← Book details Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 76

Sashe 54

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuma shi  Secondary infertility ( rashin samun ciki bayan mace ta haihu ko hayayyafa) yana faruwa ne lokacin da mace ta haihu sai kuma haihuwa ta zo ta ɗauke kwata kwata ayi ta nemanta ruwa a jallo amma bata samuwa wani lokacin har sai an dangana da asibiti. Mace a haihuwar farko ta san lafiyarta lau saboda ta samu ciki ba tare da neman taimakon likita ko shan magani ba, amma kuma daga nan sai haihuwar tayi ɓatan dabo."

Nan ma sai ta É—an dakata kafin ta cigaba da faÉ—in.

"Yawancin abubuwan da ke haifar da secondary infertility sun haÉ—a da low egg quality(wato kwan haihuwar mace ya kasance baida karfin haihuwar) matsalar mahaifa, matsalar rashin karfin maniyyi, yanayin abinci da wasu abubuwan wanda suka danganci rayuwar mace kama daga yanayin cututtuka da uwa uba Family Planning"

Ta É—an É—ago ta kalleni ganin ina kallonta sannan hankalina na kanta ya sa ta É—an gyara zama gilashin ta sannan ta sake cigaba da faÉ—in.

  "Babban abunda ke kawo secondary infertility musamman a kasar hausa shine family planning wato tsarin iyali. Yawancin mata idan sunyi tsarin iyali yana haifar masu da matsaloli wanda cikin matsalolin nan babbansu shine sanadin family planning.
Family planning na haifar da jinkirin rashin samu ciki da wuri saboda karfinshi da kuma aikin da yake a productive system na mace
Kama daga hormones har zuwa Reproductive organs

"Kuma kowani abu ya na da Siide effect, kuma shi planning yana ninka adadin shekarunsa sau ɗaya ma'ana zai iya haurawa da kashi ɗaya, wani lokacin har biyu, kamar ke ɗin nan kin yi na shekaru biyar amman ya haura ki har shekara tara ba ki haihu ba, sannan kafin ki samu ciki side effect ya taɓa ki kin ta samun matsaloli ko?
Ba ta damu da na amsa ba ta cigaba da faÉ—in.

"Secondary infertility kuma mace ta taɓa haihuwa sai ta zo ta hanyar planning ko kuma haihuwar ta tsaya mata chak, shine za ta je asibiti ayi aune aune sai a bata maganin da zai dakile karfin planning din nan da kuma wanda zai taimaka mata wajen buɗe mahaifar ta da hormones ɗin don a samu cikin, kamar irin problem ɗin ki kin gane?

Sai na gyaÉ—a mata kaina alamun gamsuwa. Tana mgana da hausa ta na haÉ—awa da turanci a maganarta kawai na fahimci ita É—in kanuri ce saboda ba ta da hausa sosai.

Fayel É—ina ta jawo ta fara rubutu kafin ta ce" Kafin mu kai ga É—ora ki kan mgani Akwai bukatar sai kin yi wasu gwaje gwaje kamar yadda tsarin mu ya ke."

Mintina sama da biyu sannan ta sake É—agowa tana kallona kafin ta ce"

"Muna da gwaje gwaje a kallah guda tara waÉ—anda sai kin yi su gabaÉ—aya ne za mu iya gano ta in da matsalar ki take, da kuma hanyar da zamu É—ora ki kan mgani."

Gwaje Gwajen da ake sun haÉ—a da

1.A semen analysis (mace da namiji zasu tara, sai a tara sterile container a debi sperm din daidai lokaci  da namiji ke kawowa, da gaggawa ake yin awon sbd kada sperm cells din su mutu kafin ayi awon wanda hakan zai iya lalata sakamakon da ake bukata a wannan awon ne ake gane cewa sperm din namiji na active zai iya haihuwa ko aa.
2.Blood tests to look at hormone levels (zai nuna level din hormones, suna over secreting ne ko under secreting)
3.A transvaginal ultrasound 
4.A hysterosalpingogram, a type of X-ray that allows your provider to see your uterus and fallopian tubes( wannan da x-ray machine ake yin shi,zai nuna cikin mahaifa da kyallemun mahaifa duka honestly speaking its painful)

5.Blood tests. Samples of your blood can be tested for a hormone called progesterone to check whether you're ovulating. ...

6.Chlamydia test. Chlamydia is an STI that can affect fertility

7.Pap smears
8.FSH follicle Stimulatiing Hormone
9.LH Luteinizing Hormones
All these are the most common primary and secondary fertility tests for women."

Ta na gama yi min bayanan ta miƙo mini takardan mai tambarin sunan asibitin a jiki, hannuna biyu na saka na karɓa ita kuma sai ta maida hankalinta a wajen system ɗin gabanta.

"Ki je lab ki kai musu, za su yi miki cikakken bayanin a can"

A sanyaye na ce" Yanzu Dr?

"Yes. Ki je yanzu a can za su ƙara miki ƙarin bayani da yadda za a yi."

Sai na miƙe ina mata godiya.

"Sai an baki result sai ki dawo mun da shi , on Monday ranar da zai ma ranar clinic É—in ki."

Na yi mata godiya sai kawai ta gyaɗa kanta. Ina fita na nufi Yallaɓai ya na ganina ya taso, sai na bashi takardan ina faɗa masa yadda muka yi da ita sai ya ce mu je lab ɗin.

Tare muka je lap ɗin amman shi bai shiga ba ni ce na shiga na ba su takardan, laboratory ɗin da ya karɓa ya duba takardan sai ya ce.

"Muna bukatar ki zo da mijin ki "

Haka ya ce mini wani É—an baki ne, kai tsaye na ce" Tare mu ke yana waje."
Sai ya ce na je na shigo da shi, bayan mun dawo tare sun bamu wajen zama, sai wani lap tecnicial ɗin ya fara mana bayanin gwajin da za mu fara yi a matakin farko wato Semi analysis na sperm ɗina da na Yallaɓai."

"Ya za mu iya kawo muku samples É—in?

Yallaɓai ya tambaya sai ya kora mana jawabi a tsanake, yanzu dai ya ce za mu fara yin bucking ko gobe ko jibi za mu iya kawowa amman mu kawo shi cikin gaggawa. 
Kafin mu tafi sai da ya bamu sterile container  ya ce mu yi amfani da shi, kafin mu baro asibitin har kuɗin test ɗin sai da muka biya suka samu takardan da cewar sai jibi in sha Allahu za mu kawo ya yi ta jadaddamana da kar mu ɓata lokaci ana son a yi awon da gaggawa ne.

Mun fito daga asibitin muna hanya sai kawai na yi tunanin bari na tsaya a kasuwa na Æ´an siyayya ta daga nan na tsaya in yi saloon kafin na koma gida.

Nan take Yallaɓai ya tura mini 50k kuma ya ijiye ni a kasuwar Wambai.

"Yanzu sai ina?

Na faɗa ina ƙoƙarin buɗe motar na sauka bayan mun iso shagon da na ke zuwa gyaran kai kusa da kasuwar Wambai.

"Office zan fara zuwa akwai mutanen da zan gani."

Sai da na fita sannan na leƙa ta window motar ina faɗin" Ka tura list ɗin ga babban shago saboda su kawo mana da wuri"

Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Kin tabbata ba abin da za a buƙata daga baya?
Jin abin da ya ce ne ya sa sai na buɗe motar na sake shiga na karɓi wayarsa na dubo list ɗin da na tura masa.

Kallonsa na yi kafin na ce" Ina jin su kenan. Amman za ka iya ce ko zai duba wancan list É—in?

"In ya na da shi ba"

Ina Æ´ar dariya na ce" Ya na da shi mana. Ai suna ijiye rocord saboda babban shago ne."

Sai ya jinjina min kai kafin ya ce" ƙarfe nawa za ki koma gida?
Ina gyara zaman mayafin jikina zuwa saman kaina na ce" Da na gama siyayya zan koma gida in sha Allahu"

Hannuna ya riƙe ya sumbata kafin ya ce" Take care. Ki koma gida da wuri."
Ni kuma sai na sunkunya na sumbaci ƙuncinsa ina faɗin" Allah ya ba da sa'a."

Daga nan muka yi sallama ya sauke ni ya wuce, shagon wata Amesty ne anan na ke zuwa gyaran kai tun da daɗewa.  Ina shiga ta na ganina ta tarɓeni saboda mun saba da juna har lambar  wayar juna gare mu.

"Hajiya zuwa ba waya?

Ina zama kan ɗaya daga cikin kujerun dake cikin shagon na ce" Ba da niyyar zuwa na fito ba. Daga asibiti na muke sai kawai na ce Yallaɓai ya sauke ni anan, daman ina ta wa ƙen zuwa."

Yaran shagon na ta gaisheni, ina amsawa ita kuma sai ta je ta É—auko min ruwa. Ba musulma ba ce amman in ka ganta sai ka rantse musulma ce hausa a bakinta kamar jakar Kano dressing É—inta irin na hausawa ne.

"Na gode."

Na faɗa lokacin da ta ba ni ruwa na karɓa na sha kaɗan saboda ina jin kishi. Amesty na zaune gefe na tana faɗin" Ina su Jidda kwana biyu? Ina Baby mai kuka."

Ina dariya na ce" Duk suna makaranta."
Saboda ba ko yaushe na ke yi musu gyaran kan ba, amma na fi kawo su lokacin salla ko biki saboda ba ni da lokaci tsayawa na yi musu.

"Me za mu yi? Wankin kai ko Saloon?

Sai na zare mayafina na tuɓe ɗankwalina na zame ina nuna mata kaina.

"Saloon ko? Kamar wata biyu kenan ban yi ba."
Ta na dubawa sannan ta kalleni ta na faÉ—in" Gaskiya. Bari mu yi Saloon É—in"

Daman in dai na zo da kanta ta ke yi mini saɓanin sauran da yaran ta ke yi musu, ni kuma muna yi duk abin da na gani ina mata tambaya saboda ɓarayina ne, na iya wankin kai Saloon ɗin ma na iya, Amesty na dariya ta ce" Hajiya wannan shagon na Saloon sai yaushe za a buɗe shi?

Nima ina mata dariyan na ce" Yallaɓai ya ce Soon in sha Allahu.".
Sai ta ce Allah ya nuna mana.

Na yi awa É—aya da wani abu a shagon Amesty, kafin a gama min Saloon kaina ya yi kyau. Ba ni da kuÉ—i a hannuna sai na ce zan tura mata ta banki in na koma gida da haka muka yi sallama ta rako ni har waje.
Chapter 54 · 0% Book details