Sashe 62
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su" ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ƙaramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa"
A harabar gidan mai sunan baba suka haÉ—u da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba.
Mahmud ya ce "Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da alaƙa da rumaisa ko?".
Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce "Eh ƙanwata ce".
"Kamannin na gani ai, sunana Mahmud"
Mai sunan baba ya ce "Babban suna, ni kuma umar"
Mahmud ya ce "Masha Allah, ka gaida gida, a gaida mama, duk ina jin sunanku a bakin Æ´a ta, bari na zo na sauke ka a hanya, fita zan yi" Umar ya jinjina kai, dan gaba É—aya ya ji Mahmud ya burge shi, mussaman yadda ya yi masa magana kamar sun saba.
A É—aki rumaisa ta tarar da iman, ta na kuka.
Ruma ta ce "Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir É—in nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?".
Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raÉ—au, kamar shi ya raÉ—a mata.
Ruma ta ce "Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy"
Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba".
Ruma ta ce "Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wulaƙanci ba, amma cika mini alƙawarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ƴar tsintuwa?".
Iman ta É—an yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata.
***
ASALIN LABARI.....
1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi.
Masarautar kano na É—aya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta.
Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al'ummarsa.
Ya na da tarin dukiya, Æ´aÆ´a, barori da sauran hadimai.
Yana da tarin ƴaƴa, daga matansa da kuma ƙwarƙwarorin sa.
A wannan lokacin, ya na kimanin ƴaƴa goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ƙaunar ɗan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya ɓoyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran.
A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu.
Galibi ƴaƴan sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ƙallafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su.
Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban É—aki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban É—aki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya É—auketa ita ma.
Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ƙasar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da ɗan sa, Sharif ya ƙallafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban ɗaki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince.
Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ƙanƙanin yaro kamar Sharif a wannan lokacin.
Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daɗin zaman ƙasar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaɗaici, a cewarsa.
Da ƙyar mai martaba ya saka aka dawo masa da Sharif, sai dai da ya dawo duk ya yasar da wasu al'adun, harkar gabansa ce kawai ta dame shi.
Ko zaman fada ba ya zuwa, idan ya shilla ya tafi na sa yawon, sai an ganshi.
Hakan ya fara damun mai martaba, ya fara tunanin yi wa Sharif sarauta, ko zai nutsu, sai dai ya na cikin yaransa ƙanana.
Sharif ya tsiri cewa zai tafi master's gombe, nan ma sai da aka kai ruwa rana, mai martaba ya ce ya na da sharaɗi, abokin sa wazirin daura, ya bashi ƙanwar matarsa ya aura wa ɗaya daga cikin ƴaƴansa dan ƙarfafa zumunci, dan haka ya ce Sharif ne zai aure ta.
Sharif da fari ya ce "Shi ba ya son ta, daga baya saboda yana so karatu, ya amince, amma sai ya gama master's ɗin sa, mai martaba ya ce bai yadda ba, lokacin ya yi tsayi, wazirin daura ya ce a saka shekara, ba damuwa kan nan ta ƙara girma ita ma.
Ko da Sharif ya tafi gombe, ya samu abokai ya cigaba da rayuwarsa, yadda yake so, duk da mai martaba ya na turowa, ana saka masa ido a kan sa, duk da akwai manyan mutane da suke bibiyar sharif, saboda karamci ga mahaifinsa.
ÆŠalibai ba kowa ya san Sharif ba, yayi ta kashe musu kuÉ—i, suna bin sa, har sabon babur ya saya, yake yawonsa a garin gombe.
Ana haka yawo ya kai shi wani ɗan ƙaramin gari, nesa da cikin gari kaɗan, ya kusa buge wata yarinya, ya yi ta bata haƙuri, ya kafe babur ɗin sa ya rakata gida.
Tun da ya haÉ—u da yarinyar nan ya samu wurin zuwa, kusan kullum suna tare, ita kuma a lokacin yarinya ce sosai, yadda yake biye mata suna shirme, yake bin ta gona ya sanya ta saba da shi sosai.
Sunanta Bintu, Æ´ar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri.
Babanta ya na ƙaunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma'a, a titi suke haɗuwa da Sharif, ya ɗauke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar ƴar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata.
Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata faÉ—a, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida.
Yayyen Bintu suka kore shi, amma yaƙi tafiya, sai da ya haɗu da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana.
Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif.
Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa.
Mai martaba da fari ransa ya ɓaci, mai babban ɗaki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka.
Matan mai martaba suka din ga ƙanan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa.
Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta.
Mai martaba ya ji daÉ—in bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta.
Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar É—an sarki daga kano, zai auri Æ´ar talaka.
Aka yi shagali sosai, aka yi auren.
Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba.
Mai martaba ya tura mutane, da ban haƙuri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila.
Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif.
Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata ƙawa.
Wasa² sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan.
Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da naÉ—in Sharif a matsayin Galadima.
Ƴaƴan mai martaba da matansa, suka ɗaga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa.
Mai martaba ya yi burus, kuma bayan naÉ—in sarauta, aka É—aura masa aure da Jamila.
Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar. Jamila ta ƙudiri aniyar, ɗaukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu.
Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban É—aki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa.
Hakan ya ja mata baƙin jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "Ƴa ta bintu".
Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.
Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.