← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 76

Sashe 75

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na amsa masa cikin so da ƙauna. Sai kawai ya ce" Gani na ke yi kamar jiya jiya muka yi aure sai ga shi wai mun kusa cimma shekaru goma sha biyar da aure cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa."
"Nima haka na ke ji a zuciyata." Haka na faÉ—a masa na ke jin kamar jiya muka yi auran ashe shekarun sun tafi.
Ƙara kamkameni ya yi kafin ya ce" Har yanzu ba ki sauya daga Sadiyar da na fara sani yar shekara sha tara ba."
Nima ina mirmishi na ce" Kai ma har gobe baka sauya min a wannan gwarzon matashin da na aura a shekaru ashirin da bakwai ba."
Sai kuma muka kalli juna ta cikin duhun ɗakin da ɗan hasken da ya kan shigo ta window ɗin cikin bedroom ɗin kafin ya sumbaci goshina ni ma sai na maida masa martani na sumbaci kumatunsa kafin mu koma mu kwanta yama ƙamƙame dani kamar za mu koma abu ɗaya.

******

Wed.13 JULY 2015.

Rana ta ƙara zagayowa ranar da a irinta ne aka ɗaura mana aure ni da Yallaɓai a irin kuma ranar ne muka zama miji da mata. Jiya Yallaɓai ya dawo domin tun washegarin ranar da muka dawo daga Ɗorayi ya je kaduna sai jiya da daddare ya dawo. Kuma yau tun safe ya fita saboda Nene ta kira shi a waya tana son ganin shi. Bai ko tsaya a gida ya ƙarya ba ya fita wanka kawai ya yi. Su Jidda sun koma makaranta tun jiya sun tafi gidan ba kowa sai ni kaɗai Marwa ba ta dawo ba amma na kira Saude na ce ta zo ta ta ya ni mu gyara gidan.

  Na ba da a yi mana cake babba sannan a gida na ce zan yi mana zoɓo muna da sauran naman sallah na ce kawai sai mu yi amfani dashi bayan haka na yi dambun nama da yawa ya na nan. Kawai dai yar walima ce daga ni sai mijina sai ƴa'yana.

Saude ta zo da wuri tare muka gyara gidan ko'ina muka turare shi da turaren kamshi. Saude na saka ta dafa farar shinkafa tunda ina da miya da na yi a frigde sai na koma ɗaki na ɗau wayata na kira telanmu domin na ɗinka wani material mai kyau saboda wannan ranar na tuna masa yau zan yi amfani da shi sai ya ce zai aiko min da shi anjuma kaɗan. Sauran kazar da na siya wajen Surayya Halin yau na ce Saude ta ɗumama ta kai mini falon yara ni kuma sai na kunna data na shiga ina ganin saƙonni.

Na ga group ɗin gidanmu ana ta tagging ɗina ina shiga sai na ga  Ma'u ce ta sanar da Anniversery ɗin mu ana ta yi mana fatan alheri ni da Rahila da Ya Muntari.
"Mrs Injinya Allah ya ƙara dankon ƙauna."
In ji Yaya Auwal shi kuma Ya Hamza tagging ɗina ya yi kafin ya ce" Yallaɓiya an gangara a bautar ubangiji.. Allah ya zaunar da ku lafiya."
Haka suka yi ta ma Ya Muntari shaƙiyanci wai ɗankwali ya ja hula.
Nima na shiga ina amsawa cikin farimciki.
Na je na yi status amma ban saka hoto ba na dai saka Alhamdulillah!
Sannan sai na rubuta"

"Shekaru goma sha biyar cikin farinciki Alhamdulillah."

Duk da ban yi caption ba sai aka fara mini mgana ta private ana mana addu'a yawanci duk yan makarantar mu ne da muka yi BUK tare waÉ—anda na ke da lambarsu.

  Sai Adnan ɗin su Yallaɓai da ya gani ya ce min" Ma sha Allah Happy Wedding Anniversery Mrs Yusuf Muhammad Tafida."
Musabahu ma haka ya ce mini" Ma sha Allah Allah ya ƙaro danƙon kauna ta Yallaɓai"
Duk na amsa su. Sauran dai su Anty Bahijja ban ga sun gani ba. Zuwa na yi na zaƙulo hoton Rahila a waya na ranar sunan ɗiyarta da aka ɗauka na saka a status ɗina na c

" Happy 15 years Wedding Annivesary Mrs Muntari Amini yashe(Hubby)"
Sai na ƙara da emojin rawa da murna da dariya. Ina ta dariya saboda na san in ta gani sai ta yi mgana Ya Hamza ya fara gani kawai sai ya yi tagging ɗin status ɗin da cewa.

"Ina na ki hoton?

Ina dariya na ce ni ban da hoto ya ce ban isa ba. Kowa sai ya ce wai ina hotona da na Yallaɓai tunda na saka na Rahila. Ganin sun dameni ya sa dauko hoton da ranar idi ne ma Marwa ta ɗauke mu da wayata ni da Yallaɓai yana tsaye ni kuma na jinginar da kafaɗata a saman kafaɗarsa. Shi waya ma ya ke yi bai san ana hoton ba ni kuma ina mirmishi. Hoton ya yi kyau sosai yana sanye da farar shadda mai babban riga sai dai ya cire babban rigan. Ni kuma na saka leshi mai ruwan haske akwai zanen marun a jikin leshin sai ya haskani gabaɗaya.
Ina mirmishi shi kuma Yallaɓai ya ɗan sunkuya yana kallona aka ɗau hoton shi na saka a kasan hoton sai na saka.

"Barka da shekaru goma sha biyar cikin Aminci, soyayya, sadaukarwa a gare ka ya amintattace na. MRS HALIMATUSADIYA YUSUF MUHAMMAD (YALLAƁAI NA)"
Na ƙara da gayyar emoji kafin ka ce kwabo duk yan gidanmu sun ce na tura musu  a group ɗin gida na tura hotunan tuni har sun sakamu a status daga ni har Rahila ni a bayan wannan sai na saka hoton Jidda da Baby shima da wannan sallan aka yi musu na yi mgana a ƙasa da cewa.

" A shekaru 15 da auren mu ga albarka da Ubangiji ya yi mana nan. Allah ya raya ku HAUWA'U YUSUF MUHAMMAD(Jidda) DA MAIMUNATU YUSUF MUHAMMAD(Baby)."

Kowa sai addu'a ya ke yi. Har ta Ma'u sai da ta ce na tura mata itama ta saka ta yi mana addu'a na amsa mata ko da bai kai zucci ba.

Na duba Yallaɓai ba ya online na kuma kira layin shi ba ta shiga. Sai kawai na tura masa test massages.

"Happy Wedding Anniversy Yallaɓai na"

Na jira na jira amman bai turomin amsa ba sai na yi tunanin ƙila Network ya sa bai shiga ba. Da ya tafin na kira shi na ji ko Jikin Nenen ne ya tashi sai ya ce mini yanzu ya iso gidan lafiyanta ƙalau sai hankalina ya kwanta.

Na yini cikin farincikina ina ta amsa wayoyin yan' uwa da abokan arzuƙa har mutanen fatakol Anty Zabba ta kirani ta na min fatan alheri Haka Munnira Hauwa dai wayar ta ya lalace ba ta sani ba.
Amma har Nafisa Muhammad Sani mun yi mgana da ita, sauran yan gidansu Yallaɓai duk waɗanda suka ga status ɗina mun yi mgana hatta da Halima Autar su Yallaɓai amma ban ga Anty Bahijja ko Anty Maimuna sun gani ba Mimisco dai tana online amma ba ta duba ba.

Ban damu ba, na cigaba da harkokina. Saude sai wajen uku ta tafi gida ni kuma salla kawai ke ta da ni a inda na ke Yallaɓai har lokacin bai dawo ba na kuma kira shi ta shiga bai ɗauka ba na ƙara kira shuru sai can ya turamin saƙon zai kirani ya je wani waje ne ni kuma sanin sabgoginshi sai ban damu ba.
Na cinye sauran kazar hadin uwargida duka na sha gumba sannan na sha kayan marmari ranar ko abinci ban ci ba har Jidda suka dawo makaranta daman na gaya musu in Yallaɓai ya dawo da daddare za mu yi walima Jidda ta ce" Umma waliman mene?
Ina mirmishi na ce" Na cikar mu shekaru sha biyar da aure ni da Abbanku."

Da ya ke ta na da wayau sai ta ce" Umma Allah ya bar ku tare." Na amsa da Amin Baby kuma sai tsallen murna ta ke yi, ko kafin mangariba har ɗinkina an kawo min daman kunshin sallar da na yi bai fita kitso kuma daman bai dameni ba ƙara gyara kaina kawai na yi, na saka Jidda ta ƙara gyara gidan ta kunna turaren wuta. Ina da bloons na ma Baby ne jidda ta kama min muka hura su na ɗaura su a falon mu wajen guda ashirin kala kala. Sai falon ya yi kyau sai bayan mun yi sallar mangariba sannan mai cake ta aiko mini dashi da kwatance sai gashi a gidana ta online na siya ƙanwar wata mate ɗina ce da muka yi Buk ce ke  yi.
Sannan na siya ma Yallaɓai gift wani agogo mai kyau 25k shima a wajen wacce muka yi BUK na siya daman kayan maza take saidawa na saba siyayya a wajenta in dai zan siyam Yallaɓai wani abu na gift wajenta na ke siya.

Bayan mun idar da salla mangariba muka ƙara kawata falon a center table na ijiye cake ɗin sai muka zagaye shi da voul na nama da dambun nama cake, da donut sai lemuka da ruwa. wajen ya yi kyau muna gamawa na ce Jidda ta kashe hasken falon in an ji motar Yallaɓai yana shigowa sai a kunna daga nan na ce su je ta yi wanka ta yi ma Baby na ce su saka dogayen rigunan da na siya musu yan kati ita na Jidda riga da wando ne. Baby kuma doguwar riga ce kala ɗaya na siya musu mai kalan baƙi da fari.

Nima na shiga bedroom ɗina na tuɓe na faɗa Tiolet na yi wanka amma a ƙasan raina ina tunanin ina Yallaɓai ya je? Ko kaduna ya je? Ya ce zai kirani amma shuru har na fito wanka ina wasi wasi. Daman na yo alwalata ana kiran isha'i na kabbarta salla bayan na idar ne na zo na zauna gaban madubi na tsantsara kwallya mai ƙayatarwa.
Na gyara gashina na sake shi baya na yi ɗauri mai kyau ɗinki riga ds sikat ne sun kamani sun yi mini cif a jikina haka na yi ma kaina barin turaren humra ko'ina na gifta ina tashin kamshi na saka wani takalmina baƙi mai ɗan tsini kaɗan ina tafiya ya na ɗan ba da sauti kaɗan ƙwas! Ƙwas
Chapter 75 · 0% Book details