Sashe 73
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Barira ta ce "Ba wani sharri baba uwani, mu ba butulu ne irinki ba, idan baki yi wasa ba, an ƙulla miki kyakykyawan tarko kema, kamar yadda ake haɗa baki da ke, ake cin dudduniyar giwa".
"In ji uban wa? Waye ya haÉ—a bakin da ni?".
Asiya ta ce "Oho, a juri zuwa rafi da tulu...".
Barira ta ce "Wataran zai fashe".
Ruma kuwa daÉ—i take ji, ta san tana daf da tonawa baba Uwani asiri. Ta shiga kitchen ta duba fridge, taga takawa ya kawo kaji, amma bai gaya mata ba. Ga kayan miya duk ya ajiye bai gaya mata ba, balle ta yi aikin su.
Tana aikin tana mita, ya zo ya tarar da ita a kitchen.
"To uwar ƙorafi, menene kuma?".
"To ba kaine ka kawo aiki ba, kuma ba ka gaya mini ba".
Ya ce "No, su Aisya na ce idan sun gama aiki, su zo su gyara miki, sai ki É—ibi naki, ki basu na gida".
Rumaisa ta ce "Saboda ni ban iya aiki ba ko? To Wallahi ina ƴar ƙaramata, na iya gyara nama, ko kaza ko kofi, ni fa tun ina shekara uku mama ta ce nake kuka, a bani ɓare maggi, da daka, na iya aiki sosai da kake ganina".
"To Allah ya baki haƙuri, idan kin gama, ki dafawa mama wani abun, ko mu saya a waje, mu je ki gaishe ta, dan ni ina zuwa mu gaisa".
Tsalle tayi a kitchen É—in "Yeeee, zan ga mama, amma shine ka yi mini wayo, ka ke zauwa kai kaÉ—ai?".
"Eh, ai da yake maman tawa ce, ba taki ba, kuma a kyauta zan kai ki ba, da sharaÉ—i".
Cikin mamaki ta ce "SharaÉ—i kuma?"
"Eh sharaÉ—i mana.
Ta ce "Na me?"
"Kiss zamu yi"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Kiss, iskanci fa kenan".
Ko a jikinsa ya ce "Eh, shi zamu yi".
"Taɓ wallahi a'a, ƙazantar?"
Matsawa ya yi kusa da ita, ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai tata, ta rintse ido ta kame jikinta.
Ya ce "Wai ke haryanzu kamar robot ki ke, ba kya jin komai ne?"
Ta sake kawar da kanta gefe, tana rintse ido.
Ya rungumota a jikinsa, ya kai fuskarsa tata.
"Wallahi idan ka yi mini zan yi ihu, kuma ma ba kullum nake yin brush ba, bakina wari yake" ba ƙaramar dariya ta bashi ba, gaba ɗaya ta tsorata sosai.
Ya girgiza kai ya ce "Ki yi girki mu tafi da shi, idan an yi sallar magariba zamu tafi" yana fita, tayi ajiyar zuciya, tana ta sauke numfashi.
***
Iman ce zaune a gaban Ammi, ta tattara mata hankalinta, jin ta ce mata, akwai maganar da take son su yi mai muhimmancin.
Ammi ta ce "Iman, Jabir ne yazo mini da wata magana, wai yana sonki, kuma nan kusa yake son ayi komai a gama, baki ji daÉ—in da na ji ba, kin ga shi na gida ne, kuma ya san duk halin da ake ciki"
Ras! Gaban Iman ya faÉ—i, mussaman ganin yadda ammi ke murna da al'amarin.
"Ya ki ka yi shiru, ba ki ce komai ba?"
Iman ta ce "Ammi tsoro nake ji, kin san mamansa ba za ta amince ba"
Ammi ta ce "Iman addu'a zamu yi, Allah ya sa ta amince ya shige mana gaba, na san babu yadda za ayi"
Jiki a sanyaye Iman ta ce "To Ammi" daga haka ta tashi ta tafi É—akinta, ammi ta nuna goyon bayanta a kan lamarin, gashi ita ko kaÉ—an, ba ta ra'ayin Jabir, hasali ma zuciyarta na tare da wani daban, da bai san tana yi ba.
Mai sunan baba yana É—akinsu yana cin abinci, yana jiyo tsalle-tsallen ruma a tsakar gida, takawa kuma yana tare da mama suna hira.
Haka kurum ya ji gabansa ya faÉ—i, har sai da ya ji tamkar abincin da ya haÉ—iya ba zai wuce ba.
A take tunaninsa ya kai kan iman, ya janyo wayarsa, ya shiga What's app É—in sa, sai dai ba ta online, to idan tana online ma me zai ce mata?.
Ya taso ya fito tsakar gida, rumaisa ta zauna ta saka Yasir a gaba, suna magana ƙasa-ƙasa.
"Yasir, kai ka san ta kan waya, na san kai gwani ne, hacker ne kai, hacking nake so ka yi mini"
Ya harareta ya ce "Ni ne hacker?"
"Yi haƙuri, wani abu zaka yi mini, wayarka zaka ara mini, zan haɗaka da wanda zaku yi aikin tare, sirri muke so".
"Ke, bana son iskancin banza, haka kurum ki ja mini masifa, ke idan kin nemo magana mijinki zai fitar da ke, ni kuwa fa?"
Ruma ta ce "Ba irin wannan aikin bane, yaya usy ya san komai, tare muke shawara ma, papa zaku tayani mu taimakawa, amma bana son ya san halin da ake ciki, bari ya usy ya dawo, zan baka lambar Mahmud ɗin, ƙanin mijina ne" gyaran murya suka ji a bayansu. Ruma ta waiwaya taga mai sunan baba a tsaye.
Da sauri ta tashi ta ce "Laa mai sunan baba ina wuni, ban san kana nan ba ai"
Alama yayi mata da ta je, ta ƙarasa zuwa cikin ɗakinsu, ya kalleta ya ce "Ina yarinyar nan, ta warke?"
Cikin rashin fahimta ta ce "Wace yarinyar?"
"Ƙanwar mijinki?"
Ruma ta ce "Auu, Anty Iman, dama ba ta da lafiya ne?".
Ya ce "Never mind, je ki kawai".
"Tana lafiya ƙalau, shekaranjiya ma mun je gidan, kusan kullum idan muka je, sai ta ce mini ina yaya Umar, ko ta bani wayarta ta ce....
"Fita ki bani wuri" ya katseta, saboda yadda ta fara zuba.
Sum-sum ta fice, ya nemi wuri ya zauna, yana tuhumar kansa meye ma na tambayar rumaisa.
Tamkar mata, haka suka din ga shewa da Usman ya dawo, ta baje musu abincin da ta zo da shi, ta haÉ—u a cikinsu, suna ci.
Idan da sabo, takawa ya riga ya saba, dan haka ba ya damuwa ma yanzu, ya riga ya fuskanci irin alaƙar da ke tsakanin su, shiyasa a rashin su, take sauke masa duk wani kwandon rashin ji da take yi musu.
Sai ƙarfe goma suka bar gidan, suka tafi gida.
***
"Jamila ina cikin damuwa, wai ni Jabir zai tunkara, ba tsoro ba kunya wai yana so in bashi dama ya auri Æ´ar da giwa ta tsinto iman?"
Mummy ta ce "Ni na san wannan maganar tuni, ba wannan ne ya dameni ba, lamari ya fara jagulewa, na fuskanci kamar aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"
Cikin mamaki ta kalli Mummy ta ce "Kin sani fa ki ka ce? Amma baki gaya mini ba"
"Ban zaci abun har zai kai haka ba, ban É—auka da gaske zai yi maganar aure ba, amma na san ba wata matsala ba ce ba, zaki iya jajircewa a kan hana faruwar hakan".
"Lallai ma jamila, ke kin fi kowa sanin, ba zan haɗa alaƙa da giwa ba, ya auri ƴar ta idan Allah ya sa ya samu sarauta, su mallake mini ɗa?"
"Lubabatu naki fa mai sauƙi ne, nifa abubuwa sun fara sakwarkwacewa, dole a nemo sabon boka, duk da na bayar da aikin da aka bani na ƙarshen nan, amma dole na nemi abun yi, akwai matsala".
Hajiya Lubabatu ta ce "Kin ga ni yanzu bana gane komai, sai anjima ma yi magana daga baya kawai"
Mummy ta ce "Dole in motsa in sauya taku, ban taɓa samun matsala a abubuwan da nake ba sai a wannan karon, saboda zuwan wannan matsiyaciyar yarinyar, ƴar wannan abar daga zuwanta za ta hargitsa komai, Allah ya sa uwani ta yi abun da na sakata, yadda yakamata".
Wayar Mummy ta fara ringing, ta duba taga baba Uwani ce, ta É—aga ta ce "Ya aka yi?".
Cikin kuka baba uwani ta ce "Ina cikin bala'i ranki ya daÉ—e, yarinyar nan wai ashe tana sane ta ce kina yi wa takawa asiri, dan ta gane idan ina kai miki maganar giwa, wallahi a sashinki ma akwai munafukinta, wallahi yarinyar nan ba yarinya ba ce aljana ce ranki ya daÉ—e, dan Allah kiyi wani abu a kai".
A fusace Mummy ta ce 'Kuma ki ka samu ƙwarin gwiwar kirana ki gaya mini wannan shirmen? Yayi miki kyau, ki mayar da hankali ki yi mini aikin da na saka ki, na san matakin da zan ɗauka a kanki"
"Na shiga uku, hajiya wani irin mataki?" Katse wayar Mummy ta yi, ta jefar a kan gado ta ce "Aikin banza"
**
Kamar kullum takawa ya je gaida ammi, ya tarar da kaya a ɗakinta, har da ƙaramin keke na yara.
Ya ce "Ammi, wannan kayan fa?"
"Mahmud ne ya saya wa takwaransa"
Har zai yi magana, da ya kalli fuskar ammi sai ya fasa.
Ammi ta ce "Yauwwa, ban gaya maka wani abun arziki ba".
"Wane abun arzikin?".
"Ina ranar da jabir ya zo, muka fita ka ke tambayata fara'ar me nake yi?"
Ya jinjina kai alamar ya tuna.
"Wata magana ya zo mini da ita, da ta faranta mini rai"
"Maganar me kenan?"
"Cewa yayi ya na son Iman, kuma aurenta zai yi"
Adam ya yi Jimmmm sannan ya ce "Yaushe kuma ya fara sonta?"
Ammi ta ce "Ban sani ba, ya ce mini dai zai je ya lallaɓa hajiya Lubabatu, ba ka ji daɗin da na ji ba, idan ta amince ai na ji daɗi, tun da ɗan gida ne, kuma na yaba da shi, jabir ɗa ne a wurina"
Adam jinjina kai kawai yayi, ya tashi ya ce "Bari na je wurin aiki, ina da idan na taso zan biyo, sai na dawo"
Ammi ta ce "Allah ya tsare".
Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaÉ—in da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba.