Sashe 18
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Sai ya ce na kwantar da hankalina bari ya kira shi, muna gama wayar a daddafe na tafi tiolet ɗin falo ma ba na ciki ba, kayana duk sun baci ina ma turarradin ban bata ma mai Napep kujera ba, kayan jikina sun lalace na tube na yi wanka kayan kuma na jika su a bucket, haka na fito ina hawaye, ina ta murna side effect ɗin planining ya daina taɓa ni, tunda duk a asibitocin da na riƙa zuwa a baya sun tabatar mini da komai lafiya zan iya samun ciki ko yaushe ne.
Mun kashe kudaÉ—e a asibitocin kuÉ—in dake garin kano ba a dace ba, shi ya sa na yi amfani da shawaran mutane na ga gwara na je babban asibiti.
A baya na yi ta fama da ciwon mara da zubar jini a can wani babban private hospital sun ɗorani kan wani mgani na yi amfani dashi kuma cikin ikon Allah komai ya daidaita. Ina cike da yaƙinin komai zai zama tarihi sai ga shi al'amarin ya dawo sabo.
 Zubar jini nake yi sosai sai da na saka Pampers daman ina da shi, saboda ina bleeding in ina period shi na ke amfani dashi.
 Ina zaune kawai ina hawaye, abin duniya ya isheni Yusuf ya sake kirana labarin da ya ke faɗa mini ya saka ina hawaye ina dariya.
Likitan da zan gani a Shika ta ba ni dama ranar monday sha É—aya na safe, in na je zan kira wayar Dr Fadil wanda Uncle Abba ya tura masa lambar.
 Ina mirmishi na share hawayena ina faɗin"Alhamdulillah."
Me na ke tunani. Ina tunanin kamar ina da wata matsalan anan ba a gano ba ne,tun da ba babba asibiti ba ne.
Ina hashashen in na sauya waje da asibiti mai kyau da ke da ƙwararru kila za a iya gano wani abun har na nemi magani domin na samu waraka.
"Ki kwantar da hankalinki, sai mu je tare in sha Allahu "
 Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce" Shi ke nan, Allah ya kaimu nan da kwana shidda kenan ko?
 Sai ya amsa mini ganin duk na damu sai ya shiga lallashina, da cewa in sha Allahu ba wata matsala. Cikin yaƙinin da na ke dashi na ce" In sha Allahu."
Bai kashe wayar ba sai da ya ga na sake har muna hira da dariya sannan ya kyaleni.
Amman bayan mun gama wayar tagumi kawai na yi ina tunanin makomar rayuwata. Ina kwaɗayin na ƙara haihuwa, an ce komai na mahaifata lafiya kalau zan iya samun ciki kowani lokaci amman sai yaushe? Sama da shekaru uku tun ina saka rai har na fara gajiyawa? Ni kaɗai na yi ta kukana ina sharan hawaye kasa komai na yi kafin su Jidda su dawo makaranta jinin ya ɗan tsagaida sau ɗaya na sauya pampers, ban yi musu ko abinci ba cewa na yi su sha goldenmorn sannan in sun huta Jidda ta dafa musu ko farar taliya ne su ci da mai, ɗakina na koma kawai na kwanta ina jin kasala na rufe ni.
*Janafty*
*TURKEN GIDA.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿ï¸06*
Har bayan mangariba ina cikin ɗaki ban iya fitowa ba, na ci kukana har na ƙoshi na lallashi kaina. Baby ta zo za ta dameni da surutu na ce ta je Yaya Jidda ta kunna mata Cartoon. Ita kanta yarinyar ta lura da yanayina har yadda ƙasan idanuwana suka kumbura.
 "Umma ba ki da lafiya shi ne kike yin kuka?
 Sai da ta saka ni mirmishi, kanta na shafa kafin na ce" Lafiya ta ƙalau. Je ki wajen Jidda, kun yi sallah ko?
Sai ta gyaÉ—a mini kai.
 Jin abin da na ce ya sa sai ta juya ta fice daga bedroom ɗin na bita da kallo tana fita na ƙara fashewa da kuka, ƴaƴa biyu gare ni su Allah ya ba ni, yanzu in ban ƙara haihuwa ba suka zo suka mutu fa?
Tuna haka kaÉ—ai sai da ya sa na ji kamar jinina ya yi sama, domin ji na yi numfashina na barazanan barin jikina gabaÉ—aya tsabar tashin hankali da damuwa.
 Daga ƙarshe suma sun gaji da zama a falo su kaɗai sun saba in ina gida tare muke yi salolli da azkar mu yi karatun Qur'ani sannan na duba littafansu na makaranta muna yi muna hira, su kaɗai gare ni domin a wannan rayuwar ƴan'uwanka ma suna gudunka, Mijin ma ba lalle ya zama mai amana ba, su ko ƴaƴa ko akan bola uwa ke kwana ba su isa su sauya ma tuwo suna ba.
 Ganin har an yi sallar isha'i takwas ta gota ban fito ba sai ga Jidda ta kwaso mini Baby sun shigo har Bedroom ɗina, ina cikin bargo na dunkule suka hawo har saman gadon suna kiran sunana.
'"Sannu Umma? Kan ki ke ciwo?
 Haka Jidda ta tambaya, sai na yi ƙoƙarin goge idanuwana na miƙe zaune ina faɗin"Na ji sauƙi, kun yi sallar isha'i? Jidda ta ɗaga min kai kafin ta ce"Har karatun Qur'ani mun yi na ƙara ma Baby na ta karatun"
Kanta na shafa kafin na ce"Allah ya yi miki albarka Jiddan Umma."
Baby ta ɓata rai tana faɗin"Ban da ni Umma? Sai itama na shafa kanta ina saka mata albarka, kantowa ta yi saman jikina, ni kuma sai na koma ina wasa da jelan kitsonta na 2step da akayi mata, da ya ke suna da tsawon gashi ni suka ɗauko duk da shima babansu da dangin shi gabaɗaya suna da cikar suma.
 Jidda ta yi ta yi ta zubo mini abinci na ce ta bari in na tashi zan sha Tea. Wanka na ke so na yi ga kaya can da na ɓata ma ban wanke ba, Baby har ta yi barci a jikina sai na ce Jidda ta ɗauketa zan ta shi.
 Tashin ta ta yi, domin ba ta iya ɗaukanta Baby akwai jiki a cure, bayan ta tashi ta kama hannunta zuwa ɗakinsu na ce ta tabbatar ta kaita tiolet ta yi fitsari, na ɗan ƙara samun natsuwa ganin jinin ya ɗan tsagaita amman bai ɗauke gabaɗaya ba. Wanka na yi, na fito kenan na ji buɗe get na san Yallaɓai ne.
 Ba ni da wani ƙarsashi sai kawai na zura wata rigar barcina doguwa, kaina buzu buzu ko ta kan shi ban bi ba, haka na koma gefen gado na zauna ina tunanin abin yi? Sai na ji kamar ina rasa tunanina na wani lokaci saboda halin damuwar da na ke ciki.
 Ina jin sa sai da ya shiga ɗakin yara ya gansu sannan ya ƙariso Bedroom ɗin mu, yanayin yadda ya ganni kamar ƙanwar mahaukaciya shi ya san ya yau ɗin fa ba lafiya.
 Hannuwansa ya buɗe mini alamun in ta so amman na kasa tashi, kallonsa kawai na ke yi hawaye suna cika mini kwarmin idanuwana. Shi ko ganin naƙi tasowa ya sa ya tako gabana, hannunsa akwai brief case ɗinsa sai wasu takardu, sai da ya sauke su saman madubi sannan ya ƙariso gabana ya durkusa lokaci ɗaya ya na rike mini duka hannuwana.
 Ina jin ya riƙe ni sai kawai hawayen da na ke ta riƙewa suka kwaranyomin a saman fuskata, marairaice fuska ya yi kafin ya ce"Haba Sadiya ta, ba na ce ki bar damuwa ba? Kin kuma ce min kin bari? To me ya sa kike kuka kuma? Kalle ki fa Yallaɓanki ya dawo amman kin kasa taran shi da irin mirmishinki da kika san ya na kwantar masa da hankali, sai ki tare shi da kuka? Alhalin kin san kukan ki dai dai yake da yi ma kwanciyar hankalinsa barazana?
 Ya ƙarishe faɗa, ya na kallona ni kuma sai na ji raunina ya bayyaana share mini hawaye ya ke yi da tattausan hannayensa duka biyu, faɗi ya ke yi" Ki daina kuka, ki bar wannan kukan? Kina so na shiga damuwa ne?ko so kike yi nima na fara kukan? Uhm Sadiya ta?
 Sai kawai na riƙe masa hannunwansa da duka hannayena guda biyu, ban san ma lokacin da na barƙe da kuka ba, kuka wiwi kamar Jidda. Daman a jikin Yusuf kawai na ke samun daman wannan kukan, ba ni da uwa da ace Mama na raye ita zan yi ma wannan kukan. Gwaggo kuma ba na zuwa gaya mata matsalolina ita da Alhajinmu ba na so su shiga damuwa, sannan duka ƴan'uwana ba ni da sakewa da kowa sai Rahila, itama ta na da ji da na ta auran ba zan ta zuwa ina damunta, a ɗakin mu Yaya Auwal ne kuma shi Namiji ne sannan ya yi nesa da mu, Amina kuma ƙanwata ce itama kaduna ta ke aure, Datti kuma yana makaranta sai in ya zo gida hutu.
 Dole dai kafaɗan Yusuf ne abin jingina na in yi kukana shi kuma ya lalace wajen lallashina, har a raina ina jin ƙila watarana wannan kafaɗan da na ke kwanciya na yi kuka za ta iya yi min nesa da wat rana sai dai na yi kuka na a saman gwiwoyoyina ba zan iya samunsa a duk lokacin da na ke bukata ba, tunda ƙila ba lalle ya ƙare rayuwarsa da ni kaɗai ƴaƴa biyu kacal ba, ahalin ya na da yadda zai yi ya samu abin da ya ke so na mallakan yara da yawa.
 Lallashina yake yi da duka iya kalamansa bakinsa, amman sai da na ji zuciyata ta rage kunci sannan na daina kuka na koma shassheka, rumgumeni ya tashi ya yi bayan ya zauna gefen gado, yana ɗan tapping ɗin bayana alamun lallashi.