← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 76

Sashe 68

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ƙarfe biyu na koma gida na.  Daga kuma ranar ko a fuska ban ƙara nuna ma Yallaɓai wani abu ba. Ban damu da ma ƙara saka masa ido ba saboda mu zauna lafiya amma ni na san ba ta fasa kiran shi da tura masa saƙo ba, amma dai bai ƙara buɗe baki a waje ba sai a gida mun shiga goman karshe an fara ibadar na tahujjud Yallaɓai masallaci ya ke zuwa ni kuma in ta da yara mu yi namu a gidaa.

  Ranar da za mu ɗau azumi na ashirin da 24 Yallaɓai ya dawo daga masallaci ya ɗan kwanta huɗu da rabi na tashe shi sai ya shiga tiolet yana wanke baki a lokacin na ga Gimbiya ta na kiran shi bayan ta katse sai ta tura mssa saƙo zuciya ta rinjaye ne na ɗau wayar na duba saƙon na ta.

"Daddy jiya ba ka zo ba? Kuma fa na yi maka kunin tsamiya mai daÉ—i"

Motsin fitowarsa na ji da na so na yi saurn ijiye masa wayar ne sai kuma na fasa sai da ya fito. Ya yi mamakin ganina tsaye da wayarsa sai da ya matso gabana sannan na miƙa masa wayarsa ya karɓa kafin ya samu sararin mgana na ce.

"An tura maka saƙo."

  Ina gama faɗin haka na fice na san kuma bayan ya duba saƙon ya ji nauyi domin ba na ce kunya ba tunda maza ba su san kunya ba. Har ya fito muka yi sahur jikinsa a sanyaye ni kuma sai na yi masa bariki ban nuna masa ko a fuska na ji haushi ba sai ya ɗan saki jikinshi amma a raina na kudiri niyyar koya masa hankali daga shi har Gimbiyar ta shi.
Washegari ya tura mini kuɗin kayan salla nawa da na yara sai na su Nene da na Gwaggo. Daman yana yi musu kaya duk shekara. Dija collaction na tura ma kuɗin daman mun yi mgana na zaɓi komai har Marwa na yi ma kaya da Saude saboda mun yi waya a gida za ta yi salla in ta dawo sai kuma ta gama pratical ɗin ta za ta koma makaranta. Kuma daman ta turo mini kayan na zaɓa tuni suna wajen ɗinki kuɗin ne sai da ya tura mini bayan mun gama lissafi na tura mata.

  Ni da yara kala huɗu ya yi mana. Leshi biyu atamfa biyu. Nene Atamfofi biyu su Hajiya Iya kowacce ɗaya sai Jawahir kala biyu Adanan kuɗi ya tura masa sai Gwaggo guda ɗaya Alhajinmu kuma shadda mai kyau. Sai ni mayafai guda biyu da Hijabi ni da yara sai takalman mu har Nene an siya mata takalmi da Hijabi gabaɗaya tun lokacin da a ka kawo kayan na nuna masa ya ce komai ya yi. Telanmu kuma daman na yi masa mgana kuma ga kuɗi har da na Nene na kai mana ɗinki tare da na Jawahir da Marwa Saude kuma na ta na bata mamanta na ɗinki ita za ta ɗinka mata. Gwaggo kuma da Alhajinmu na kai musu na su suna ta godiya duk da suma su Yaya Hamza duk sun yi musu. Nene ma na kai mata takalmi da hijabinta na ce kaya na wajen ɗinki ta na ta saka albarka.
Ranar da muka ɗau azumi na ashirin da shidda Mimisco ta aiko da kaya yan kanti kala biyu biyu na jidda da baby. Anty Bahijja ma ta aiko musu da material a ɗinke sai Anty Maimuna itama kala biyu amma Bby uku ta yi mata har da wani riga da wando masu kyau da takalma. Gimbiya kuma Yallaɓai ta ba ma kayan ya kawo ma su, kayan kwalliya ne sai hijabai da mayafai sai takalma masu igiya sai abun hannu da ɗan kunne sai kwalban da ake kitso da shi kayan kuma ta ce suna wajen ɗinki duk Yallaɓai ne ya ke koramin jawabi nan yaran suna ta murna shima bakin shi ya ƙi rufuwa. Daga gani ya ji daɗi kuma har hakan ya nuna a saman  fuskar shi.
  Ni dai ban nuna masa komai ba na yi godiya har ya na saka min kati a waya ta ni kuma na san na kiran da na ce zan yi ma Gimbiya na yi mata godiya ne. Kai namiji munafuki ne wallahi.

  Ranar da muka ɗau azumin ashirin da bakwai ɗaure Yallaɓai ya yi saboda na zo tashin shi na ga Gimbiya na kiran shi sai kawai raina ya ɓaci ban tashe shi ba. Ni kaɗai na yi sahur saboda Jidda na ce ta huta jiya ta sha wahala. Yallaɓai bai tashi ba sai da aka fara kiran salla lokacin ina zaune na idar da raka'atul fajir, ya tashi ya na kalle kalle kiran sallar da ya jiyo ne ya sa ya kalleni cikin muryan barci ya na faɗin

"Sadiya mun makara ne? Na ji kamar ana kiran salla?

Sai da na kalle shi kafin na ce" Kai dai ka makara. Ni na yi sahur É—ina."

Cikin mamaki da tuni barcin ya sake shi ya ce" Ban ga ne ba? Ni fa?

Kai tsaye na amsa masa da cewa" Ba ka yi ba."

"Me ya sa ba ki tashe ni ba?

Sai da na yi shuru kafin na ce" Ban tashe ka ba. Saboda na ga wacce ka rabama girki da ita na kiranki sai na koma a tunanina ta tashe ka yau É—in"

Galala ya yi ya na kallona sunana ya kira na yi masa banza sai kawai na miƙe na kabbarta salla ganin haka yasa shima ya mike amma sai ya ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya mike ya fita zuwa tiolet ya ɗauro alwala ya fita zuwa masallaci sanda ya dawo ina ji da na yi baricn ƙarya weekend ne yara ba makaranta sun ma yi hutu jiya jumma'a.

  Na san mganar da na faɗa masa na cin ransa bai iya hakuri ba ina barci ya tashe ni da mganar wai bai gane me na ke nufi da ya raba mana girki ba? Da wa ya raba mana girki?

Kai tsaye na ce" Da wacce ta ke yi maka girki kana zuwa ka ci ka biya tuƙwaici mana."

  Wani kallo ya yi mini ni kuma ina shirin na juya na koma barci ya riƙo ni ya na kiran sunana.

"Sadiya."

Ido na sakar masa kafin na ce" Na'am Yusuf."
Kawai sai ya girgiza kai bayan ya saki hannuna kafin ya ce" Sadiya karki fara abin da ba halin ki ba ne. Bincike mini waya kike yi yanzu saboda ba ki yarda da ni ba?
Kai tsaye na ce" Allah shi kyauta. Kawai dai akasi aka samu na gani."
Komawa na yi na kwanta ina faÉ—in" Karka damu ba wani abu fa."

Miƙewa ya yi ya na kallona ni kuma sai na ja bargo har saman kaina. Hannu ya saka ya janye bargo ya na faɗin" Ki tashi mu yi mgana"
Sai na ƙi tashi na riƙe bargon ina faɗin" Wata mgana? Ai mun gama mganar nan ko?
Zura min ido ya yi kafin ya ce" E duk da haka na ce ki tashi mu yi mgana."

Na ko ƙi tashi na juya zan gyara kwanciya a saman kaina Yallaɓai ya yi min tsawa.

"Sadiya na ce ki tashi mu yi mgana ko? Kar ki bari raina ya ɓaci wallahi."

Yadda ya yi mganar ne ya sa na gane ranshi ya ɓaci sai na miƙe na zauna a saman gado shima sai ya zauna ya na mai sauke ajiyar zuciya.

"Sadiya wallahi ba komai tsakanina da Daughter fa. Kawai dai kin san am her favorite ne tun a baya. Kuma ni tana kira ne ba domin ta san ba ni da mata ko wani abu ba just normal na yan'uwan juna kin gane?

Sai kawai na gyaÉ—a masa kai, domin ni na san kawai yana faÉ—a ne.

"Kar ki ɗauke shi a wani abu don Allah. Ni ina mijinki haƙƙi ne a kanki ki tashe ni kamar yadda kika saba."

"To ba za a ƙara ba."

Na faÉ—a saboda na gaji da jin mgananunsa.

"Kuma game da abinci in na je duba Nene sai ta yi mini ta yi in na ce ba zan ci ba sai Nene ta ce ko kaɗan ne na taɓa. Kin san dai ba zan yi ma Nene gaddama ba. Mganar tuƙwaici kuma wannan kyautatawa ce kema kuma ai ina yi miki ko?

Ina ta kallon shi dai amman na kasa mgana.

"Ba ki son kiran ne?
Sai na ce mata ta daina Sadiya ta ba ta so."

Wani kallo na yi masa kamar in yi dariya saboda na ga zai raina min wayau amma ban yi ba.

"Zan faÉ—a mata ta daina kirana da asuba gashi yau ta ja mini yin É—aure."

Ya faɗa ya na yar dariya har yana shafa min kumatu. Yaƙe kawai na yi masa ban yi mgana ba. Hamma ƙarya na fara yi masa sai ya ce na koma na kwanta shi zai fita can falo akwai aikin da zai yi har ya ɗau laptop ɗin sa ya fice ina bin shi da kallon mamaki. Ajiyar zuciya na sauke ko ba komai a zuciyar Yallaɓai game da Gimbiya ita har gobe shi ne zaɓin ta tsoro  na ɗaya wannan karon mafarkinta zai iya zama gaskiya in dai ba wani ikon Allah ba tunda ba ta da shamaƙi da hakan ta kowanni fanni.
Tun kuma daga mganar da muka yi ba mu ƙara tada mganar ba. Ita ma ta daina kiran asuba ina tunanin da gasken ya yi mata mgana sai na ji daɗi ko ba komai  ya nuna mata ni matarsa ina da daraja. daga nan nima sai na watsar da abin da ke cikin zuciyata na kishi na rumgumi mijina.
Chapter 68 · 0% Book details