Sashe 39
Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Dubu ta faɗa tana gyara zama. Sai da ya kurɓi ruwa da cikin kwanon sha mai murfi da aka kawo masa sannan ya ce" Duk suna nan lafiya Hajiya. Rukayya da Maimuna duk suna gaishe ki. Takwaran ki kuma ta so ta biyo ni to sun fara zango karatun sakandiri na farko shi ya sa ban zo da ita ba. Sai dai ta yi jadadda mini saƙon gaisuwarta zuwa gare ki."
 Hajiya Duhu ta yi mirmishin farin ciki kafin ta ce" Duka ina amsawa. Allah sarki ashe takawara an sake zama ƴan makaranta. Ina jiranta in suka samu hutu."
"In sha Allahu."
Sun fara taɓa hira sama sama ta na faɗa mai gidan su Maimuna ma an yi rasuwa jiya ƙanin mahaifinta ya rasu sakamakon ba wayar hannu a lokacin sai dai a tada ɗan aike ya je ya faɗa. Daman tana shirin aika Sani ne sai kuma gashi ya zo.
"Allah Sarki. Allah ya jiƙansa. Daman tana ta zencen sa ashe jinya ba na tashi ba ne. Allah ya yi masa rahama."
Ta amsa da Amin Amin. Shi kuma ya ce zai je ya yi musu gaisuwa kafin ya tafi gobe in Allah ya kaimu.
"Gobe gobe nan za ka koma Sule?
Kai ya gyaɗa kafin ya ce"Saboda wajen aiki Hajiya. dama na ga kwana biyu ban leƙo ba shi ya sa na ce bari na zo na duba ku".
Ya faÉ—a lokaci É—aya yana buÉ—e jakarsa ya fiddo da ledojin guda biyu duk ya tura gabanta ya na faÉ—in" Sabulai ne da sai siga Hajiya. A yi hakuri ba kamar yadda na saba zuwa ba ne. Tsakiyar wata ne ba a yi albashi ba."
Ta jawo ledojin gabanta ta na faɗin" An gode. Allah ya yi albarka Allah ya raya maka zuru'a. Allah ya ba ka masu jiƙan ka kamar yadda kake jin ƙanmu. Allah ya ba ka aljanna sanadin wannan zumuncin naka."
Yana ta amsa mata da Amin Amin cikin jin daÉ—i.
"Hasiya dai na can lafiya ko?
Hajiya Dubu ta gyara zama za ta yi mgana kenan sai kawai ta ga inuwa daga saman kanta ta na ɗago kanta sai ta ga Asma'u tsaye ta na leƙen su. Shima Sulen sai ya kallo ƙofar ɗakin ya ga ana leƙe.
"Ke Asma'u zo nan.."
Sai ga ta ta shigo ta na laɓe laɓe hannunta ta jawo ta zaunar da ita a gabanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kowa ya zo ya gaida babanku ke ba ki da hausan zuwa ki gaishe shi?
Sai ta kalle shi cikin yarinta kafin ta ce" Ina yini"
Cikin sanyin murya kamar za ta yi Sule ya yi mirmishi kafin ya ce"Ina kwana dai ko?
 Ya faɗa ya na kallonta. Hajiya Dubu ta taɓe baki kafin ta ce"Haka ta ke. Tunda Hasiyar ta kawo ta wajen wata ɗaya kenan ta kasa sakin jikinta. Ga yara ƴan'uwanta ta kasa sakin jiki a cikin su sai ƙulafacin uwa."
Sai ya kalli Hajiya Dubu kafin ya juya ya na kallon Æ´ar yarinyar cikin mamaki ya ce
" Ƴar waye wannan Hajiya?
"Yarinyar wajen Hasiya ce fa. Wacce ta haifa da marigayi Hashimu."
Cikin buÉ—e ido ya ce"Dama ba tana hannun dangin babanta ba ne?
Hajiya Dubu ta ce"Uhm' kafin ta cigaba da faɗin" To Hasiya da ƙulafaci mana. Wai can Asma'u ba sa'aninta ba ta jin daɗin zaman gidan. Bayan ta yi auren nan ta amso ta ta tafi da ita to ashe dai zama bai yi daɗi ba sai gashi ta dawo mini da ita wai ta zauna a hannuna."
"Me ya sa?.
Ya faɗa cikin mamaki Hajiya Dubu ta amsa shi da cewa" To ta dai ce min yaran mijinta na ta sun ƙi karɓan Asma'u sai megidan ya ce ta maida ta dangin ubanta. Su kuma kasan duk mata ne ƙannen Hashimu wata ma ƙanwarsa da yake can ƙauyen gaba damu ta so ɗaukan Asma'u Hasiya ta hana shi ne ta bar ta a wajena ni zan riƙeta in har Allah ya aramin rayuwar."
Sai ya jinjina kai kafin ya kira Asma'u da hannun alamun ta zo. Hajiya ta tura ta gabanshi. Riketa ya yi ya É—ora ta a saman cinyarta ya na faÉ—in" Me sunan ki?
"Asma'u."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce"Ma'u ce" Sai ya ƙara kallonta kafin ya ce" Za ki bi ni can birni kano? Akwai abokan wasa kamar ki Rahilatu da Sadiya. "
Sai ta kalle shi kamar yadda Hajiya Dubu ke kallon shi sai Asma'u ta kalle shi kafin ta kalli Hajiya ita kuma sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba ruwana. Kawun ki ne in za ki bishi shike nan nima na huta.".
Sai ta ɗaga masa kai alamun za ta bishi. Sai ya dawo da kallonsa kan Hajiya ya na faɗin" Hajiya zan ta fi da Asma'u na je na haɗa ta da su Sadiya na sakata a makaranta. Ba zan bari a kaita ƙauye a gurgurta mata rayuwa ba"
"Allah ya ba ka lada Sule. Daman Hasiya burinta Asma'u ta samu rayuwa mai inganci. Allah ya taya ka riƙo"
Ya amsa mata da Amin Amin sai ta ce to Asma'u ta tashi ta haÉ—o kayanta a wanke saboda gobe Sule zai wuce zai tafi da ita. Sai ta fice tana murna. Hajiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ja'ira itama tana son bin ka ashe."
 Sun cigaba da hira har aka kira sallah ya yi alwala ya fita masallaci domin ya yi salla bayan ya idar ya daɗe a waje yana gaisuwa da mutane da aka kwana biyu ba a haɗu ba. Ya na wajen Aminu da babban ɗansa Muntari da Sani suka dawo daga gona rumgume ɗan uwansa Aminu ya yi yana murna da ganinsa Muntari ya duƙa har ƙasa yana faɗin.
"Sannu da zuwa Baba Sule."
Kansa ya shafa kafin ya ta da shi tsaye yana faɗin" Muntari ka ƙi zuwa dai na saka ka a makaranta tare da su Hamza ko? Ka gwammace ka yi ta zuwa gona da babanka ko?
Kansa na ƙasa ya na shafa ƙeya ya ce" Zan zo Baba in sha Allahu."
 Sani ne faɗin ai yana yin makaranta gwammati na cikin garin kusada. Sai Sule ya ce hakan da na kyau in ya gama ya zo ya same shi a kano domin ya nema masa ta gaba da sakandiri saboda ilimi na da amfani sun ga misali a kan shi da ilimin da ya yi ya zama abin ya zama yanzu.
Cikin gida suka shiga gabaɗayansu kamar yadda suka saba in dai Sule ya zo a ɗakin Hajiya Dubu suke haɗuwa su ci abinci. To yau ma haka suka yi bayan sun gama cin abinci suka sake fita suka raka shi gidan su Maimuna ya yi gaisuwa da alƙwarin in ya koma ita za ta zo in sha Allahu.
Ranar dai ya yini cikin ƴan'uwansa har dare suna tare Hajiya ta faɗa musu zai tafi da Asma'u Aminu ya ce gwara haka ƙila za ta fi sakin jiki sannan can za ta yi karatu nan kuwa sai dai ta ta ƙara tasawa a yi mata aure.
 A tsohon ɗakin su na zaure ya kwana gidan da ya ke ginin mutanen da ne na ƙasa ne da yaɓe. Da safe bayan sun karya ya yi wanka ya yi shirin tafiya kuɗi ya ba ma Hajiya Duhu ta yi ta saka albarka Asma'u an haɗa mata kayanta a kullen ɗan kwalli itama ta ci gayunta da takalminta ɗan madina da hijabinta da ya yi mata yawa.
Lokacin da Sule da Hajiya Dube suke sallama ya ce mata" Hajiya don Allah ki bari na zo na É—auke ki in na gama gina gidana ki koma can da zama."
Hajiya Dubu ta ce"To Sule in na bika su na nan ai sai su ce na fi sonka ne ko?
Su Sani na wajen su ka saka dariya domin su san ba ta son barin garin kwata kwata.
 Aminu ne ya ce" Hajiya da mu da Yaya Sule duk ɗaya ne. Mu ma za mu so ki samu rayuwa mai inganci da jin daɗi kafin wa'adi ya yi. Mu kuma ki bar mu anan mu ai ba yara ba ne muna da iyalai da yara. sai mu riƙa zuwa muna duba ki in sha Allahu."
 Ba ta dai ce komai ba sai ta wani rausayar da kanta alamun ba ta amince ba shi kuma Sule ya shuru ne ya dai gama gina gidan na shi tabbas sai ya ɗauke Hajiya zuwa Kano domin itama ta samu chanjin rayuwa.
Har ƙofar gida Hajiya ta raka shi da zugan yara duk ya sallamesu da kuɗi sulalla ya ce su je raba a tsakaninsu Muntari ne ya ɗaukan masa jaka yana gaba tare da Asma'u shi kuma ya na baya tare da ƴan'uwansa suna tattauna mganar gonar shi da ake noma masa tana hannunsu ne tun da sune suke cikin garin.
Sune har zuwa in da ya samu akori kuran da zai É—auke su zuwa babban hanya da za su samu motar kusada daga can su hau ta zuwa garin Kano.
*****
*KANO. Fagge.*
Ba zan manta ranar da Alhajinmu ya zo da Ma'u gidanmu ba. A wata ranar lahadi ne da yamma domin sanda suka iso ba ma gida muna isalamiya ni da Rahilaa mun dawo makaranta ne muka ga wata baƙuwar yarinya mai kallon mutane da idanuwanta a tsaye a cikin ɗakin mu.
A lokacin Yaya Aina ce kawai ta yi aure. Amman su Yaya Murja sune ƴan mata a lokacin ita da Yaya Balki tun da ba su da tsareyan haihuwa. Ita Yaya Murja ta na ajin kusa da ƙarshe a babban sakandiri ita kuma Yaya Balki tana ajin farko. Ni da Rahila ne muke tasawa a lokacin sai Amina da ke bin bayan mu a lokacin da Datti da ya ke namiji.