← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 76

Sashe 19

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ɗagowa na yi ina kallonsa fuskata jage jage da hawaye, shi kuma sai ya saka haɓan hannun rigansa zai share mini hawaye da sauri na kauda kaina na saka hannu ina sharewa da kaina cikin muryan damuwa ya ce"Me ya sa kika hanani na share miki hawaye Sadiya?

  Cikin dakushewar murya na ce" Saboda kar ka ɓata kayan ka."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Kaya? Me nene kaya? Ban so kar ki sake hana ni share miki hawaye, domin ina fatan har ƙarshen rayuwata na zame majinginar in za ki yi kuka, sannan na zama mai share miki hawayen ki, ba na so na ji kamar na gaza miki ne Sadiyata."

  Kai na girgiza kafin na ce"Ko ɗaya. Ba ka gaza mini ba Yallaɓai. Sai ma ni ce na gaza maka, na kasa ba ka farincikin da ka ke so, na kasa sake Haihuwa Yusuf, wallahi ina so na ƙara haihuwa ko ɗaya ne? Ko ɗaya ne ko? Ai kana so ko?

  Haka na ke faɗa da sauri da sauri  sai ya lura kamar ma na fara fita hayyacina sai ya yi ƙokarin rike mini hannu lokaci ɗaya yana faɗin"Shii. Kin manta muna da ƴaƴa? Ƴaƴan mu biyu Sadiya muna da Jidda muna da Baby? Me ya sa za ki yi ta damuwa bayan muma muna da ƴaƴa ba wai ba ki taɓa haihuwa ba ne"

  "Ba za mu rayu da ƴaƴa biyu ba Yusuf, in suka zo suka mutu fa?

  Haka na faɗa, ina jin har hannuna da ke cikin na Yusuf na rawa. Kallona kawai ya tsaya yana yi cikin mamaki kafin ma ya samu zarafin mgana na cigaba da faɗin.

  "Ina ta tunanin me ya sa lokacin da na kawo shawaran zan yi planning saboda makaranta ba ka hana ni ba? Me ya sa ka biye mini? Me ya sa ka amince, da ka hana ni da ka bar ni, na yi ta haihuwa ai wahala ba ta kisa, ba zan mutu ba sai lokacina ya yi, me ya sa ba ka hana ni ba?

  Haka na faɗa da ƙarfi sannan lokaci ɗaya ina jijjiga hannayensa, Kasa motsi ya yi sai kallona ya ke yi, yasan na fita hayyacina kuma ko ya yi magana ba zan saurare shi ba, sai kawai ya kamani ya yi mini wata irin rumguma da ƙarfi sai da na ji numfashina ya na barazana ɗaukewa dole na yi shuru amman fa na fashe masa da kuka.

  Ƙamƙam ya riƙeni yana faɗin"Ba na so, me ya sa kike irin wannan tunanin? Ba za su mutu ba in sha Allahu ba yanzu ba."

  "Yara suna mutuwa fa Yusuf? Ko Baby in ta mutu fa?

"Na ce ki bar cewa haka ko?

Ya yi min tsawa bayan ya ɗago ni yana mai ƙureni da ido.
Sai na sadda kaina kasa ina kuka.

"Kin yi nadama ne? Ko ba ki yi planining ba. In abin da Allah ya kaddaromana kenan Sadiya ba fa mu isa mu tsallake wannan kaddaran ba, kuma planning ba laifi ba ne domin kin nemi tazara saboda karatun ki, ko malamai ai suna mgana kan a yi tazaran haihuwa, me ya sa yanzu kike nadama? Ko an ce kina da wata matsala ne? Kin je asibitin nan an yi duk gwaje gwajen an tabbatar da lafiya lau mahaifanki. Side effect ne, kawai ya taɓa ki, kuma kusan daman komai na rayuwan yana da nashi amfanin da rashin shi, me ya sa za ki zauna ki rasa hankalinki? Har kina yi ma ƴaƴan mu fatan mutuwa?

  Kafaɗata ya rike duka biyu, sannan ya kira sunana har sau biyu na amsa sannan na ɗago ina kallonshi.

  "Kar na kara jin mganar mutuwa a bakin ki kin ji ko?
Sai na gyaɗa masa kai kawai ba tare da na yi magana ba, shi kuma sai ya koma ya na sharemin hawaye yana faɗin"In Allah ya so za ki kara haihuwa, in bai so ba duk som mu da haka ba za ki ƙara ba. Ubangiji ne ke iya tsara ma bawa rayuwarsa tun daga ranar haihuwarsa har ranar mutuwansa."

  Jikina ya yi sanyi, shi na ke kallo kafin na ce" Kai fa? Haka za ka zauna. Na san kana son yara a kallah dai ko ba da yawa ba kamar biyar haka."

Bai yi min mgana ba sai da ya gama gogemin fuska tas da haɓan rigan shi, ya na kauce ma mganar ne, ya mikar da ni yana faɗin"Mu je ki yi wanka"

  Kai tsaye na ce"Na yi wanka fa" muryata a shake, shima kai tsayen ya ce"Ba irin wannan ba, irin wankan da kika saba mini"
Ban san lokacin da na yi mirmishi ba, har cikin tiolet ya kaini, ya duka ya sumbaci bakina sannan ya fice ya barni, na ɗan samu natsuwa shi ya sa na ƙara tuɓewa na sake yin wanka lokacin da na fito ya na ɗakin shi ya taya ni na shafa mai na shirya, kwalliya ya ce yana so na yi masa ina shagwaɓewa na ce"Wani kwalliya kuma da daren nan Yallaɓai na?
Hararana ya yi kafin ya ce"Bashi za ki biya,  ki yi mini abin da kika saba na more kallon ki kafin na kwanta,."
Ganin na yi shuru ya sa ya marairaice ya na faÉ—in"Ko ba ki so na samu natsuwa daga kallon ki ne?

  Ina jin haka na yi saurin girgiza kaina. Kwalliyar na yi masa na saka riga da wando. Wandon mai ɗamewa ne, rigar ma haka shi ya tayani na gyara gashina na saka rebon zan saka hula ya ce na bar mai kayansa ahaka, to kayansa ne shi ya sa bar masa kayansa.

  Na faɗa masa ban yi girki ba, taliya ne Jidda ta dafa, sai ya ce kar na damu ya siyo mana kaza. Falon farko muka fita ya ɗauko mana kazan muka baje a saman cafet muna ci, ya na bani a baki ina bashi muna hira haka sama sama sannan jefi jefi muna kallo.

  Na leƙa su Jidda har sun yi barci daman guda biyu ce muka ci ɗaya muka saka musu ɗaya a fridge, bayan mun gama ci muka ɗora da sanyayar maltina Yusuf ya kwashe komai da muka gama ya gyara wajen, ya kawo mini tissue ya goge mini hannuna da bakina shima ya goge na shi, kujeran mai zaman mutum ɗaya muka zauna ni na kwanta saman jikinsa,   shi kuma ya saka hannu ya rumgumeni yana wasa da gashin kaina, muna hira sannan muna kallo a tashar Mb2 ne ana wani film ɗin Horror ina ta cewa ina jin tsoro amman Yusuf ya ƙi sauyawa wai ba wani tsoro.

  Mu ne har 12 na dare sai da film ɗin ya ƙare, sannan muka kashe komai muka koma ɗaki. Yusuf ya yi wanka sannan muka kwanta muna rumgume da juna, dukkanmu mun yi shuru muna jin bugun zuciyan juna.

"Yallaɓai na"

"Uhmm"

  Sai na gyara kwanciya a saman ƙirjinsa ina faɗin" Ka yi hakuri, na gaza ba ka dukkan farinciki ta bangaren ƴa'ƴa. Na san kana son yara domin tun kafin mu yi aure in ka zancen wajena sai ka yi ta faɗin Sadiya ko ƴaya goma kika haifa min ba za su isheni ba, na daɗe da sanin kai mai so ka ga gidanka cike da yara ne, bayan haka kuma ƴan'uwanka ma son ka haihu da yawa Nene ma haka, uwa uba ƙannenka da suka yi aure bayanmu duk sun fika yawan ƴaƴa na san ko yaya ne kana jin ba daɗi a ƙasan ranka, ka yi hakuri ba ni da wata mafitar ne."

  Na faɗa muryata na yin ƙasa,. Kamar ba zai yi magana ba na ma ɗauka yana barci ne. Sai da na ɗago ta cikin duhun ɗakin akwai ɗan hasken dake shigowa ta window, na ganshi idanuwansa a lumshe, na fahimci ba barci ya ke yi ba da ya ƙara rumgumeni ƙam a samam kirjinsa. Ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Ni ba ki taɓa gazamin ba,kin ba ni dukkan wani farincikin da ko wani namiji ya ke bukata. Kin zame min matar rufin asiri, da me kika rage ni? Ba ki rageni da komai ba mganar ƴaƴa na faɗa miki in biyun Allah ya bar mana mun gode in ya ƙara mana mun gode, mganar ƴan uwana kuma wannan na su ra'ayin ne, ba wanda ba ya son ya tara kyakyawan zuru'a Sadiya. Ita kuma Nene ki daina maganarta jikokinta nawa? Me ya sa sai nawa ne za ta damu domin ban haifa da yawa ba?

  Idanuwana suka kawo kwallah kafin na ce"Saboda kai ne Tafida. Kowa ya shaida kai ɗan gatan Nene, ne ta sha yi maka addu'an ka gaji mahaifinka wajen tara  zuru'a mai yawa. Sannan ka manta burin ka na sake haihuwata domin na yi ma Alhajinku takwara?

  Numfashi ya saki ya fesar kafin ya ce"Ban manta ba. In kin sake haihuwan zan yi ma Allah godiya in ma ba ki sake ba duka godiyar zan yi masa, ai bar ni haka ba ya bani biyu, ina waɗanda suke nema har yau ko ɗaya ba su samu ba? Ko ban yi ma Alhajinmu takwara ba, ƴaƴan sa nawa ne suka yi masa? Masu sunan Alhaji ai ba su da adadi  ballatana in sha Allahu za ki sake haihuwa bayan Alhajinn Gwammaja har Alhajinmu za mu yi ma takwara in sha Allahu."

  Kansa na ɗago na sumbata kafin na ce" Allah ya amsa" ya amsa min da Amin, ƙara shiga jikin juna muka yi, ya na so ya yi barci ni kuma ba na jin barci.

  "Sadiya ta"

  "Yallaɓai na."

  "Barci na ke ji,"

  Haka ya faɗa mini a saitin kunnena, sai na yi mirmishi kafin na ce"Saura magana ɗaya ta rage, in muka gama sai mu yi barcin ko?

"Umh"

Kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba, ni kuma sai na yi shuru saboda ina ƙoƙarin iya faɗin abun da ke cikin raina.

"Yallaɓai."

"Ina jin ki"
Chapter 19 · 0% Book details