ɗaga mata kai zan yi mgana kawai cikin zaƙin muryanta ta ce.

"SECONDARY INFERTILITY"
 
Kai tsaye kuma ta cigaba da bayanin ta.
Chapter 53 · 0% Book details