← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 76

Sashe 34

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yallaɓai na ji sa shuru har bayan mangariba sai da na kira sa ya ce bai dawo da wuri ba ne.  Zai je gida ya yi wanka sai na ce ya taho da su Jidda tare da Saude asibitin ya amsa min da toh.
GabaÉ—ayanmu muna asibitin har sai da likita ya yi mana tsiyar Alhaji ba zai mutu ba zai ta shi mu je gida hakanan saboda sun ga zugan ne da yawa.

  Tare da Alhaji Mustapha Yallabai suka shigo wajen da muka zazzaune. Kowanne da leda su Jidda na baya Yallaɓai dai kayan lambu ya siyo shi kuma mijin Ma'u ban sanin masa ba. Su dai an bar su sun shiga duba Alhaji ya farfaɗo da sauki wannan karon har sun gaisa ya ce ina yan matansa Yallaɓai ya ce suna waje suma sun zo duba megidansu.

  Ganin ya farfaɗo da sauki sai likita ya ce mu shiga gabaɗaya mu duba shi amman da sharaɗin ban da hayaniya kuma muna dubashi mu fito mu tafi gida. Haka ko aka yi ɗaya bayan ɗaya muna ƙarisa gaban gadon shi muna gaishe shi yana amsawa ga jikokinshi kusa dashi Jidda har ta na bare masa ayaba ta nufi bakin shi tana cewa" Alhaji ga ayaba."
Aka saka dariya Baba Aminu na cewa" Ka ji min ja'ira tun É—azu ta ganni amnan ba ta bare min ayaba sai Yaya Sule dake kwance rai ga hannun Allah."

  Su dariya mu ma muna ta dariya Alhajinmu ya buɗe baki ta saka mai sai da ya haɗiye sannan ya ce"To ai ta ga duk yinii yau ina kwance ban ci abinci ba. duk ta fi min sauran matan nawa ita maimuna ban ma ganta ba "
Yana mgana sai ga Gwaggo ta shigo ta na faÉ—in" Gani nan na zo. Wace ce ta zo za ta yi min fashi miji."

"Gani nan. Tunda kin yi tafiyarki kin bar shi."

  Jidda ta faɗa ta na mirmishi gabaɗaya aka kwashe da dariya ban da Baaba da ke wani taɓe baki kamar ta ga kashi.
Yaya Hamza ya ce" Ai sai ba É—iyar Sadiya ba."
Anty Aina ta karɓe da faɗin" Ai Baby ce Sadiya sak. Jidda kuma Yallaɓai ce ba ta da hayaniya"

  Likita ne ya zo ya ce dubiyar ta isa haka kowa ya fita shi ya sa muka yi ma Alhaji sallama muka fito. Khaleesat na haɗa da Saude tunda can gida za su kwana na ce su wuce mini da ita. Ina jin Ma'u na neman yan kwana a gidanta ba ta samu ba Anty laila yar kano ce amman nan gida ta ce min zata kwana Baaba dai ban sanin mata ba na dai ganta da yarta suna ƙuskus.  Baba Aminu daman gida ne Baba Sani ne aka bari zai kwana da Alhajinmu Yaya Abubakar ya so ya je gida ya Huta ya ce miye amfanin shi? Shi zai zauna ya kwana har a sallami Alhaji.

  Wajajen tara muka bar asibitin Gwaggo a motar Ya Auwal. Shi Yaya Abubakar ya ɗauki matarsa a mashin dinsa ita kuma Rahila ya Muntari shima yana da mashin Baaba kuma a motar mijin yarta ni kuma a motar Yallabai ni da Ya'yana.
Mun yi sallama gabaÉ—aya Yaya Murja ta riga tafiya daman da megidanta ya dawo suka tafi tare Anty Aina ma mijinta na da wata tsohuwar benz shi ya zo ya É—auketa.

  Sai goma saura muka shiga gida yunwa na ke ji ya sa Yallaɓai ya siya mini tsire a hanya da lemu sai ya siya biredin da zamu ƙarya da shi da safe in Allah ya kaimu.

*Janafty*
*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SSADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

*🅿️10*

Tun da na tashi da safe na fara tunanin wani abinci zan dafa na kai ma Alhajinmu. Gashi kayan abincin mu duk sun ƙare kuma Yallaɓai har yanzu bai ce mini komai ba. Da safe ma Tea muka sha shima kayan tea ɗin saboda ya na yawan siyan shi ne ba sai ya ƙare ba shi ya sa shi ya kan zama na ƙarshen ƙarewa.

  Na daɗe ina tunanin abin da zan yi. Kafin na tsaida shawara yin tuwon shinkafa miyar agushi tunda shinkafar tuwon kaɗai gare ni. Sannan ina da kayan miya nikaƙƙe a frizer sauran kayan cefanen ba zai gagara ba. Tun safe na kira wayar Ya Auwal mun yi mgana ya ce sun je ma asibitin sun duba Alhaji da safe jikin sa da sauƙi ya na ta barci sun ɗan dawo gida su karya ne sannan su koma  ni ma na ce in na gama abin da na ke yi zamu zo asibiti tare da Yallaɓai in sha Allahu.

Yana falon farko ya na aiki na je na same shi na faÉ—a masa ina so zan yi ma Alhajinmu girki in za mu je mu tafin mai dashi.

"Me za ki dafa masa?

Ya faÉ—a ya na ture takardan gabansa lokaci É—aya yana kallona.

Kai na rausaya kafin na ce" Tuwo zan yi masa miyar agushi. ".
Kai ya jinjina mini kafin ya ce" Kina buƙatar wani abu ne?
Kai na gyaÉ—a kafin na ce"E. Ina son Nama da ganda. Sai ganyen Ogun ina da sauran stock fish da agushi É—in."

   Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Shike nan. Zan yi ma Musbahu waya sai ya siyo ya taho dashi."
Duƙawa na yi na sumbaci bakinsa kafin na miƙe ina faɗin" A huta lafiya Yallaɓai na."
Kai ya jinjina min yana ɗan mirmishi fita na yi daga falon bayan na rufe masa ƙofar saboda zane ya ke yi ba ya son hayaniya ɗakin su jidda na shiga ba hasken sai da na kunna dukkansu suna kwance suna barci ga darduman da suka yi salla nan da azkar din su ko kwashewa Jidda ba su yi ba ban tashe su ganin yau asabar kuma suna hutun Tahfeez ya kamata su huta tattara kayan na yi na maida shi a muhallin shi sannan na gyara ma Baby kwanciya ita kuma Jidda na zare mata Hijabin jikinta ganin da shi ta kwanta. Sake kashe musu hasken ɗakin na yi bayan na rage musu iskar fankar a hankali na rufe ƙofar kar ƙara ya tashe su.

  Tuwon na kunna gas na fara ɗorawa. Saboda ina so mu fita da wuri duk da za mu fara biyawa ta Gwammaja mu kai su Jidda sannan mu wuce asibitin. Ɗaki na koma ina gyarawa saboda Yallaɓai ya ce na haɗa kayanmu waje ɗaya mai wanki zai zo ya ɗauka sai na firfito da kayan ina haɗawa. Ni kaya ba su da yawa atamfofi ne da lesuna ƙananun kayana ni na ke wanke su da kaina in na samu lokaci tare da unders ɗin Yallaɓai na na yara kuma ba su taru ba ko sati biyu ba a yi da kawo musu wanki ba.

Bayan na gama haɗa kayan na saka su cikin ghana must go ɗin da daman saboda kai wanki ne in kuma za a dawo dasu a ciki ne a goge. Gyara ɗakin na fara saboda ya ɗan yi ƙura, sai na fara tunanin unders ɗin Yallaɓai duk sun yi datti ya kamata na wanke masa. Amman sai na duba ya na da sauran wankakku zan bari in Alhajinmu ya koma gida ya samu natsuwa sai na yi mana wankin. Allah ya sa ma ya na da su da yawa tun da in na samu kuɗi ina siyan masa da turaruruka in yi masa kyauta a matsayinsa na mijina.

   Ban ma gama gyaran ɗakin ba na koma kitchen na wanke shinkafar na saka kafin ma ya tafasa saboda in ya jiƙu ya fi danƙo. Ƙara komawa ɗakin na yi na gama gyaran na ɗauko abin shara na share sannan na ɗauko towel ɗin goge na gege madubi da jikin wardrope ɗina tunda ya na da glass. Sai kawai na ji yau gwara na yi aikin gidan tunda ba ma nan kar na ba ma Saude wahala tuna haka ya sa na ɗau waya na kira Sauden tun da ni na siya mata wayar saboda matsala irin haka bayan mun gaisa na ce yau ta yi zamanta ba sai ta zo ba sai ta ce mini toh.

  Ina tuwona ina aikina. Ban share falon farko ba saboda Yallaɓai na aiki amman gabaɗaya na share gidan na yi mopping sannan na turare gidan da turaren wuta na kajiji a burner.
Kitchen kuma ma bari sai na gama girki gabaɗaya. Sai da na tuƙa tuwon sannan Jidda ta taso ta na murza ido ta ganni ina fito da sabbin kolilina in da zan saka abincin.

"Ina kwana Umma."

Na waiwayo ina faÉ—in" Lafiya lau jidda. Ina Baby ba ta tashi ba ne?
Ta na murza ido ta ce" Ta na wajen Abba"
Sai na gyaɗa kai ina faɗin" Akwai ruwan zafi a flasks a saman dining ni da Abbanku mun ƙarya. "
Ta na kallona ta ce" Umma ba ki tashe mu ba to?
Ina kai kololin wajen sink ina faÉ—in" Na ga yau weekend sai na barku ku huta. In kun gama karyawan ki yi ma Baby wanka tare za mu fita. Gwammaja za mu kai ku ku zauna har dare."

"Umma ya jikin Alhaji?

Na ce mata da sauƙi ina ƙokarin fara wanke kololin sai ta ce in kawo kallonta na yi ina faɗin" Ki je ku karya. In gama aikin sai ki wanke sauran ki gyara mini kitchen ɗin" sai ta amsa da toh sannan ta wuce. Ni kuma bayan na wanke su na saka Towel na goge su tas sannan na kwashe tuwon a leda na ƙulla. Wajen guda goma na saka a kula sauran kuma guda huɗu na bar mana a gida in mun dawo mu ci ban ɗora miyan ba tunda har lokacin musabahu bai zo ba.

  Ban ko kai ga barin kitchen ɗin ba sai ga Jidda da leda ta kawo min ina karɓa na kalle ta ina faɗin" Uncle Musbahu ya zo ne?
Sai ta gyaɗa min kai. Ijiye ledan na yi na koma ɗaki na sako hijabin na fito falo in da suke da Yallaɓai muka gaisa.

"Anty Sadiya ya jikin Alhaji? Yallabai ke faÉ—a min bai ji daÉ—i ba?
Chapter 34 · 0% Book details