← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 76

Sashe 1

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY). NA GODE BISA KARAMCINKI GARE NI, UBANGIJI YA RAYA MIKI ZURU'A AMIN*

*LABARIN TURKEN GIDA NA MUSAMMAN NE ZUWA GA ƘAWATA SURAYYA DEE(MARUBUCIYAR HALIN YAU) NA GODE DA MARTABAWA ƘAWATA. TURKEN GIDA NA GODIYA DOMIN KE KIKA SANYA MA LABARIN SUNA. A MADADIN NI DA MASOYANA MUNA YI MIKI TA'AZIYAR RASUWAR BABA YAU SHEKARU GOMA, ALLAH YA JIƘANSA DA RAHAMA ALLAH YA GAFARTA MASA AMIN. MUNA BARAR ADDU'ARKU FANMILY*

*GARGAÆŠI*

*LABARIN TURKEN GIDA HAƘƘIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE. A GUJI JUYA SHI KO SARRAFASHI TA HANYAR TAƁA SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BA NI DA MASANIYA. YIN HAKAN KAMAR SAƁA MA DOKAR HAƘƘIN MALLAKATA NE A KIYAYE.*

*MANUNIYA*

*LABARIN TURKEN GIDA ƘIRƘIRAREN LABARI NE.  DUK ABIN DA A KA CI KARO DA SHI YA YI KAMCECENIYA NA SUNA KO HALLAYA, GARI KO DAƁI'A. TO A YI HAƘURI AN SAKA NE DOMIN ARASHIN LABARI BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WATA ƘABILA KO AL'ADA BA*
*NA GODE*

_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI*_

https://www.wattpad.com/story/393283954?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=JamilaUmar315

https://www.tiktok.com/@jamilaumar630?_t=ZM-8w7lOpzJaYJ&_r=1

*🅿️ 01*

*SHIMFIÆŠA*

*NIGERIA, KANO STATE*
_AREA: LODGE ROAD KANO._
MONDAY, 2rd Feb. 2015.

Jihar kano, jiha ce da take a arewa maso gabashin yammacin Nigeria. Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilimota murabba'i 20,131 da yawan Jama'a miliyan sha ɗaya da dubu hansim da takwas da ɗari uku(a ƙiyasin 2011).

*****

ENGR. YUSUF MUHAMMAD INUWA ya fito daga masallacin dake can gaba da gidan shi, lokacin misalin shida saura kaÉ—an ne na safe, tun da ya saba sai ya tsaya ya yi azkar da yan addu'o'in shi bayan nan kuma ya kan É—an tsaya ya gaggaisa da mutane, duk da anguwan ta masu dashi ne amman akwai mutane masu mutumci da dattako mazauna a anguwa ko dai ba a haÉ—u a ko'ina ba magidanta na haÉ—uwa duk sallar asuba a masallacin, tunda wasu daga asuba sai asuban ake samun damar ganinsu saboda aiki, irin su injiniya Yusuf ma masu harkokin da yawa da baya ma samun zama ko yini a gida shi ko weekend ne yana fita tunda shi ba aikin gwamnati yake yi ba ma'aikaci ne mai aikin kai da kai da ya tsayu da kafafunsa tun da kuruciyarsa.
A ƙiyastin shekaru Injiniya Yusuf ba zai gaza shekaru 42 a duniya ba. Kuma ba zai iya haura haka ba, yana tafiya sannu sannu bayan barowan sa daga masallaci zuwa gidansa tunda kusa ne ba nisa, sanye yake da jallabiya baƙa mai kyau har tana kyallin sabunta kansa kuma da hula wata baƙar dara sannan hannunsa ɗauke da Casbaha. Dogo ne namiji ne a tsaye mai zati da haiba, a kallo farko in ka ganshi za ka shaida bafullatani ne saboda ya na da haske sannan sumar kansa za ta iya fallasa ko shi waye, duk da ba ma'abocin tara suma ba ne. Ba doguwar fuska gare shi ba tana da ɗan faɗi amman Injiniya Yusuf yana da kyau saboda yana da dogon hanci ga kwarjini da zatin na cikakkun maza.

Wani maidaidaicin gida ya nufa a anguwan Lodge road, gidan yana bakin titi ne saboda gabaɗaya anguwan tana shimfiɗe da kwalta ne. Fasalin gidan na ƴan gayu ne ko na ce ma tsarin gini ya sanu akan aikinsa. Sannan yanayin gidan daga waje zai iya shaida maka gidan ko ba sabo ba ne, to bai daɗe ba domin har a lokacin baƙin get ɗin dake gidan yana ta ƙyallin sabunta sannan fentin gidan daga waje mai ruwan ganye yana nan a sabuntar shi kamar yau aka yi shi, yana zuwa ƙofar gidan ya zura hannu a aljihun gaban jallabiyansa ya ɗauko key ya buɗe gidan ya shiga sannan ya maida kofa ya rufe, haraban shima ƙarami ne na zaman mota ɗaya zuwa biyu, sannan ga wata baƙar mota ƙiran TOYOTA C.HR. a fake a haraban gidan sannan haraban ya ƙawatu da filawoyi masu kyau da sha'awa suna fidda kamshi. Ƙofar da zai sada shi da cikin gida tana rufe ne itama sai da ya sanya key ɗin hannun shi ya buɗe sannan ya shiga kuma ya maida ƙofa ya rufe.
Falon gidan na farko ya fara iskewa wanda ba wani hayaniya daga kujeru sai ƙaton tibi dake kafe sai cafet ɗin tsakar ɗaki. Falon yana da girma sosai saboda daga can gefe ta hannun dama akwai dining mai zaman mutum biyar, falon kalan shi mai ruwan golden yellow mai haske, hatta labulayen da suka zagayen falon kalarsu kenan.
Daga falon ya fara cire takalmin kafarsa ya fara taka doguwar kafarsa mai cike da gargasa zuwa wata kofa dake fuskanta shi, domin falon shuru, ko'ina ya na rufe har wutan ma falon a kashe ne sai da ya yi amfani da hasken wayarsa duk da kuma akwai wutar nepa bai tsaya neman makunnin wutar falon ba, tunda ba zama zai yi a ciki ba.

  Ƙofar da ya sake buɗewa bai saka mata key ba tunda ta na buɗene. Tura ta kawai ya yi ta buɗe sai ga shi ya ƙara bayyana a wani ƙaramin falo mai ɗauke da kujeru guda uku ba manya sosai ba, sannan akwai tibin bango ƙarami ba wani babba ba sai cafet da Fridge babba mai kofa biyu. Daga can gefe kuma akwai dispanser a kafe shi wannan falon kalan brown ne, hatta shima labulanyan nashi suma kalansu kenan, shima falon tsit ba motsin komai, sai da ya saka hannu ya kunna wutar falon haske ya bayyana ko'ina. Daga tsakiyar falon akwai wata kofa a rufe, daga gefe kuma korido ne dogo da zai sadaka da wata kofa amman daga gabas ɗin sa kuma akwai wata itama a rufe ita ya taka ya nufa.
Sai ya ƙwankwasa lokaci ɗaya da sallama saboda daga bakin kofar kana iya jiyo sautin karatun azkar da wasu muryoyi sirara ke yi.
Buɗe ɗakin ya yi lokaci ɗaya yana shiga sannan ya maida kofar ya rufe. Lokaci ɗaya mirmishi ya wanzu a saman fuskarsa lokacin da ya yi arba da kyakyawan ƴaƴan nashi dake zaune a saman karamin cafet ɗin da ya ɗan rufe tsakiyar ɗakin. Duka mata ne babban kimanin shekarunta na haihuwa 13 da kaɗan a duniya ta na sanye da Hijabi baki har kasa da littafin azkar a hannunta sai ƙaramar mai kimanin shekaru biyar itama da irin Hijabin ɗayar a jikinta itama da ƙaramin littafin azkar a hannunta.
Sanda ya shigo har ƙaramar ta yi ƙokarim milƙewa da sauri ya ɗaga mata hannu lokaci ɗaya ya na faɗin.

" Ku ƙarishe azkar ɗin ku Baby."

Babbar ta kalleshi ta yi masa mirmishi sai shima ya maida mata, ya É—an jima tsaye yana kallonsu kuma yana saurarensu suna rera azkar É—insu cikin muryoyinsu mai sanyi da karaÉ—i, kamar ma sun haddace a kansu ba gargada ba komai agogon wayarsa ya duba ya ga shidda ta wuce na safe sai kawai ya kaÉ—a kai kafin ya ce" Jidda kar ki manta yau Monday in kun gama azkar É—in ku yi wanka ku shirya"
Da kai babbar ta amsa masa wacce ya kira da suna Jidda, ya juya ya fice ya na mai rufe musu ƙofar ɗakin a hankali kada ta ba da sauti, ɗakin daman ba shi da wani girma akwai tiolet a ciki sai ƙananun gadaje guda biyu kowani gefen shi akwai ƙaramin wardrope mai ƙofa biyu, sai daga can gefe ƙaramin dirowa in ds suke tara littafansu na boko da na isalamiya.
Yana fitowa ya nufi hanyar korido ya buɗe kofar ya shiga sai ga wani ɗan lungu ƙarami mai kofa na fuskantan shi, sai wasu kofofin na kallon juna. Ƙofar da ke hannun dama ya buɗe ya shiga da siririyar sallama a bakinsa daga bakinsa duk da ya san wacce ke cikin ɗakin ta na barci ba lalle ba ne in ta farko, ballatana ace ta ji shi amman tunda sallama wajibi ne ko babu kowa a ɗakin shi ya sa ya yi sallama sannan ya shiga lokaci ɗaya mai da kofar ya rufe.
Akwai hasken wuta a É—akin ya manta shi ya kunna lokacin da zai fita sallar asuba.

Yanayin kwanciyar da Sadiya ta yi ne ya sa sai da ya kusa sakin dariya shi kaɗai a sannu sannu ya karisa bakin gadon dake bedroom ɗin kafafunsa suna mai nitsewa cikin ƙaramin cafet ɗin da ya yi ma bakin gadon kwalliya.
Sanye take da kayan barci riga da wando, masu taushi kanta ba ɗankwali ko ma ta saka wajen barci ya cire, kuma ba ta yi kitso ba duk gashin ya birkice duk da a kallon farko za ka fahimci ma mallakiyar gashin ta na da yawan gyara. Kwance take a kan gadon amman yanayin kwanciyar ne abin dariya kafarta ɗaya ta sauka ƙasa, ɗayan kuma ta yi can gefe da ita ta buɗe kafarta kanta ya sauka daga kan filo sannan kwanciyar rigingine ta yi hannunta ɗaya ya yi yamma ɗaya ya yi gabas ne.
Kai ya girgiza kafin ya saka hannu ya ɗago kafarta guda ɗaya da ta sauka ƙasa ya maida ta saman gado, sannan ya gyara mata hannuwanta ya jirkitata ta yi kwanciyar gefen dama, yana shirin rufa mata blanket ɗin da ta yi gefe dashi ne ta yarfa masa hannunta a fuska a cikin barci sannan ta yi wani juyi sai da ta ture shi ba domin yana da ƙarfi ba sai ya faɗi saboda da karfi ta yi juyin. Kai ya kara girgizawa ya ja blanket ɗin ya rufa mata daga ƙafafunta zuwa cikinta, ya san ta na fashin sallah sannan a satin da ya gabata kaf ba ta zauna ba saboda Rahila ta haihu sun sha hidima.

  Wajen kanta ya koma ya tattara mata gashin kanta, rebon ɗin can ya tsince shi gefen da ya kwanta ya zura hannu ya ɗauko shi ya kama sumar kan nata duk da ba shi da cika amman akwai tsawo ya kama mata shi, sannan hular dake kanta a daran jiya mai taushi da ta yi wani gefe can ya ɗauko ya saka mata sai motsawa ta ke yi tana ƙananun kunƙuni na barci. Ba ta buɗe ido ba amman ta motsa kuma ta riƙe hannunsa mai cike da garsasa bakin ta ya motsa wajen faɗin

"Yallaɓai na."
Chapter 1 · 0% Book details