← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 76

Sashe 5

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Dariya ta yi har ina jin sautin ta kafin ta ce" To Anty."
Ni kuma Bedroom ɗina na koma kan Dressing ɗin mirrow ɗin da ke ɗakin na ijiye wayata na koma na kwanta har da shigewa bargo. Har ga Allah na ji ana ta kiran wayata amman ban mai da hankalina ba, na ɗauka yan gidanmu ne kan maganar ƴar gwal Ma'u shi ya sa ban ko motsa daga cikin bargon da na ke kwance ba afili ma sai da na yi ƙwafa kafin na ce"Ku ci kan ku." Na ƙara shigar da kaina cikin bargo ina ƙara gyara kwanciyata.

  Barci ya fara ɗauka ta domin har na fara wani mafarki mai ɗan karan daɗi, kamar daga sama na ji muryan Saude ta na kirana.
"Anty. Anty.."

A firgice na tashi saboda a saman kaina a can cikin barci na ji kiran sunan.

  Saude na gani a cikin Bedroom ɗina daga can baƙin kofa, tana ganin na tashi zaune da sauri ta ce"Anty kin yi baƙuwa."
Yamutsa fuska na yi kafin na maimaita kalmar" Baƙuwa?
Sai ta gyaÉ—a min kai kafin ta ce"E. ta ce na faÉ—a miki Bahijja ce."
Shuru na yi ina tunanin wace ce kuma Bahijja, ido na É—an waro kafin na yi saurin yaye bargon jikina na sauko daga kan gadon lokaci É—aya ina faÉ—in" Tana can falo ne?
Saude ta gyaÉ—a kanta kafin Ta ce" E. tana can falon farko."
Kai na gyaÉ—a kafin na ce" Je ki ce mata gani nan zuwa Saude." Ta amsa min cikin ladabi sannan ta buÉ—e kofa ta fita ta barni ina sauke numfashi.

  A gaban madubi na tsaya ina kallon fuskarta sai da na tabbatar da ba ni da wani abu da za ta kalla ta yi ƙorafi sannan na gayyato mirmishi da fara'a a saman fuskata sannan na zura takalmina mai taushi na zirga zirgan cikin gida, na zo zan gota ta jikin madubin sai da na ƙara tsayawa na kurama kaina ido ta cikin madubin ina jin gabbaina suna yin wani irin sanyi ƙalau, yanayin jikina na bi da kallo tabbas ina da son gayu da gyara ni macece da kana ganina kafin ma a faɗa maka wani abu akaina za ka sha shaida ina da son gyara, tun da ga kan gyaran fata na gashi da gyaran ƙasa na mace duka ba na wasa dasu bangaren gyaran fata kayan AISHA LAME +234 703 666 2633 na ke amfani da su, in kuma bangaren kayan ƙawa na gayu ne tun da ga kan atamfofi da abayoyi da takalma a wajen DIJA COLLECTION na kan yi siyayyata da ga ni har su Jidda shi ya sa kayana tare da na ƴaƴana muka fita dabam a cikin Dangi.

  Numfashi na ja sannan na ƙara fesarwa, wayata na ɗauka sannan na fice daga ɗakin ba ta kitchen na bi ba sai ta bi ta korido tunda falon farko zan je, ina tafe ne ina latsa wayata na ji na tsorata lokacin da na ga cikin waɗanda suka kirani har da Anty Bahijja, lalle yau Allah ne kaɗai ya isa ya cece ni daga ƙorafi da ƙananun mganganu sai wanda kunnena suka iya ji,  ina tura ƙofar falon lokaci ɗaya tare da sallamata da kuma tahowa da fara'a a saman fuskata.
+234 903 661 7473

  Ta na hakimce kan kujera mai zaman mutum ɗaya, sanye da dogon hijabi mai ruwan kuka har da liƙabinta, kenan daga makaranta take, ta biyo ta nan ina nufarta ina washe baki lokaci ɗaya ina faɗin"Maraba da Anty Bahijja."
Sai a lokacin ta É—ago kanta daga duba wayarta da take yi, sai da na kariso gabanta na zauna saman kujera mai zaman mutum ukun da take gefenta ina faÉ—in" Ina kwana Anty Bahijja."
Sai a lokacin ta iya ɗaga likaɓin ta sama fuskarta ta bayyana.
Cikin yanayin maganarta ta kalleni daga sama har ƙasa ni kuma ina ta faman yi mata mirmishi.

"Barka dai ta tashi gimbiya ko na ce Sadiya yar laushi ba"

  Wani abu mai ɗaci ya taho daga cikina ya tokare a saman ƙirjina. Shi ya sa har abada ba zan taɓa ƙaunar Ma'u ba, kuma ni da ita ba za mu taɓa zama a inuwa ɗaya ba. Amman ban nuna mata ba sai ma na ɓige da yin wani kayattacen mirmishi kafin na ce"Kai Anty Bahijja, ki yi haƙuri kin kirani ban ji ba. Na ɗan kwanta ne."
Baki ta taɓe kafin ta ce"Ai fa aikin kenan barci, kina ciki kin kwanta yar aiki na yi miki aikace aikace"
Kai tsaye nima na ce" Saude ai tana zuwa tana taimaka mini ne, kinsan aikin gida da yawa Anty Bahijja."

"Ina wani yawa a aikin gidan nan Sadiya? Kawai daman kin saba da hutu shi ya sa kike kallon shi a matsayin aiki."

  Ni ko sai na yi mata mirmishi duk da maganar ta na sukan zuciyata amman sai na ɓoye hakan a saman fuskata. Kai na kaɗa kafin na ce"Hutun ne ya zo Anty Bahijja  amman karki manta a baya nima na yi aikin."
Ta san magana na gaya mata shi ya sa ta yi mini wani kallo, ban bari ta samu damar magana ba na cigaba da faÉ—in" Kuma Anty Bahijja laifi ne in mace ta samu hutu ta huta a gidan mijinta? Kema fa kina da yar aikin nan sannan ki na fatan nan gaba in su Sulaihat suka yi aure suma su samu gidan da za su huta ko ba haka ba ne? Ba fa wanda ba ya son jin daÉ—in nan fa."

  Na faɗa ina kallonta saboda na ga kuma wata magana za ta ƙara faɗa mini, sai na ga ta juyar da kai ta na faɗin"Ba irin na ki ba Sadiya."
Ban yi magana na nima sai na kauda kaina ina É—an mirmishi, na rasa wani hutu suke hangomin a cikin wannan gidan? Sun manta a baya komai na gidana da mijina da Æ´aÆ´ana ni nake yi ma kaina? Saude ba ta fara zuwa mini aiki ba sai bayan mun tare a wannan sabon gidan amman gabaÉ—aya Æ´an'uwan Yusuf gani suke yi da kuÉ—in É—an'uwansu na ke walwali ina haskawa sannan na samu duniya ina ta jin daÉ—ina.

  Ban ƙara ce mata ƙala ba, amman ita sai faman kalle kallen falon take yi tana wani taɓe baƙi, ba yarinya ba ce tunda Yayar Yallaɓai ce, daga ita sai shi tana da manyan ƴaƴa amman ba taba aurarwa ba suna karatu ne.
Can ta ga ji da zaman mulkinta ta kalleni ta na faÉ—in" Su Jidda suna makaranta ko?
Sai na gyaÉ—a mata kai, kafin na yi magana ta rigani da cewa" Kuma sai satin nan ba ki kai su gidan Yaya Maimuna ba? Me ya sa ?

  Daman na san rashin zuwan su gidan Anty Maimuna sai ya zame min abin magana, zama na gyara kafin na  fara faɗin" Ba su samu zuwa ba. Amman weekend ɗin nan in sha Allahu za su je."
  Anty Bahijja ta ƙara faɗin" Me ya sa na ke tambaya?
Kai tsaye na ce"Gidanmu muka yini ranar asabar, lahadi kuma na ce su tsaya saboda shiryen shiryem makaranta, su goge uniform da homework lokaci ya ƙure shi ya sa sai na ce bari su bari wannan satin da sun dawo makaranta ranar jumma'a zan tsa yar mai mashin ɗin su, sai ya kai su in sha Allahu."

  Miƙewa ta yi, lokaci ɗaya ta na rayata jakarta, kafin ta kalleni tana faɗin"Kina  da ƙulafucin ƴa'ƴan Sadiya. To ki yi zuciya ki sake haihuwa mana. Amman ace kamar gidan Yusuf shi da ke son yara a ce ƴaƴa biyu kaɗai gare shi kamar ba shi da wani zaɓi, yanzu in muka ce ya ƙara aure sai ki ji haushin mu ko?
Ƙuramin ido ta yi saboda tana so ta ga yadda zan yi, sai ni kuma na nuna mata har yanzu ba ta gama sanin wacece Sadiya ba.

  Dariya na saki har ta na fidda sauti kafin na ce" Jin haushi kuma Anty Bahijja? Ai aure umarnin Allah ne shi ya ba su damar ƙarawa, wallahi tallahi na sha faɗa ma Yallaɓai in zai ƙara aure ya ƙara domin ni ba ni da matsala da ƙarin auransa tun da ba akaina za ta zauna ba, kuma ko ta zo sai dai ta zo a ta biyu kin ga kenan ko ya ya dai na ke na amsa sunan Turken gida. Haihuwa kuma ta Allah ce, in ya tsara min ƴa'ya biyu zan haifa shike nan, kuma ni ba zan yi ma Yallaɓaina baƙin cikin ya ƙara aure ya sake haihuwa ba, duk wani abu da ya fito daga tsatson Yusuf abin so ne a wajena."

  Kamar ba ta yarda da magana ta ba, domin sai ta ƙara kallona take yi, tana mirmishi, kallonta na yi domin har ta mirmishinta irin na Yallaɓaina ne. Ganin ta kama hanyar barin falon ya sa na miƙe na bi bayanta dai dai lokacin da na ji ta na faɗin"Ke fa kika tsaida haihuwan da kanki Sadiya kin ga ko, ko auran Yusuf ya ƙara bai yi miki rashin adalci ba."
Ina bin bayanta na yi mirmishi amman ban yi magana ba.

  Ni ce har haraban gida na rakata, ina ce mata"Ba ki zo da mota ba ne Anty Bahijja?
Kai tsaye ta ce" Tana waje."
Sai na gyaɗa kaina fulawowin gidan ta bi da kallo kafin ta ce" Fulawowin nan sun ƙara ma gidan nan kyau fa."
Na biye mata ina cewa" Sosai ni ko ma da farko ban so Yallaɓai ya saka su ba sai bayan sun fara girma sai na ga sun yi ma wajen aiki."

  Wani kallo ta yi min ta cikin likabinta  da ta saki kafin ta ce"To gidan ki ne? Da sai kin zaɓi abin da zai saka ma gidan shi? Dariya na yi kafin na ce" Gidana ne mana Anty Bahijja, ko kwatance za a yi gidan Sadiya za a ce ko Maman su Jidda, kamar yadda kema a ke kwatancen gidan mijin ki da gidan Malama Bahijja."
Kallona ta yi ido cikin ido ni ko sai na waske ina dariya.
Chapter 5 · 0% Book details