Sashe 43
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar ta bangaren Yaya Abubakar da Yaya Hamza ne. Shi Yaya Abubakar ba shi da zafi shima dai akwai sakewa da mutane ga surutu saɓanin Yaya Hamza da bashi da wasa ƙwata ƙwata. kamar misalin Yaya Auwal ne shi kuma wannan ɗan i dont care ne. Abu goma za a yi a cikin gida bai ma san an yi ba shi fa rayuwarsa kawai yasani sai ko in ya ji yunwa ya ci abinci. Yaya Aina itama ba ruwanta ba ta da faɗa amman Yaya Murja ta fi kowa shegen shisshigi da shiga abin da ba ruwanta ga sa ido sannan ba ta da haƙuri kamar zawo ta ke. Shi ya sa ba mu taɓa shan inuwa ɗaya da ita ba ita faɗa ni kuma rashin kunya. In aka duba Amina da Datti. Gwara ma Datti ita Amina miskila ce irin Auwalu sha'ani ko an saka su aciki ma ɓata lokaci ne abu nawa zai faru a cikin gidan suna nan amman ba dai ka ji bakin su ba. Shi ya sa na ce a gidanmu kowa da irin halin da ubangiji ya yi masa dai dai gwargwado da zai zauna da mutane.
******
*2000*
*ÆŠorayi*
Hajiya Dubu ce ta ƙure Radiyo ɗin ta a tsakar gida tana sauraran gidan radiyon jihar kano ana karanto labaran yammaci. Zaune take saman tabarma daga can ƙofar ɗakinta. Gwaggo na gefen ta suna jin labaran jefi jefi Mama ma dake can gefe tana tankaɗen garin masara a cikin farantani. Tana ɗan saka musu baki jefi jefi.
Ina kwance a kan gadon Hajiya Dubu har wani ƙara nitsewa ne ke yi. Ba wanda ya san ina ciki saboda gadon mai rumfa ne. Kuma san da na shigo har Hajiya Dubun ba ta sani ba. Yau alhamis ba islamiya kuma ni ce ke da girki gabaɗaya na gaji. Da rana alkubus ɗin alkama na yi gabaɗaya a gajiye na ke daman kun sani yar laushi ba na son aiki kawai ina kwance bayan na idar da sallar la'asar ina hutawa Mama ta leƙo ta ce min na fito na ɗora miya a lokacin tura baki na yi kafin na ce.
"Mama Tuwo kuma?
"E."
Haka ta faɗa tana kallona idanuwana har ya ciko da ƙwallah. Gaskiya dai na gaji kuma a ƙasa ƙasa sai da na ce na gaji Mama ta yi tsaki ta na sakin labule kafin ta ce"Ke daman ai ko kina kwance ne sai kin ce kin gaji. Malama ki taso kar dare ya yi kin kuma san Alhaji ya hana ku tuwon dare."
Na fi mintina talatin kafin na taso sai da Mama ta Æ™ara leÆ™owa tama faÉ—in za ta make ni. Ni kaÉ—ai ne a É—akin Amina ta bi su Rahila yau wata yar islamiyan mu na aure ni daman ba na zuwa biki ban je ba ina gida amman daga baya na fara nadama da na sani na bisu sai na ga wanda zai tsaya har a ce ya yi tuwon dare. Shekaru wajen biyu kenan Alhajinmu ya ce aikin gidan da ya dawo kanmu ni da Rahila da Ma'u tun da alokacin mu ne Æ´an matan gidan muna cikin shekaru na sha tara ne kuma muna zangon karatu na Æ™arshe a matakin babban sakandiri a makarantar GGSS ƘAWAJI dake kwanar dakata a jihar kano.Â
 Yaya Balki ma ta yi aure shekaru wajen huɗu da suka gabata. Yanzu a gidan daga mu sai Datti da ke ajin ƙarshe a ƙaramar sakandiri sai Amina dake ƙokarin shiga matakin farko a babban sakandiri. Sai Yaya Muntari da ya dawo gidanmu da zama shekaru uku yana karatu anan FEC KANO. Sai Hajiya Dubu da Alhajinmu ya ɗauko ta bayan mun tare a sabon gidanmu dake Ɗorayi.
Domin Alhajinmu tuni likafa ta cigaba ya koma aiki da Hukumar KEDCO na jihar Kano.
Sai Yaya Abubakar da ke karatu a jami'ar Bayero yana karantar Vitnary ya na shekara ta uku ne. Sun ɗaɗe a gida shi da Yaya Hamza kafim su samu su ci jarabawar babbar sakandiri a lokacin samun jami'ar ba ta wahala cin jarabawar sakandiri ne mai wahala wajen sau uku suna sake rubutawa sannan suka ci. Shi sai ya zauna a gida nan kano shi kuma Yaya Hamza sai ya lula Sokoto Usman ɗanFodiyo University Udus. Acan ya ke karantar accounting shima yana shekara ta huɗu ne. Yaya Auwal kuma yana Nasara state University Keffi. A shekaran nan ya tafi shima.
Mun zama ƴan mata duk wani tantanin budurci ya gama bayyana mana. Alhajinmu yana da burin in mun gama sakandiri mu yi aure. Ban san dai tunanin sauran ba amman ni ba ni da burin aure yanzu sai na gama jami'a na samu aiki saboda a lokacin Alhajinmu ya samu ƙarin girma manaja ne a hukumar wutar lantarki ta jihar kaduna kuma ya samu daman ƙaro karatu tun a zamanin baya. Ni ma sai na ji ina sha'awar haka. Rahila dai na san cewa ba ta da ra'ayi mai zurfi kamar nawa, Ma'u kuma har gobe ba jituwa a tsakanimu shi ya sa ni ban san me take ciki ba. Amman shekarun sun tura da ya sa na ƙara aminta da zargina na cewa Tana son Yaya Hamza shi kuma ba ta gabansa duka ɗaya ya ke ɗaukan mu. Shi kuma Yaya Abubakar a yanayin yadda ya ke kafa kafa da Ma'u son ta yake yi ita kuma baya gabanta ni dai ina gefe ina kallon komai ina tunanin ta yadda Ma'u za ta ɓullo ma lamarin ƴan'uwa guda biyu. Amman na ci alwashin ba zan bari ta zo gidanmu ta raba mana kan yan'uwa ba na san halinta ba ta da kirki kanta kawai ta sani.
A yadda muka taso a haka muka girma. Ni da Rahila mune masu tsawon. Sai dai muna da bambamcin jiki ita Rahila ta fi ni kiɓa. Ma'u kuma muna da yanayin jiki bamu da kiɓa amman ita ba ta kai mu tsawo ba ta ɗauko tsawon mahaifiyarta ne Baaba dake can kura ta hayyaffa da wasu ƴaƴan bayan Ma'u. Amman kuma duk wanda ya ganmu ya san mu ɗin jini ɗaya ne. Ballatana ni ban cika yawo da Ma'u ba sai dai makaranta in ya zama dole a gida kuma ta shafa mini lafiya saboda ba na ƙyaleta. Sannan dawowar Hajiya Dubu gidanmu ya sa ba ma wanda ya isa ya taɓa ita da Yaya Abubakar sun sha artabu a kaina. Tun kuma da Hajiya ta dawo gidanmu na tattara kayana na koma ɗakin ta can na ke kwana sai in har na ga dama ne nake shiga ɗakin mu duk saboda kar na haɗu da Ma'u za mu kwana gida ɗaya mu tashi amman ba za mu yi ma juna mgana ba. In ko faɗa ya haɗa mu in na fara gaba da ita sai mu yi wata ba mu yi mgana ba sai in Rahila ta gaji ta kai ƙarar mu wajen Alhajinmu in ya yi mgana sai Ma'u ta ce in ta yi mini mgana ba na tanka ta. Sai a ɗora laifin a kaina amman thank god Hajiya na nan ita ce ke zama justice ɗina in dai akan Ma'u ne.
 Bangaren Yaya Murja ma ba ta sauya zani ba. Ko bayan auran ta in dai za ta zo gidan da abun arziƙin da za ta kawo ma Ma'u da Rahila har da Amina ni kuma sai ta ce ba ni da kunya. Ni ma da na gane ko gidan zan iya kirga zuwana, na fi zuwa gidan Yaya Aina ko Yaya Balki in ma fitan ya kamani kenan. Har a lokacin ba ni da wata kawa da zan iya nunawa amman Rahila da Ma'u suna da ƙawayen su. Barin ma Ma'u ƙawarta din nan Shema'u har lokacin suna tare su Gwaggo duk sun santa ta na zuwa nan gida itama Ma'un ta na zuwa gidan su saboda su haɗu da Ma'u su yi ta munafunci har can dakata tare suke a makaranta. Ni dai kamar yadda ban son Ma'u itama Shema'u ban ƙaunarta domin gabaɗaya halin su ɗaya. Za mu haɗu sau goma a makaranta sannu ba ta haɗamu da Shema'u amman in ta zo gida tana mini fara'a kamar ta Allah. Na daɗe da yarda da mganar hausawa da suka ce sai hali yazo ɗaya ake abota. To akwai mugayen hallayar Shema'u da Ma'u da suke kamamceceniya.
Â
****
 Mama ta shiga madafi ta ga na ɗora miya tana tafasa ko ƙashin miyan ma da Muntari ya shigo da shi ban saka ba sannan ban ko ɗora tuwo ba. Ba ta yi mamaki ba sanin halina sai ta fito tana faɗin" Sadiya me take son zama ne ni Rukayya?
Gwaggo na zaune ta ce"Me ya faru hala?
Sai ta kaɗa kai tana nufar ɗakin mu kafin ta ce" Ba ta ko ɗora tuwo ba. Kuma miya na ta dahuwa ko ƙashin da muntari ya shigo da shi ba ta saka ba."
Lokacin ta É—aga labulen É—akin tana kwala min kira ina daga É—akin Hajiya har na fara barci.
"Ba ta fa a É—akin"
Hajiya hankalinta na wajen jin radiyonta ba ta ma jin su. Gwaggo ce ta leƙo dakin Hajiya ta na kiran sunana na ji har gyara kwanciya na yi. Ban ankara ba sai ji na yi an ɗaka mini duka a cinyata da sauri na miƙe ina sosa wajen sai na ga Mama tsaye a kaina tana huci.
Cikin tura baki na ce"Kai Mama a cinya fa kika dake ni."
"In ba ki tashi ba sai na mare ki a fuska yanzu."
Ina jin haka na yi saurin saukowa daga gadon saboda na san halinta tana da saurin hannu. Ina fitowa na ga har mangriba ta yi Gwaggo ta kalleni ta na faÉ—in" Sadiya ho. Ke ko koyi da Æ´an'uwanki ba kya yi. Su in dai suna da aiki akan lokaci suke gamawa."