← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 124

Sashe 98

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani mataki ne mimi?".

"Sauran ma ka tsallake su, ba tare da ka sani ba, wannan ma dan kan ka nake son ka yi surrender ka tsallake shi. Kullum ina yi maka Addu'a, duk wanda na yi wa abu yaji daɗi, sai in ce ya saka ka a addu'a, komai zai zo ƙarshe fa"

Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan mimi, Allah ya yi mana jagora"

Ta ɗebo abincin ta kai bakinsa, amma ya girgiza kai ya ce "I loss my appetite, na ƙoshi".

"Dan Allah ka ci papa, zan yi kuka, kar ka saka na karaya na rigaka miƙa wuya, ba haka muka yi da anty aisha ba"

Cikin mamaki ya ce "You mean you set a deal with her a kaina?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"What was it?".

"This is not the right time to voice it out, i have to finish it first, but am sorry papa"

Idonsa fal hawaye ya ce "Shikenan miki, baki yi mini laifi ba"

Tuni hawaye ya gangaro mata, ta shafa fuskarsa ta ce "Dan Allah papa kar ka yi kuka".

"No mimi allow me, it really hurts me, ina jami'in tsaro na kasa bawa iyalina kulawa, har ta rasa ranta mutuwar wulaƙanci, ta haihu a dokar daji, what a mess".

Ruma da tuni ta fara sheshsheƙa ta ce "Daga baya na gane is not your fault, ka daina dan Allah".

Ya kwantar da rumaisa a ƙirjinsa, yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma hakan ya bashi damar, zubar da nasa hawayen silently.

A hankali ya ce "Ashe turanci ya fara zama Inyeee".

Ya zira hannu ya kamo hannun brziar ya ce "ina zamu je celebration ne? A buga cards, da  congratulations on your newly developed... Bai ƙarasa ba ta gantsara masa cizo a hannunsa ta tashi.

Dariya yayi, atleast ta rage damuwar da ta shiga yanzu.

***
Yasir kuwa kai da fata ya dage, ya ɗauki lambar iman a wayar mama, kasancewar mama ta kira iman da kanta, tana mata ƙorafin, ta daina zuwa gidan gaba ɗaya, wanda ba iman ba ƙaramar kunya ta ji ba.

Yayi amfani da damar, ya ɗauki lambar, ya yi wa iman magana ta what's app, bayan sun gaisa yayi mata bayanin shi ne, ya tura mata akwatuna ya ce ta zaɓi wadda take so.

Iman ta ce "Yasir duk abun da yaya umar ya bani ina so, ba zan zaɓi komai ba dan Allah ku ce masa kar ya wahalar da kansa yayi mini iya abun da Allah ya hore masa".

Yasir ya ce "Amma dai bani ni ne zan gaya masa hakan ba ko? Ai wannan aikin sai ke ko hajiya mama, ni a suwa, dan Allah ki zaɓa amma kar ki gaya masa"

Iman ba ƙaramin burgeta suke yi ba, suna matuƙar son junansu, fiye da tunani.

Ƙin zaɓa tayi, ta ce kowacce aka yi ta gode.

Da yamma mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ana ta cigaba da gini, yana tara kayan lefe, kowa ya fita ya dawo, sai ya kawo wani abun na kayan lefe, kuma Æ´an uwa basu gaza ba, da cigaba da kawowa mama gudunmuwa.

Turus yayi ganin wasu kyawawan akwatuna, guda shida da kid, haÉ—aÉ—É—u masu kyau.

Mai sunan baba bai tanka ba, sai da mama ta ce "Babana, mutuminka fa ya cika alƙawari ga akwatunanka nan".

"Meyasa Yasir ba ya jin magana ne? B jari yake tarawa ba, dan me zai kwashe kuÉ—insa ya yi wannan hidimar, sonake na ga me zan samu a cika masa, amma ya kwashe kuÉ—insa yayi wannan aiki, sai kuma da nace masa ya bari, yanzu kan ya mayar da kuÉ—in fa"

Yasir da yake tsakar gida, bai ji daÉ—in abun da mai sunan baba yayi ba, sai dai ko menene shi ya san yaya umar ha cancanci fiye da haka.

Mama ta yi ta yi wa mai sunan baba faÉ—a a kan bai kyauta ba.

Ko da ya fita tsakar gida, ya kalli fuskar yasir, fuskarsa ta nuna bai ji daÉ—in abun da mai sunan baba ya yi masa ba.

Har dare Yasir sabgoginsa kawai yake yi, ko É—an shishshigin nan da suke yi wa mai sunan baba, yau bai yi masa ba.
Sai dai da ya shiga ya fita, sai mama tayi ta saka masa albarka tana kwarara masa addu'a.

Har ƙarfe goma na dare, yasir bai shiga gida ba, mai sunan baba ya ɗau babur ya biya shagon yasir, ya tarar da shi yana ta aikin wayoyin mutane da system, shi da yaransa.

Horn É—in da mai sunan baba yayi ne ya dawo da shi hayyacinsa, ya ajiye wayar hannunsa ya fito.

Mai sunan baba ya bashi galan ɗin man fetur, ya ce "Gashi nan ka zuba a  injinka" Yasir ya karɓa ya ce "To na gode sosai"

"Ka rufe shagon nan mu tafi gida, dare yayi goma tayi"

Ya amsa masa da "To, bari na sallami yaran" ya wuce cikin shagon ya sallame su.

Shagon da Yasir yake harkar wayoyinsa da system, har ma da POs mai sunan baba ne ya kama masa shagon, ya saya masa system. Ya ce hauzaifa kuma ya iya É—inki, shegiyar shirirtar sa ta hana mai sunan baba bashi jari.

Yasir ya rufe shagon, ya hau babur suka tafi gida, a ƙofar gida mai sunan baba ya ce "Yasir".

"Na'am"

"Ban yi maka faɗa a kan abun da kayi mini dan na ɓata maka rai ba? Kaga jari kake tarawa, bai kamata ace na mayar da kai baya ba".

"To waye ya bani jarin?".

"Duk da haka bai kamata dan na baka na dawo na cinye ba, anyway ka daina fushin na gode sosai Allah ya ƙara buɗi, ya sanya ku fi haka, ya sanya maka albarka a nemanka" yayi maganar yana musabaha da hannun yasir.

Yasir yayi murmushi ya ce "Muke da godiya mai sunan baba"

"Nima yakamata na gode, na san ka kashe kuÉ—i sosai, Allah ya mayar maka da ninkin abun da ka kashe"

Ya amsa da "Amin Yaya"

Suka shiga gida tare.

***
Kwanan Adam huÉ—u da dawowa, rumaisa ta tarar da shi a É—akinsa, da travelling bag.

"Ya haka, me nake gani, wannan jakar fa? Ga breakfast can".

Ya ce "Kin tashi kenan?"

"Eh mana ina zaka?"

"Nemana ake a abuja, zan je na yi booking Flight"

"Daga dawowar taka za ka kuma tafiya?"

Takawa ya ce "Kiran gaggawa ne, suna buƙata ta, ba zan fi sati ɗaya ba"

Haushi ne ya kama rumaisa, kawai ta fice daga É—akin, ta koma nata.

Bin bayanta yayi yana kiran sunanta, ya tarar da ita a falo, ta cika tayi fam.

Ya zauna kusa da ita ya ce "Wai mimi meyasa ki ke da matsala ne, harkar aiki ne, idan ban je ba ya zan din ga samo mana kuÉ—i, na biya miki kuÉ—in makaranta, na saya mana abubuwa"

"To daga dawowarka sai ka kuma tafiya, kullum baka nan ai shikenan"

"To yanzu ya ki ke so ayi?"

"Kawai ka fasa"

"Mimi zuwana yana da muhimmanci, ga kuma karatuna na kammala, akwai aikace-aikace a gabana sosai da sosai, kiyi haƙuri 5days kawai in sha Allah zan dawo".

"Ni sai dai ka tafi da ni, idan ba haka ba zan yadda ba".

"To shikenan, zan saka ayi mana booking Flight shikenan"

Ta waro ido ta ce "Dan Allah jirgi zan hau?"

"Ƴar ƙauye zata hau jirgi"

Ruma har da tsalle ta ce "Wayyo daÉ—i, bani waya na kira yaya usy, na gaya masa zan riga shi hawa jirgi".

Yayi murmushi ya ce "Sai mun sauka tukuna, Ki É—aukko mana akwatinki guda É—aya, ki haÉ—a mana kayanmu"

Tashi tayi da sauri ta tafi tana murna yau zata hau jirgin sama.

Ta waya ta sanar da mama zata raka takawa abuja, amma ba zasu fi kwana biyar ba zasu dawo.
Aliyu ya ce "Yarinyar nan tana sararawa, taɓararta kawai take yi son ranta".

Rumaisa bakinta yaƙi rufuwa, da ta ganta a cikin jirgi, ta ce "Papa, yanzu idan nayi tsalle a jirgin nan, ya zai yi ƙasa zai yi".

"A'a sai dai idan yanzu zaki gwada tsallen".

Ta ce "Haba dai su rainani"

"Gaskiya dai, babbar yarinya kamar wannan mai abun arziki ai sai a rainaki"

"Zaka fara ko?"

Ya ce "Ban fara ba tukuna".

Ko da suka sauka taxi suka hau, suka nufi hotel É—in da zasu sauka.

"Papa, to ina gidan shugaban ƙasa yake a nan?"

"Me zaki yi wa shugaban ƙasar?"

Rumaisa ta gyara zamanta ta ce "Zan ce masa dan Allah ya saka a daina sace mutane, wallahi wahala ake sha sosai"

Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba.

Hotel É—in yayi wa rumaisa kyau, sai dai nanata masa take yi, ko sun koma gida kar su gayawa kowa hotel suka zo a abuja, kar ayi musu kallon mutanen kawai.

Da suka shiga bedroom ta ga É—aki É—aya tal, da toilet.

Ta ce "To ina banÉ—aki, da kuma kitchen da nawa É—akin?"

"Babu kitchen, a nan zamu din ga kwana tare"

"Kai, ni da kai a É—aki É—aya, kuma ba kitchen to me zamu din ga ci?".

"Saya zamu din ga yi"

"To waye zai din ga kwana a kan gadon?"

"Ke dai kin san ba zan biya kuɗin ɗaki in kwana a ƙasa ba ko? Sai ki nemawa kanki mafita"

Ya ajiye akwatin, ya nemi wuri ya zauna, ya É—auki wayarsa yana kiraye-kirayen wayarsa, ya ce a kawo masa mota.

Da daddare ya ɗauki ruma suka fita yawo, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ruma ba, duk da dare ne fitar tayi mata daɗi sosai.

Ta É—auki wayarsa ta kira Huzaifa, tana ta bashi labarin yadda jirgi yake, da abubuwan da ya sai mata.

Usman ya karɓi wayar ya ce "Ke wayar nan a handsfree take?"

Ta ce "A'a"

"To ki ba ya fita dake yawo ba, har kin hau jirgi kina yashe baki, ga uwar tsaraba da ya yi miki da ya dawo, idan. Ki ka kuma kawo mini ƙarar kin yi masa wani shirmen, wallahi kina zaune zai auri wata ya din ga wannan yawon da ita, gara a din ga gaya miki gaskiya".

Shiru tayi daga baya ta ce sai anjima, ta kashe wayar tana tura baki.

Takawa bai san me suke cewa ba, kuma bai damu da ya tambaya ba.
Chapter 98 · 0% Book details