Sashe 16
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Ɗagowa na yi ina kallonsa, in na ce zan yi magana ma ba zai fahimta ba sai na gyaɗa masa kai, yana zaune a gefen gado ya miƙaar da kafarsa ga laptop samansa.
 "Ki yi barcin ki. Zan yi aiki ne."
 Sai na ƙara jinjina masa kai. Zane zai yi, tunda Mijina Yusuf ya karanta fannin zane zane ne Archicture, sai kuma fannin da ya yi ma haye shi ne kwangilan gine gine, shi ya sa ya samu sunan injiniya, tun a sanina da Yusuf mutun ne mai neman na kansa mai fafutuka, ina ta kallonsa yana aikin sa, in muka haɗa ido, sai ya yi min mirmishi nima na maida masa martani har barci ya sace ni ban sani ba.
 Tun asuba wayar Anty Bahijja ta tashe mu, wai Halima a asibiti ta kwana naguda. C.S ma za a yi mata. Wayar ɗan'uwanta ta kira nima shi ya ke faɗa mini. Na so na huta a gida ranar amman ya na iya cewa ya yi na shirya nu fita tare ya kaini asibitin sai ya wuce Office. Ba ni da mafita haka na sake shiryawa bayan mun karya, ko da sha ɗaya ta yi muna asibiti, wani asibitin kuɗi ne sanda muka isa an shiga da ita tiyatar ma.
Mun iske su Anty Maimuna da Anty Bahijja, Anty Zuwaira ta zo amman ta wuce makaranta suna da taro.
 Muna nan Mutaƙƙa ya zo, bayan mu ga mijinta da yayarsa. Mutaƙƙa tare suka fita da Yallaɓai., ya ce zai kira Hauwa ta yi girki ta taho zuwa anjuma.
Zaman jugum jugum muka yi duk na gaji har aka fito da ita daga Tiyata an samu nasaran ciro mata namiji, an kawo mana jaririn ita kuma sun kaita É—akin hutu ba ta farfaÉ—o ba.
 Ranar dai a asibitin nan na yini, gajiya na yi da la'asar na ce ma Anty Bahijja zan ta fi, tunda ita Anty Maimuna ta koma gida, Badawiyya ce ɗiyarta ta biyu ta zo, Hauwa sai wajen biyu na rana ta zo da abinci, ni ban ma iya ci ba, saboda ba na iya cin wani abu in dai a acikin asibiti ne sallah ne da ya zame min dole na fita can haraban asibitin in da masallaci ya ke na yi sallah.
 "Za ki tafi kuma? Ba ki jira ta farfaɗo. Kuma ai na ɗauka sai dare in Tafida ya dawo sai ya ɗauke ki, ku koma gida tare."
 Mamakinta ya kamani, ita wai ba ta da tausayi ne, ko mijin Haliman ya ta fi gida yayar tasa ma tace bari ta je ta dawo. Ni fa na yi iya abin da zan iya yi ko ƙanwata ce ai sai haka, kuma ba zan zauna domin na faranta musu ni na ƙuntata ma kaina ba. Sai na buɗe baki na ce.
"A'a ba mu yi haka dashi ba, gida zan koma na takura da zaman waje É—aya. Zan dawo gobe da safe in sha Allahu."
 Wani kallo ta yi min kafin ta ce" Uhm! Ni ban ma tsaya bi ta kanta ba na ce ma su Hauwa zan ta fi gida, lamgwabar da kai ta yi kafin ta ce"Na ɗauka sai dare"
 "Wallahi ko Yallaɓai ya ce na zauna sai dare zan faɗa masa na gaji haba. Gida za ni da safe sai na dawo."
 Tana min dariya ni kuma na sha kuni, mun yi nesa da su Badawiyya, ta rakani har haraba asibiti sannan ta koma ita kan zama daram tun da sai Mutaƙƙa ya dawo zai biyo ya ɗauketa su koma gida yara ma gidan Nene ta kai su wajen Jawahir.
 Ko da na isa gida na gaji, wanka na fara yi sannan na nemi abin da zan ci indomie na dafa na ci sannan na dawo dai dai. Sai a lokacin na samu daman duba wayata na ga ashe Yaya Auwal ya kirani har sau biyu ban gani ba sai na bi bayan kiran na shi.
Bai É—auka ba sai na kyaleshi, Dan Abuja ne masu aiki a gidan kuÉ—i ba sa É—aga kira sai dai su kira, ba daÉ—ewa sai ga shi ya sake kirana. Bayan na É—auka mun gaisa da tambayan iyalai.
 "Ke wai me ya faru ne? Na ga ana ta cewa kun samu matsala da Ma'u a can group na gida?
Baki na taɓe kafin na ce"Rashin Fahimta ne. Amman Alhajimu ya daidaita mu."
Sai kawai ya ce"Oh. Ku ma dai kamar wasu yara. Sadiya kin girma fa ya kamata ki daina wasu abubuwan.".
 Da toh na amsa shi sanin halin shi, busy shi baya bashi daman zama ya gane abin da ke faruwa na kuma san sai yanzu ne hankalinshi ya kai kan abin da ya faru, daga nan muka sauya wata hirar.
"Yaya Auwalu me zan samu ne?
 Ya na yar dariya ya ce"Me zan samu dai Matar injiniya?
Baki na rufe ina yar dariya kamar ya na ganina kafin na ce"Ku ne masu kuÉ—in a hannun ku fa, ni dai faka faka ko yar wata ashirin ne ina jira."
 "Allah ya kawo."
 Daga haka muka yi sallama, bayan na ce ya gaida Aneesa da yara, nima ya ce in gaida su Jidda, mun gama waya ba daɗewa sai ga alert ɗin 10k ya turamin na yi mirmishi, shi ya sa fa nake son Yaya Auwal ba ya kiran banza, irin Yaya Hamza ne, ba su ba ka ɓacin rai amman kuma za su saka ka farinciki.
Ba irin su Yaya Abubakar ba, shi ai wani lokacin kamar wani mace haka ya ke jin kansa.
 Sau ɗaya na kira Alhajinmu muka gaisa bayan ya yi mana Sulhu da Ma'u. A raina na yi niyyar sai an yi wata ban je gida ba, Ma'u ta cigaba da zuwa a madadina.
Yaya Murja, har yau ban buɗe sakon ta ba ni fa ba na son munafurci, Rahila daman ita ban saka ta a lissafi ba ta da matsaya. In na ce ta na tsoron Ma'u sai ta ce ba haka ba ne, amman dai na san cewa tana ƙaunata, takaici na ɗaya tafi kaunar Ma'u sama da ni.
 Sai can mangariba Yallaɓai ya kirani wai ina asibiti ne? Na ce na dawo gida sai ya ce shi zai biya sun yi waya da Anty Bahijja ta ce Halima ta farfaɗo na ce to ya gaishe ta.
 Sai can dare ya dawo, bayan ya yi wanka muka zauna a dinining ya ci abinci, muna hira sama sama akan dai wani aikin kwangilan makaranta da ya yi sama da wattani goma shuru ba a biya su ba sun gama processing komai suna ta saka rai shuru, ni har na saba saboda na san yanayin aikin na su, kafin kuɗin su zo duk sai na hannun ya gama ƙarewa an jigata. Ko da zamu kwanta hirar da muke yi kenan, ina faɗa masa ko kayan abinci sun yi ƙasa ga haihuwan Halima ma, Allah dai ya rufa mana asiri.
 Ko a baya in ƙannensa ko yayyensa cikin ƴaƴansu sun samu karuwa in bashi da shi, ni na ke yi wani lokacin ma ba na jiransa in akwai kuɗi a hannuna, tsakaninshi da su dabam nima haka, in ban yi ba sai surutu ya tashi ko ba yawa ina zuwa na miƙa, ban damu da a gode ko kar a gode ba abin da na san zan iya shi na ke yi ba ruwana da yin abu don wani ya gani ko ya yaba, kai tsaye na ke yin al'amarina ka zauna da ni domin Allah ko akasinsa ruwanka ni ba ruwana harkan gabana kawai na ke yi.
 Da safe ma da ya shirya zai fita cewa ya yi ko zai ijiyeni a asibitin ne, na ce a'a ya je kawai in na shirya an juma zan je da kaina ina zan bi shi na je saman jumgum kamar ni ce na haihun. Sai azahar na fita bayan na ci na ƙoshi na je na iske asibitin cike duk da fa an ce a bar ta ta huta, dangin mijin ma kaɗan ne duk iyalan marigayi inuwa ne.
  Na iske Anty Zuwaira da Anty Maimuna. Anty Bahijja ne ba ta zo ba sai dai su Suhailat. Hauwa ma can na isketa amman ba ta daɗe da zuwa ba. Ban daɗe da zuwa ba Sai ga Hajiya Iya, tare da Suwaiba. Muna asibitin Maman farko ta zo tare da su Zulaihat, daga gidan gaisuwan suke, anan na yi ma Mama gaisuwan ma, Anty Zuwaira ce ta ce min wai ta daɗe ba ta ganni ba, ina yar dariya na ce"Mimisco ba ki zaman gida ko an je bakya nan."
Mirmishi ta yi kafin ta ce" In na dawo ai za a faÉ—a min kin zo ko? Har su Jidda ma ana yi min rowan su?
 Hakuri na ba ta na ce suna gidan Anty Maimuna amman za su zo mata in sha Allahu, Anty Maimuna na kusa ta na ji ta fara faɗin itama da ya ya na aikasu sai da ta yi ta mita ban takan ta ba, itama Mimisco ɗin da ya ke yar ba ruwanta ne ba ta wani maida kai kan mganar Anty Maimuna ba.
 Ni dai na ga mun yi yawaa a asibitin ana la'asar na yi musu sallama, na ce zan biya na gaida Nene an ce ta kwana da zazzaɓi, tare koma da Hajiya Iya, a gidan Nene na yi sallar mangariba sai na kira Yusuf na ce ina Gwammaja, in ya ta so daga Office ya biyo mu ta fi gida.
 Nenen ma ta ji sauƙi, tunda Anty Zuwaira ashe ta zo da safe sun je asibiti an duba ta an bata mganguna.
Ni dai na ce har da hayaniya saboda yaran Halima suna nan kuma ba sa jin magana sun cika ƙiriniya.