Sashe 74
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa" Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba."
Rahila ta ce" Ehem daman na san za a rina."
Yaya Aina ke faÉ—in" Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci?
Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce" Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne."
Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce" Mata kamar mai almatsutsai"
Ya Aina ta ce" Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi."
Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma'u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma'u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma'u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma'u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma'u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani.
 Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata sana'a za ta fara. kowacce na faɗin albarkacin bakinta nima sai na tofa nawa na ce ta saro dogayen riguna da takalma da mayafai na mata ta fara saidawa mu gani ko za su tafi. Sai Ya Aina ta ce yauwa ta ƙara har da atamfofi da kayan yara ni kuma sai na ce kayan yara ta jinkirta tukunna zuwa gaba ta fara da waɗanan dai ta gani yadda kasuwan za ta kaya.
Cikin mirmishi ta ce" Haka ma Shema ta ce. Da ya ke mun yi mganar da ita ta waya. Ya ce dai na tsaida shawara visa na fitowa Egypt za mu je a can zan yo sarin kayan nawa in sha Allahu."
Ya Murja ta washe baki tana faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ƙanwata."
Ta amsa mata da Amin Amin. Ita kuma Ya Balki ta ce " Sai ki faÉ—a ma Gwaggo da Alhaji su suka albarka."
Sai ta ce za ta faÉ—a musu sai mata fatan alheri suke yi nima na yi mata ta re da fatan Allah ya sa a fara a sa'a ta amsa lokaci É—aya ta na kallona kafin ta ce" Amin Sadiya. Amma fa kema ya kamata ki zo ki fara wata sana'ar zama haka ba daÉ—i."
Wani abu ya tsaya mini a maƙogawaro. Ma'u ta bala'in raina min wayau. Kuma kawai sai su Ya Balki suka amsa da wallahi kuwa Sadiya. Rahila ce ke faɗin" Ita fa Sadiya Shagon saloon da gyaran jiki take son buɗewa"
Ya Balki ta ce" To wannan ai lissafi ne me yawa. Ta dai yi tunanin fara wani abun kafin ta yi ƙarfin da za ta buɗe saloon ɗin."
Duk yadda na so na yi mgana sai kuma na kasa. Da na so na mayar mata da martanin mganarta ne sai kuma na yi tunanin ina yi magana za a ce ni ce fitinanniya Ma'u ta yi min mganar arziƙi na maida shi ta tsiya
 Sai kawai na kalli Ma'u nima sai na mayar mata da martanin mirmishinta kafin na ce" Kar ki damu ki maida hankali kan naki. Nima soon in sha Allahu Suprise zan ba ku."
Sai ta ce Allah ya yarda ta na min wannan dariyan na ta na mugunta. Ya Aina ko sai faman mgana take yi ta na cewa sana'a ita ce mace ko da mijinki na maka komai to ka yi dogaro da kan ka ko domin wata rana.
Ya Balki ta ce" Har da ma rayuwa Ya Aina."
Rahila ma na ji tana fadin itama za ta fara awo a cikin gida Ya Aina ta ce kasuwanci mai kyau. ita Ya Aina tana saida kayan miya da kayan nau'in É—anÉ—anon girki ita kuma Ya Balki tana saida gwanjuna. Ni ce daman ban saida komai sai Rahila Ma'u kuma daman tana nuna mijinta na mata komai sai yanzu ne ta zo da labarin za ta fara na ta kasuwamcin.
 "Albishirin ku"
Na faÉ—a ina musu mirmishi. Na gama cin abinci tuni har na sha ruwa na yi gatsa.
"Goro fari ƙal."
In ji Rahila da Ya Balki har suna haÉ—a baki.
"Nan da kwana uku za mu cika shekara sha biyar da aure ni da Yallaɓai na. Haka ma Rahila da Ya Muntari."
Na faÉ—a ina musu mirmishi.
Ya Balki ta fara cewa" Ma sha Allah. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Kai ashe kun daɗe kamar jiya ne na ke ganin bikin ku fa ke da Rahila?
Rahila na dariya ta ce" Sadiya ta na lissafi ni fa mancewa na ke yi. Ko da muka yi shekara goma sai da na ga sun yi walima ne na ce ma Ya Muktar yau auran mu shekaru goma Cif."
Ya Aina ta ce" Shekarun suna gudu ba wuya. Allah ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya raya muku zuru'a."
Muka amsa da Amin Ya Murja ma ta yi addu'a muka amsa mata. Sai Ma'u da ta gyara zama tana fadin" Ma sha Allah. Allah ya ƙara ɗankon kauna Mrs Yallaɓai da Mrs Ya Muktar."
Ni ce na amsa mata Rahila ta na jin kunya Zaituna ce ta yi karaf ta na faÉ—in" Sadiya akwai walima ne?
Ina mata dariya na ce" Akwai amma ta iya ni da Yallaɓai ce da yara."
Ma'u ta ce" Allah? Ban damu kenan? Ina mata fari na ce" Ai kun gama na ku tunda kun yi addu"a.
Ya Aina ta ce" Shi ne ko babban mgana."
Zaituna na kallah ina faɗin" Tambayi Rahilan Hubby ƙila za su haɗa mana walima."
Duka ta ɗaka min a cinya ta na faɗin" Sadiya ban son wulaƙanci."
Kamar zan yi kuka na ce" Wai don na ce Rahilan Hubby shi ne har da duka? Rahila sai kawai ta balla min harara kunya duk ya kamata mu kuma gabaÉ—ayanmu muka fashe mata da dariya.
Sai ta ji kunya ta tashi ta fita, ta na fita Ya Balki ta ce" Daga Rahilan har Muntari masu kunya ne."
Ya Aina ta ce" Wallahi ba su da hayaniya. Alhajinmu ya sha cewa tabbas an ijiye kwarya a gurɓinta."
 Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba Gwaggo ta ce Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shiri ta koma gidanta yinin ya isa haka. Jin haka yasa muka fara shiri saboda tun da Alhaji ya yi mgana to dole fa kowa ta kama hanya. Ni dai Yallaɓai na kira sai ya ce bari a yi sallar isha'i sai ya zo mu tafi gida. Ma'u ta fara tafiya Alhajinta ya zo ɗaukansu ita da yara haka ya yi mana yayyafim kuɗi goron salla damu da ya'yanmu ban sam kuma nawa ya ijiye ma Alhaji da Gwaggo ba. Su suka tafi da Zaituna da ƴaƴanta za su sauke su a gida daga can na ji Ma'u na faɗa ma Gwaggo za ta biya gidan su Shema'u.
Kafin ya zo daman Ma'u ta sanar da Alhajimmu da Gwaggo mganar jarin da ya ce zai ba ta su ka yi ta masa godiya da saka albarka.
Nima da Yallaɓai ya zo mun je gaban Alhaji na faɗa masa nan da kwana kaɗan auran mu zai cika shekara goma sha biyar da ni da Rahila.
 Alhajinmu ya yi mirmishi kafin ya ce" Ma sha Allah. Shekaru goma sha biyar masu albarka da tarin albarka zuru'a. Allah ya ƙara haɗa kawunanku. Haƙiƙa Yusufa da Muntari sun cika ƴaƴa tunda duk tsawon wannan shekarun ba su taɓa kawo min ƙaran ku da sunan kun yi musu wani abu ba hakan ma abin alfaharina ne. Allah ya yi muku albarka ya bar ku tare har jikokin ki."
Kan mu na ƙasa ni da Yallaɓai muna ta amsawa da Amin Amin.
Gwaggo na gefe ta na ta saka albarka kafin ta ce" Jiya ba yau ba. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Na tuna da Mama itama shekarunta a ƙasa kenan Allah ya jiƙanta ita da Hajiya gabaɗaya."
Muka amsa mata da Amin Amin da za mu tafi shima Yallaɓai ya ba ma yaran su Ya Murja goron sallah Marwa dai ta ce za ta bi Ya Aina zuwa gida amma jibi za ta dawo. Yallaɓai ya ba ma Alhajimmu kuɗi da Gwaggo amma ban sam ko nawa ba ne. Daga nan muka yi musu sallama ya ɗauke mu zuwa gida.
 Sai da muka koma gida har mun yi shirin kwanciya muna rumgume da juna Yallaɓai na shafa gashin kaina ya ce.
"Sadiya ta."
"Yallaɓai na"