← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 76

Sashe 66

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Falo na fita dai dai Jidda ma ta fito da Hijabinta alamun ta idar da sallah ne.
"Barka da shan ruwa Umma."
Ina kallonta na ce" Yauwa barkan mu dai Jiddan Umma. Ina Baby?
Sai ta ce min ta na ciki ta na sallah, ganin ta juya za ta koma É—aki ya sa na ce" Taho ki yi buÉ—e baki mana Jidda.'

Cikin mamaki a fuskarta ta ce" Umma Abba bai dawo ba?
Kai na kaÉ—a kafin na ce" Yana hanya in sha Allahu. Taho ko kunin ki zuba ki sha cikin ki ya warware."

Sai ta amsa da toh hijabin jikinta ta cire ta zauna nima sai na zauna ta zuba mini kunun na ce kaÉ—an itama sai ta zuba nata sai ga Baby ta fito jikina ta faÉ—a tana faÉ—in" Umma azumi na goma.'
Ina dariya na ce" Lalle Baby mai himma ce kai kai har azumin ki ya kai goma?

Ta na washe baki ta ce" Umma ke guda nawa kika yi? Ina kallonta na ce" Ai muna tare da ke nima azumina goma."
"Yaa Jidda fa?
Ta faɗa tana kallonta ina dariya na ce" itama dai dai da naki." Sai ta miƙe ta na tsallen murna Jidda ta kalleta amma dai ba ta yi mgana ba saboda ba ta da hayaniya sosai.
Har muka gama shan kunu ba Yallaɓai ba dalilin shi Baby sai cewa ta ke yi Umma ina Abba? Sai na tashi na shiga ciki na ɗauko wayata na kira shi bai ma ɗauka ba a lokacin sai da na ƙara kira sannan ya ɗaga wayar na ji hayaniya a in da yake amma ba sosai ba.

"Yallaɓai na barka da shan ruwa."

"Barka da shan ruwa Sadiya ta."

Shima ya maida min martani. Mirmishi na yi mai sauti kafin na ce" Kana ina ne? Na ga an sha ruwa ba ka dawo gida ba."
Sai kawai ya ce" Ina nan zuwa na ɗan shiga Gwammaja ne duba Nene Daughter ta kirani ta ce da zazzaɓi ta yi ni"

Cikin jimami na ce" Ayya. Allah ya ba ta lafiya ka gaishe ta."
Ya amsa mini da Amin sai kawai ya ce mu yi buɗe bakin mu kar mu jira shi in ya dawo sai shi ya yi na shi ban kawo komai ba na yi fatan Allah ya ƙara sauki mu ka yi sallama.
Tare da yara muka yi buÉ—e baki ba mu ci abinci ba kawai kayan marmari muka sha sai ferfesu. Sai da muka yi sallar isha'i da tarawehi sannan muka ci abinci ni alale É—aya na ci ma na ji cikina ya cika Jidda ta gaji da wuri ta kwanta Baby ne ma ta É—an daÉ—e ba ta yi barci ba tana kallon cartoon sai da na kora ta na ce ta je ta kwanta saboda makaranta. Duk da ma yanzu 12pm suke tashi saboda azumi.

Tun ina saran dawowar Yallaɓai da wuri har na fidda rai sai na fara tunanin ko Jikin Nenen ne ya yi tsanani har sake kiran shi na yi ban same shi ba duk na damu. Ina ta tunanin Allah ya sa ba jikin Nenen ya yi tsanani ba ne kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tunda ni dai ba waya muke yi ba sai wani abu na jaje ko barka ni ba ma zan iya tuna last muka yi waya da ita ba gaskiya amma ina da lambarta kuma nima na san ta na da nawa tunda muna ganin status ɗin juna.

  Har na fara gyangyaɗi na ji ƙaran buɗe get sannan da shigowar motar Yallaɓai sannan na mike ina duba agogon wayata goma da rabi har ta gota sha ɗaya saura na dare. Ajiyar zuciya na sauke na fita zuwa falon farko dai dai ya buɗe kofar falon ya shigo muka ci karo da juna ni da shi.

  "Ya jikin Nenen?

Da haka na tare shi domin a zato na jikin nata ne ya yi tsanani ya sa bai shigo gida da wuri ba. Lumshe idanuwansa ya yi daga gani a gajiye ya ke saboda ya na ƙarosowa gabana ya rumgumeni yana mai sauke ajiyar zuciya nima sai na rumgumeshi ta baya ina faɗin" Nenen na lafiya ko?
Cikin muryan gajiya ya ce" Lafiya lau. Na gaji Sadiya ta ko'ina na jikina ciwo ya ke yi min."

Ko bai faɗa ba na ga hakan a muryan shi da yanayin shi sai kawai na ce mu je na haɗa masa ruwan wanka ya yi wanka sai ya ji daɗin jikin shi. Muna riƙe da hannun juna har bedroom ɗim mu ina tambayan shi ya jikin Nene ya ce min da sauƙi likita ya zo gida ya dubata.  Maleria ce ta kamata cikin tausayinta na ce" Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya. Amma dai ta ijiye azumin ko?
Sai da ya gyaÉ—a min kafin ya ce" Yau É—in ma ta É—auka da jikin ya zafi sai ta ajiye"

  Ina taya shi tuɓe kayan jikinsa ya ke tambayata su Jidda na ce sun kwanta. Kai ya kaɗa kafin ya ce" Na yo ma Baby tsaraba ya na mota na manta dashi."
Ban maida masa martanin mganar shi na tura shi zuwa kofa ina faÉ—in" Ka yo wanka."
Domin ni kaina na gaji barci na ke ji idanuwana har rufewa suke yi amma ban kwanta ba sai da na kwashe kayan da ya cire na zuba cikin kwandon kayan wanki na fito masa da wasu riga da wando masu taushi na barci. Lokacin da ya fito har na fara gangyaÉ—i sai da ya yarfamin ruwan hannunsa sannan na farka.

"Ki kwanta mana. Kina barci a zaune?

Ya faÉ—a ya na nufar gaban madubin É—akin. Sai da na yi Hamma sannan na ce" Zan baka abinci ne shi ya sa ban kwanta ba."
Bai juyo ba amma ya É—au mai ya na É—an shafawa ya ce" Yi kwanciyarki kawai na yi buÉ—e baki a gidan Nene amma zan duba na gani ko zan iya cin wani abu kafin na kwanta."

  Ban damu ba na ce to sai kawai na kwanta ina jin sa ya na faɗin" Haka za ki kwaanta? Tsabar barci umh kawai na ce masa. Daga nan ban san yadda aka ƙare ba sai dai can ina jin sa ya na cire mini rigan jikina ina ta masa magagi sai da asuba da muka tashi sahur ne na fahimci rigar barci ya sakamin kuma wani ikon Allah duk gajiya da zan ji da mugun barcina ta bakin Yallaɓai huɗu na yi na asuba na ke tashi wani lokacin ma kafin huɗun na tashi Yallaɓai ne sai na yi ta fama dashi kafin ya ta shi har mamaki na ke yi ina faɗin haka maza suke? Ni dai Yallaɓai sai na yi da gaske ya ke iya tashi Sahur in na tashe sa tun lokacin da na tashi sai ya koma barci da cewa in na gama haɗa abin buɗe bakin sai ya tashi, to fa in na gama sai na haɗa da jan hannun shi ya ke iya tashi in kuma zan kyaleshi sai an fara kiran salla zai tashi lokacin an gama ma Sahur ɗin.

  Kamar haka ne yau ma uku da rabi na farka barcin da gajiya duk sun sake ni na ganni na nannaɗe jikin Yallaɓai duk na yaɓa masa kafa. Sai da na yi mirmishi bayan na sauko daga kan gado na gyara masa bargo sannan na fita zuwa tiolet na ɗauro alwala na zo na shimfiɗa darduma na yi salla raka'a biyu na ɗan zauna na yi addu'o'ina sannan na miƙe na cire hijabin na nannaɗe tare da darduma na mayar  ajiyar su ban ta da Yallaɓai ba sai na buɗe kofar bedroom ɗin na fita na bi ta cikin kitchen sai na ga Yallaɓai ya kwaso kololin da na bari a falo zuwa kitchen sai na bubbuɗe na gani bai ci alelen ba amma dai ya sha zoɓo kuma ya sha kayan marmari, ban damu ba tunda Baby ba ta azumi sannan nima zan ci alalen tunda jiya ban ci ba.

  Gas na kunna na ɗora ruwan tea kawai. Muna da sauran buredi tunda jiya ya shigo da shi. Bayan na juye a fulas sai na ɗumama alalen sannan na soya ƙwai saboda Jidda da Babanta  sai da na gama komai na kai falo sannan na shiga ɗakin su Jidda na tashe ta, ina tashin ta Baby na ji ta yi zaraf ta miƙe tana faɗin" Umma nima zan yi azumin."
Kai tssye na ce" To ku wanke baki ku fito mu yi sahur."

  Daga nan na fice tiolet  na shiga na yi brush ina fitowa hannuna da danshin ruwa na lallaɓa domin na shafa ma Yallaɓai ruwa a fuska saboda ya tashi sai dai ina zuwa dai dai saitin kan shi wayarsa ta kawo haske alamun ana kira ban saka hannu ba sai na leƙa sai na ga Daughter na kira. Mamaki ya kamani me ya sa ta ke kiran shi yanzu? Sai wata zuciyar ta ce min ko dai jikin Nene ne?

  Tunanin haka ya sa sai na yi niyyar amsa kiran sai na saka hannu na ɗauki wayar na buɗe bayan wayar ta yanke. Tunda na san password ɗin wayarsa ina shirin kiranta ne kawai sai ga saƙon ta ya shigo wayar har ga Allah ba halina ba ne duba wayar miji duk da wayar Yallaɓai ba ta da shamaki a wajena ban taɓa tunanin bin diddiginsa ba. Kuma har ga Allah lokacin da saƙon ya shigo hannuna ne ya faɗa kan saƙo sai ya buɗe kuma ban isa a lokacin na hana idanuwana karanta abin da ta rubuta ba.

  "Daddy na a tashi a yi sahur. Ko duk santin girkin nawa ne yasa ka kasa tashi? Na ga tuƙwaici na gode. Amma ka yi min laifi domin na ce ba zan karɓa ba yanzu haka ma za su dawo wajenka domin zan siya ma ƴaƴana kayan kwalliyar salla da su. Thank you so much for been their for me Daddy."
Chapter 66 · 0% Book details