Sashe 63
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. Saɓanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance ɗan wannan ɗaki da wancan.
Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haÉ—a Sharif da Bintu faÉ—a, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.
Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita.
A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.
Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban É—aki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.
Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taɓa ko ɓari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ƴan uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.
Ana haka mai babban ɗaki ta rasu, wanda hakan ba ƙaramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.
Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ƙaƙƙautawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ƙuruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna.
Aikuwa ta ƙwafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ƙiyayya.
Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.
Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi ɓari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba.
Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani.
Sai a karo na huɗu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ƙarshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ƙular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin ɗauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.
Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi É—a namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka É—auki soyayyar duniya aka É—orata a kan yaron nan.
Watanninsa shida, yayi zazzaɓin wuni ɗaya ya rasu.
Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ƙyar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake ɓari, sannan ta samu ciki ya zauna.
Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faÉ—ar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.
Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.
Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya ɓulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.
A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata Æ´ar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.
Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ƙaruwa, amma yana jin tausayin Bintu.
Ƙannen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faɗa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da haƙuri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faɗan ta rage faɗa.
Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.
Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matuƙar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu ɗaya da galadima.
Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama,
tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.
A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ƙalubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba ɗaya ya canza mata.
Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama biƙi ba ta al'ada sai dai ta ga ciki.
Ayshercool.
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please ðŸ™
Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ƙuduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita kuma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai.
Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taɓa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki.
Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu.
Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ƙarami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba.
Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karɓar mata ɗan ta, amma ya ce ta yi haƙuri, da ita da Jamila duk ɗaya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taɓa haihuwa ba.
Rashin ɗan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ƙarshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame.
Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta.
Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.
Laila ce ke satar jiki, ta ɗaukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta shaƙu da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan ɗaukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.
A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu Æ´ar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar É—an ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.
Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin É—an ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.
Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.
Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.
Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da feleƙe, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata haƙuri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.
Ammi ba ta taɓa tanka masa ba, dan a lokacin ta miƙa wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da riƙon abun ta, gefe tana zuwa makaranta.
Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka za a tsallake ƴaƴan bintu na ta su yi sarauta.
Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ƙunci tana baƙin ciki, kwanan ƴar uku ita ma ta mutu.