Sashe 2
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙayataccen mirmishi ya saki kafin ya riƙe hannun ta na dama da ta riƙe shi dashi, ya kai bakinsa ya sumbata lokaci ɗaya yana faɗin" Na'am Sadiya ta."
Sai kuma ya ga ta koma barci sai ya sauke mata hannunta ya ƙara gyara mata bargo sannan ya bar bangarenta.
Ya koma ɗaya bangaren ya zauna lokaci ɗaya ya cire hula kansa ya ijiye nan saman Side drower ɗin gadon, daman casbahan hannunsa na cikin aljihun bakin wando ke jikinsa a ciki ya saka, miƙewa ya yi ya cire jallabiyan ya rage daga shi sai dogon baƙin wandon dake jikinsa. Babban wardrope ɗin dake ɗakin mai kofa shidda ya buɗe ya saka jallabiyan sannan ya saka hannu a aljihun wandon dake jikinsa ya cire casbahan ya juya ya ijiye saman makeken madubin dake bedroom wanda ke shaƙe da kayan kwalliya. Laptop ɗinsa dake cikin drower ɗin gefen gadon ya buɗe ya ɗauka akwai aikin da yake so ya kamallah kafin ya fita office.
Kan gadon ya koma ya zauna ya jingina da jikin gadon. Sannan lokaci ɗaya ya mikar da kafarsa ya dora yar ƙaramar laptop ɗinsa ya fara aiki, lokaci bayan lokaci yana kai kallonsa kan Sadiya da ta cigaba da barcinta cikin salama. Sannan kuma wani lokacin sai ya ɗaga kansa ya na zagayen ɗakin da idanuwansa.
 Babban ɗaki ne domin bayan gado da wardrope akwai shuraf ɗin takalma mai hawa bakwai ne kuma dogo ne shaƙe da takalma na Sadiya da na Yusuf sai gefen kuma karfen sagala jakunkuna ne, ga su nan kala kala sama da goma, shi kalan ɗakin mai ruwan baƙi da fari ne ya yi kyau kwarai domin hatta zanin gadon fari ne da blanket ɗin su sannan haka labulan dake jikin window ɗin bedroom ɗin baki ne da fari.
Yana cikin aiki ya shagala kawai sai ji ganin kafar Sadiya ya yi a kan hannunsa dake saman laptop ta mako masa da karfi. Sai da ya yarfe hannu ya koma yana kallonta, kai ya ƙara girgizawa sannan ya ɗauki kafarta ya maida mata kan gado ya na ƙokarin cigaba da aikinsa ta ƙara yarfa masa hannu ya rankwafa yana gyara mata hannunta guda ɗaya,ta ƙara saka ɗayan hannun ta zargo wuyansa wanda sai da ya yi sauri cewa"Sadiya.."
Kamar ta ji sa sai ta sake shi, shi kuma sai ya koma yana kallonta bai san lokacin da ya kara sakin kayattacen mirmishi wanda Sadiya ce kaÉ—ai in ya kallah ya ke iya yi ma wannan mirmishin.
Fuskarta yake kallo yana jin wani farinciki daga ƙasan ransa, yar duma duman fuskarta mai ɗauke da kalan chaculate domin ba fara ba ce wankan tarwaɗa ne, mai ɗauke da doguwar fuska hancin ta ɗan madaidai ci ne da bakinta ƙarami mai ɗan tudu, ta haura talatin amman har gobe kamar yarinya yar shekara goma sha yake kallonta a kuma haka take a idanuwansa har gobe har kuma gaban abada.
Hancinta ya lakuce lokaci É—aya yana faÉ—in" Yar tekwando kawai."
Leɓenta ya kalla har yanzu akwai danshin jan bakin da ta yi masa kwalliya jiya, hannunsa guda ɗaya ya saka ya shafi leɓenta nata lokaci ɗaya yana mirmishi da ya tuna ranar daran amarcin su ranar da shi da Sadiya suka zama Miji da mata.
Tun ta na jin ɗari ɗari ta dunkule waje ɗaya, bai raina kansa ba sai da barci ya kwashi Sadiya ranar duk jikinsa a gajiye ya tashi, Kafafunta da hannayenta ta rika yarfa masa kwana ya yi yana gyara mata kwanciya, tun daga lokacin yake zolayanta da yar Tekwandon dare, Sadiya tana da nauyin barci da mugun barci ta yi ta buge wanda suke kwana tare, in kuma ya yi magana da safe ta musa har sai ya samu wata rana ya yi mata video ta gani sannan ta gasgasta. Tun tsawon shekaru goma sha da auransu har gobe Sadiyarsa da ya aura yar ashirin ta na nan ba ta sauya ba, ba ya kuma tunanin ko tsufa ta yi akwai wasu hallayar ta da ba za su taɓa sauya wa ba.
Vibration ɗin waya dake saman can side drower bangaren Sadiya ya katse masa tunaninsa. Wani gur gur sautin ke ba da wa ya ɗauka ma nashi ne sai da ya waiwaya sai ya ga ba tashi ba ce, sannan ya fahimci wayar Sadiya ce. Laptop ɗin dake saman jikinsa ya sauke nan saman side drower ɗin bangarensa. Sannan ya sauka daga kan gadon ya taka zuwa wajen wayar ya duba sai ga ALHAJINMU ke kira, ya na shirin ɗauka sai wayar ta katse, ya san password ɗin wayarta saboda date ɗin auran sune, ya buɗe yana shirin bin bayan kiran Alhaji ganin ko bakwai ba ta yi ba yana tunanin kamar ba lafiya sai ga wani kiran Alhaji ya ƙara shigowa sai ya ɗaga kiran da sauri lokaci ɗaya ya na faɗin.
"Alhaji barka da Safiya.."
Da yake wayar tana da ƙara ana jin sautin mgana ta cikin wayar.
"A.ah Yusufa ne?. Mun tashi lafiya ya kwanan iyalan naka?
Kamar yana ganin shi Yusuf ya rankwafa yana amsa masa da lafiya kalau.
Shima ya tambaye shi ya su Gwaggo ya ce duk suna lafiya.
Alhaji Sulaiman Yashe dagacan bangaren ya ce" ina ita DUBUN take?
Ko ta na can wajen yaran ne?
Kai tsaye Yusuf yace"A'ah ba ta tashi ba ne Alhaji amman in ta tashi zan sanar mata da ta kira ka."
Alhaji cikin gamsuwa ya ce'"To to ba laifi daman ba wani abu ba ne. Kai ma daman ina son ganinka, in ka samu dama yau bayan sallah isha'i ina son ka zo gida kai da Dubu."
Cikin ladabi Yusuf ya ce"To Alhaji in sha Allahu muna nan tafe"
Da haka suka yi sallama, ya maida wayar mazauninta ya juya sai ya ciro karo da idanuwan Sadiya kaifaffu a kansa, mamakin yaushe na farka ya bayyana a saman fuskarsa cikin sanyin murya ya ce"Oh daman idanuwanki biyu kike ta buguna da sunan barci ko?
Mirmishi na saki kafin na miƙe zaune lokaci ɗaya ina yaye bargon jikina.
Hannu guda ɗaya na miƙa masa sai ya kama na jawo sa ya zauna a gefena ni kuma sai na yada kaina saman kafaɗansa lokaci ɗaya ina faɗin" Allah yanzu na tashi, mganarka naji sama sama a saman kaina."
A tare na kuma kallonsa kafin na ce"Waye ya kira hala?
Yana wasa da yatsun hannuna na dama da suka shan jan lalle, ya na faÉ—in" Alhaji ne."
Cikin zaro ido na ce"Alhajinmu? Bayan na tada kaina daga saman kafaÉ—ansa.
Dariya ya yi kafin ya miƙe lokaci ɗaya ya miƙa mini hannunsa na kama ya miƙar dani tsaye ina miƙewa ya buɗe min hannuwansa na faɗa jikinsa ina sauken numfashin salama. Murya ƙasa ƙasa yace" Muna da wani Alhaji ne bayan Alhajinmu? Shi ne ya kira ya ce yana son ganin mu ni da ke. Yau da daddare"
Ina lafe a jikinsa ban wani jin mamakin jin haka ba, daman nasan za a rina ai ni daman uwar laifi ce yanzu har an samu wata ta je ta gaya ma Alhaji faɗan da ya faru tsakanina da Ma'u a gidan Rahila. Ban da Allan misuri amman ina da tabbacin dalilin kiran Alhaji kenan, ƙaramin tsaki na saki abin na cin rai na har yaushe ne yan gidammu za su gane Ma'u makira ce ita da uwarta? Tun muna yara ita ke nasara a kaina saboda macijin sari ka noƙe ce ni kuma ina da baki shi ya sa take ta samun nasara a kaina har kuma yau din nan komai ya faru tsakanimu ni ce mara gaskiya fitinanniya.
Ƙara sakin tsakin na yi wannan karon mai karfin har sai da ya ji, sai ya rankwafa da kansa dai dai kunnena yana faɗin" Me ya faru matata?
Sai na ƙara shigewa jikinsa kamar wani zai ƙwace min shi kafin na ce"Ina kwana Yallaɓan Sadiya"
Duk da ba na kallon shi amman na ji sautin mirmishin kafin yace"Ina kwana Sadiyan yallaɓai."
Atare muka saka dariya, sannan ya ɗago ni, ya sumbaci goshina ni kuma na sumbaci kumatunsa sannan na kalleshi cikin ido ina faɗin" ina sonka Yallaɓai na."
Mirmiahi ya yi min sannan ya sumbaci lebunana ya É—ago ya na kallona na wani lokaci kafin ya ce" Nima ina kaunarki Sadiya ta."
Komawa na yi na sake lafewa a saman kirjinsa ina faÉ—in"I miss u"
Cikin ƴar shagwaɓa da har sai da ya yi mirmishi ya rumgumeni yana faɗin"Ba ga ni ba, ni naki ne har abada Sadiya ta."
Ina jinsa ban yi mgana ba tsawon lokaci muna rumgume da juna, muna jin buguwar numfashin juna.
Da sauri na É—ago kaina ina kallonshi shima kallona ya ke yi.
"Yau wata rana Yallaɓai.?
Gira ya É—aga kafin ya ce" Monday mana."
Da sauri na waro ido kafin nace"Monday fa ka ce?
Ya na yar dariya ya ce"E, mi ye to?
Gabansa na bari ina gyara zaman kaina na ce" Yallaɓai yau fa monday ka manta su Jidda na da makaranta."
Riƙo ni ya yi na dawo gabanshi lokaci ɗaya yana faɗin" Ba matsala na faɗa ma Jidda su yi wanka su shirya."
Wuya na karya a shagwaɓe kafin na ce"Breakfast fa Yallaɓai?
Yana shirin mgana muka ji ana knooking shi ne ma ya ce a shigo, ko ban tambaya daga ni har shi mu san su waye. Buɗe ƙofar suka yi suka shigo a tare cikin shirinsu na kayan makaranta, Jidda riga da wando ne a jikinta da ƙaramin farin hijabi, sai Baby sanye da doguwar riga zuwa gwiwa daga kaɗan amman ta saka wando baƙi dogo. Itama da ƙaramin farin hijabi ita uniform ɗinta maroon ne da fari.
Da sauri na buÉ—e hannuwana ina faÉ—in"My Babys"
Da sauri Baby ta nufo ni na duƙa ta faɗa jikina tana faɗin"Good morning Umma"
Ina shafa kanta na ce"Morning my princess"
Sannan ta É—ago ta sumbaci kuncina nima sai na sumbaceta, Yusuf ta nufa tana faÉ—in"Good mornig Abba."
Gefe ya yi ya na make kafaɗa kafin ya ce"Naƙi sai da aka gama rumgumar Umma sannan a ka tuna da Abba."
Kafafunsa ta rumgume ta na faÉ—in"Abba"
Lokaci ɗaya ta na dariya ni kuma sai na miƙe ina faɗin"Yallaɓai kishi kake yi da Umma yau?