← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 76

Sashe 58

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ya sa na kira Rahila na ce, za a kawo mata su Jidda su kwana a wajenta kafin mu dawo tun da Salisu ya san gidanta. Saude kuma Yallaɓai baya nan ban taɓa kwatantan barin ta ita kaɗai da yara a gida ba.

Duk anan gidan Gimbiyar muka kwana. Abinci sai dai a kawo shi a dafen shi komai ga shi. Saboda ya na da kuÉ—i dan kwangila ne ya tara abin duniya kuma a baya ya yi siyasa.

Washegari ranar da aka yi sadakar uku da wuri su Yallaɓai suka iso shi da Uncle Abba da su Kawu Sa'adu sai Anty Bahijja. har cikin gida kuma sun shigo an yi ma juna gaisuwa.

Ni ina can ɗakin da muka kwana ba mu haɗu ba sai can yamma ma. Mun dai yi mgana ta waya da daddare kuma sun ƙara shigowa, a bakin Munnira na ji ta na faɗin wai Tafida ne ma ya matsa ma Gimbiya da lallashi har ta amince ta sha tee ɗin da yawa kuma sannan sai yau aka ji ta taɓa buɗe baki ta yi mgana amman ga Tafida kaɗai. Ban yi mamaki ba sanin shaƙuwarsu kuma a lokacin ai abar tausayi ce.

Washegari muka dawo kano amma mun bar Nene a can ita da Hajiya Kaltume da sauran ƴan uwanta. Mota ɗaya muka shiga da Anty Bahijja na ji suna mgana da Mimisco da cewa wai Gimbiya ba ta mgana da kowa sai Tafida sannan shi kaɗai ke ba ta abu ta karɓa ta sha. Su Nene haka suke yi kamar za su ari baki amman ba ta cin komai ba ta mgana sai kuka.

Anty Bahijja ta ƙare maganar ta da cewa" Ga shi kuma kin ga ba gari ɗaya ba. Balle a ce ko da yaushe ya riƙa zuwa ya na matsa mata ta ci abinci"
Ina kujeran zama ta tsakiya saboda motar irin babba ce ta yara ta mijin Mimisco ne.
Ni da Hauwa muna zaune waje É—aya har muna haÉ—a ido muka kalli juna amman ba mu yi mgana ba.

"Ba matsala ba ne. Jiya mun yi mgana Hajiya ana tunanin da an yi arba'in Gimbiya za ta koma Rano."

In ji Mimisco sai Anty Bahijja ta ce" Ai ya ma fi sauƙi. Allah dai ya ba ta dangana baiwar Allah."
Mimisco ta amsa da Amin.sai ita Anty Bahijja ta ƙara da cewa" To Nene fa? Ko itama tare da Hajiya Kaltumen za su zauna har arba'in ɗin?

Sai ta yi shuru kafin ta ce" In za ta iya sai ta zauna.  Tunda na taho mata da magungunanta da ta manta. Gida daman ba wani abu take yi ba."

Muna jin su suna ta tattaunawarsu har muka iso kano. Da ya ke mun iso da wuri Yallaɓai suna baya mun riga su yo gaba gaskiya. A bakin hanya na ce su sauke ni na samu adaidaita zuwa gida.

Sai da na isa gidana na yi salla na dafa indomie na ci sannan na dawo hayyacina. Sannan na kira Yallaɓai sai ya ce min suma sun kusa ƙarisowa, sai na ce ya kira Salisu ya faɗa masa in ya dauko su Jidda daga makaranta gida zai kawo su na dawo sai ya ce to.
Ni kuma sai na kira Rahila na ce mata na dawo sai ta ƙara min gaisuwa ni kuma na yi mata godiya har ta na cewa" Uban godiya ke fa ba ki da hali wani lokaci."
Daga nan ta kashe wayarta ta bar ni ina dariya.

Bayan Rahila da Laila ba wanda na faɗa ma an yi ma su Yallaɓai rasuwa sai gashi kwana ɗaya tsakani da dawowarmu daga Abuja a group gidanmu na ga Yaya Balki na yi min gaisuwa da na tamnbayi in da suka ji sai ta ce Yaya Murja ta faɗa mata da ta je gidanta itama ta ce Ma'u ce ta faɗa mata.

Abin sai ya bani mamaki na ga ni dai ba tamin gaisuwa ba. Amman ta je tana faÉ—a, ban yi mamaki ba tunda tana tare da Anty Bahijja ta kuma yarda da ita shi ya sa wasu labaran na dangin mijina kafin ni na kai ga furta ma wani Ma'u ta yaÉ—a shi a gari. Tsaki na yi a fili kafin na ce" Wannan ai gwara ta kashe auran nata ta auri Nasir ko Musabahu da wannan bin diddigin na ta."

A daren kuma sai ga ta ita da Alhajinta wai sun zo ma Yallaɓai gaisuwa. Kuma abin da ya ɓata mini rai shi Alhajin ya kira Yallaɓai ya faɗa masa za su zo amman Ma'u ba ta kirani ba, shima Yallaban ya kira wayata bai samu ba ƙwatsam na gansu lokacin shi bai ma riga ya dawo gidan ba.

Da ɗan fara'ata na karɓe su. Bayan mun gaisa sun yi mini gaisuwa sai na ce ai Yallaɓan bai dawo ba sai ya ce ai sun yi mgana dashi ya na kan hanya. Kafin ya ƙariso na kawo muusu ruwa da lemu na yi shinkafa da miya na kawo musu suka ce sun ƙoshi sai da suka ci abinci sannan suka fito daga gida.

Ba ko daÉ—ewa sai ga shi ya iso. Saboda mu ba su waje sai na ja Ma'u zuwa falon na biyu na kora su Jidda É—akin su bayan sun gaida Ma'u ta amsa cikin fara'anta har tana faÉ—in" Jidda idon ki kenan? Ina nan dai ina jiran ki a wannan hutun."

Sai Jidda ta fara kallo na, sai na yi saurin cewa" A'a ni ba ruwana ki tambayi babanki in ya barki in an yi hutu sai ki je."
Da sauri Ma'u ta ce" Ai ni dai na san Yallaɓai ba zai hana ba."
Sai kawai na ɗan yi yake. Muna zaune ba mgana sai baɓatun talabijin.

"Ashe kin je Abujan kema?

"Uhm"

Na faÉ—a ina kauda kaina ba na son kallon Ma'u saboda kallonta ba alheri a cikin yanayin kallon ta.

"Allah ya jikan sa."

Na amsa da Amin shuru na wani lokaci sannan ta ce" Allah sarki ta ba ni tausayi rashin miji ba daÉ—i."

"Ai fa kam."

Na faÉ—a ban bama mganar muhimmamci ba.

"Allah ya kawo mata kyakyawan zaɓi."

Na amsa da Amin na É—auka daga nan maaganar za ta tsaya sai kawai na ji tana faÉ—in.

"Anty Bahijja na gaya mini halin da ta ke ciki kamar in yi mata kuka ta ce mini ba ta cin abinci sai kuka ba ta kuma mgana da kowa sai Yallaɓan ki"

Kure ta da ido na yi domin na san daman sai ta zo wannan gabar."

"Ta ce min shi kaÉ—ai ke iya cewa ta ci abinci ta ci kuma shi kaÉ—ai take yi ma mgana. Abun mamaki ko da ya ke na ji labarin an ce daman sun shaku da juna."

Ta fada tana mini mirmishi.

"Haka na ji."

Nima sai na ba ta amsa amman ban nuna wani abu daga saman fuskata ba."

"Allah sarki. To bakomai tunda na ji Anty Bahijja na faɗin ana arba'in za a dawo da ita Rano  Sai na ce ai ko ga shi kusa ina Rano ina Kano? Yallaɓai sai ya riƙa zuwa yana kula da ita baiwar Allah abin tausayi.'

Ta gama faÉ—a har tana bayyana jimamin a saman fuskarta.

Ni na san da biyu ta yi wannan maganar sai kawai na yi mata mirmishi kafin na ce" Gaskiya ne. "
Sai na datse bakina ban kara yin mgana ba amman ina kallonta ta gefen ido tana mirmishi kafa É—aya ta É—ora kan É—aya kamar falon gidan Alhajin na ta ne.

Yadda ta ga na haɗe rai ina duba wayata ya sa ba ta ƙara mgana ba. Ba daɗewa ma sai ga shi Yallaɓai ya leƙo ya ce Ma'u ta fito za su wuce tsabar haushi iyakata a bakin kofa ban fita haraba ba Yallaɓai ne ya fita ba su shigo da mota ba sun yi parking daga waje ne.

Kamar maganar Ma'u ba za ta dame ni ba, sai gashi kuma tana sukan raina ace wai komai ya faru a dangin mijina sai  Ma'u ta sani in na ji haushinta ta wani fannin kuma ban ganin laifinta ba kowa ya ba ta dama ba sai yayar Mijina. Ta kuma wani bangaren itama Anty Bahijja sai na ke yi mata uzuri saboda in dai Ma'un da na sani ne makircinta zai iya siya mata kowa da kuma wannan makircin ta siye Anty Bahijja. Renin na ta har ya yi yawan da za ta zo har gidana tana gaya min mgana na ci ji yatsa da na ƙyaleta amman dai na san za ta ƙara wata rana dole za mu haɗu.

Washegari na koma asibitin domin ganin likita. Wannan karon ma Dr Aisha ta ce vaginal ɗina komai lafiya lau sai matakin gaba na A hysterosalpingogram a type of X RAY, that allows your provider to see your uterus and follopian tubes. Dr Aisha ta faɗa mini scan ɗin is very painfull  tunda na cikin mahaifa ne. Ta gaya mini zan iya bucking anan asibitin ko mu fita waje, da na kira Yallaɓai sai ya ce kawai na yi bucking anan asibitin, ban dawo gida ba sai da na yi bucking sun ba ni sati ɗaya na dawo su yi min scan ɗin. Ban damu da wahala ko wani abu ba babban burina na kai ga matakin nasarata shine a gabana.

******

BAYAN SATI UKU.

Bayan sati da huÉ—u rasuwar mijin Gimbiya a lissafi kuma bai fi saura kwana biyu ya yi arba'in da rasuwa ba.
Kuma har alokacin Nene da Hajiya Kaltume ke zaune da ita sai dai yan'uwa da ba su samu zuwa ba sukan je domin yi mata gaisuwa.

Har na ji Yallaɓai suna mgana da Mimisco akan a cikin satin su Nene za su dawo da Gimbiya gida.
Chapter 58 · 0% Book details