Sashe 87
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina dai yi wa mutane marasa kirki, kuma wallahi ba zan bari ka auri iman ba in sha Allah, yayana zata aura yaya Umar ba, kuma zaka gani, idan kana da zuciya ka canza hali, ka fara zuwa ka kula da mahaifinka, kan ka yi tunanin auren iman"
Ba ƙaramin zafi maganganunta, suka yi
Ya risuna ya gaida ammi, suka gaisa yace mata wurin iman ya zo, ammi ta ce masa iman tana bacci, likita ya ce a bari ta samu hutu.
Ko da jabir ya tafi, rumaisa ta din ga ziga ammi, tare da nanata mata idan har jabir bai tausayawa mahaifinsa yayi jinyarsa ba, tayaya zai tsaya ya kula da iman da ciwonta?.
Daɗin daɗawa ga masifa da tijarar mahaifiyarsa, da take iƙirarin cewa ba za a auro mata wadda ba ta da asali ba.
Kasancewar rumaisa tayi sara a kan gaɓa, domin zuciiyar ammi ta fara kaiwa da komowa a kan batun, ya sanya ta ji ita ma ta gamsu da maganar rumaisa.
Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara É—an sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaÉ—an.
Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta É—an ja shi da hira.
Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan riƙe mata shi, gaba ɗaya mai sunan baba mu'amala da shi sai mai haƙurin gaske, miskili ne na bugawa a jarida.
Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da Æ´ar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaÉ—e Saboda rumaisa.
Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne.
Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu.
Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki?
Mahmud ya ce "Wace mai jikin?"
"Ƙanwarka mana, khadija" sai da Mahmud ya ɗan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne.
Ya ce "Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai".
Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba.
Mahmud ya ce "Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sauƙi, dan na ganta ɗazu tare da daughter na a garden".
Mai sunan baba ya ce "Ina so mu yi magana ne, ban taɓa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau ɗaya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai"
Mahmud ya ce "Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya".
Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce "Ina shirin kiranka"
Ya ce "Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba ɗaya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition ɗin da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ƙara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu"
Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta roƙi ya auri iman.
Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ƙalubalen rayuwa, a wannan gaɓar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu a kan lamarin, dan jin kunnensa ya ji jabir ɗin na gayawa mummy, wambai ya san maganar, turaki zaa kaiwa kuɗin auren.
Bai gama tunanin ba ya ji muryar mai sunan baba ya ce "Ban taɓa neman alfarma ayi wa wani abu ba, a karon farko na roƙe ka, ko dan lafiyarta"
Mahmud ya ce "Kar ka damu, zan san abun da zan yi a kan lamarin in sha Allah".
"Masha Allah na gode sosai"
Mahmud yayi shiru yana kallon wayarsa, ya nunfasa ya ce "Allah ya sa rabonka ce Malam Umar, ni na yaba da dattakunka"
***
Laila ce suke waya da takawa, tana gaya masa ruma ta ishe ta da rashin ji, ita da É—an ta, yana ta dariya mussaman da ta ce wai ruma ta zana mata aljani ta ajiye a É—aki, wai hoton takawa.
"Anty laila bani shi mu yi magana" ruma tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar wayar.
Laila ta ce "Ungo ku ƙarata, ban da video call dai, bari na shiga wanka".
Ya ce "Budurwar"
"Mmm saurayin, ya garin? Ya karatu?".
"Alhamdilillah, ya naki karatun, na ji anty laila ta ce tana yi miki lesson, kun kusa fara exams, dan Allah a dage a mayar da hankali"
"To in sha Allah, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"
"Meyasa kuma?"
"Ba karatu kawai ake koya mana ba, sai a din ga faÉ—ar wasu maganganu"
Tun da ta faɗi haka ya san akwai ƙura, ya ce "Wasu maganganun kenan?"
"Wai se malamar ta din ga tsayar da mu, wai za ayi lecture, ka ji abun da take cewa kuwa?, wai a din ga saka ƙanan kaya ana karairaya sai ka ce wasu karuwai, yanzu dan Allah ya dace a zaunar da mutane ana gaya musu haka?"
Da ƙyar ya iya gimtse dariyarsa ya ce "Ke ya aka yi ki ka san karuwan ne suke haka?"
"Ai in gaya maka, da akwai wani gida a unguwarmu, sai matan su dinga saka riga da wando, ko mini skirt, suna yawo, aka koresu, na ji ana cewa gidan karuwai ne, har da vest fa suke fitowa waje ana kallonsu, na zo ina bada labari a gida, mai sunan baba ya sakani kama kunne, aka ce mini kar in kuskura abun da suke yi ya burgeni, idan mutum yayi irin wannan ba ga muharraminsa ba É—an wuta ne. Ni fa wani abun ba zan iya faÉ—a ba ne, wallahi ni duk mutuncin malamr ya zube a idona ma, ni kuwa da ta fara nake tashi na tafi.
Da fa sun rainani ba su zata ina da miji ba, sai da malama ta ce musu ni matar aure ce, wai wata ta ce mini, wai zan sai maganin mata? Na ce mata ni ban san shi ba, dan Allah a chemist ana ware maganin maza da na mata?"
Ya ce "A'a"
"To a in gaya maka, na ce mata ni idan bani da lafiya asibiti ake kaini, kawai ta nuna mini Wasu ƙulle-ƙulle da robobi mai hoton ƴan iska a jiki, Wai in saya, na rufe idona na ce a'uzubil'ahi, gaskiya ni dai a cireni daga makarantar nan"
Maimakon ta ji ransa ya ɓaci kawai sai ya din ga tuntsura dariya, har da tari, laila ta ƙarasa ta ƙwace wayar, ta ce "Ke dai ban taɓa ganin yarinya mara kan gado kamar ki ba? Wai ke baki da ƙawaye ne?"
"Nifa ƙawata ɗaya habiba, ko nayi ƙawaye mama korarsu take yi, kuma ko ba ta kore su ba, idan muka yi faɗa duka nake yi musu sai mu ɓata"
"Aikuwa wannan karatun, dole na zauna na ɗora miki shi, idan kin ƙi ganewa kuma shi idan ya dawo ya karanta miki yadda zaki fuskanta. Haba ke gaba ɗaya abaibai ce ba kya gane komai kenan".
"Anty laila ki daina hantarata, zamu yi faÉ—a"
"To muyi faÉ—an mana, ke zaki yi wa kanki ai".
Rumaisa ta kalleta ta ce "Saboda zaki daina sai mini garin kunun sabayar maman Khadija ko? Ba ita ce a zariya ba lambarta 0703777 7442. Sai maman Ilham mai magani ba da ke cikin garin kaduna kawo road ba, lambarta 08135613021, na riƙe komai tsaf a kaina saboda irin haka".
Laila ta ce "Iko sai Allah, ke yanzu zaman hadda ki ka yi kenan?"
"Ai Anty laila ba komai ake faÉ—a mini ba, in dai an yi abu a gabana, tsaf nake haddace komai tas a kan nan nawa".
"To kin kyauta, tashi ki je kitchen ki haÉ—a mana kayan aiki, yanzu zan zo ki gwada mini girkin da na koya miki, in gani idan da gaske kina haddace komai É—in"
Rumaisa ta tashi ta ce "Yanzu kuwa".
***
Iman duk ta kuma zama so silent, ba babban abun da yake sanyata farinciki, irin ƙoƙarin jan mai sunan baba da hira, da safe ta gaishe shi, daga nan yayi mata ya jiki. Mutum ne miskilin gaske, tana shan fama, amma wasu lokutan ya kan saki jiki, mussman idan tana yi masa hirar karatun addini.
Wani irin matsanancin tausayinta yake ji, da ya tuna Jabir, sai gabansa ya faÉ—i, ya san duk wani kauce-kaucensa son iman yake yi, gashi shi bai san ta ina yakamata ya fara ba, bai san meya kamata yayi mata ta din ga farinciki ba, saboda shi ya saba da bosy life, ba wasa.
Rumaisa ce a tsaye a banɗaki za ta yi wanka, tana ƙarewa kanta kallo a mudubin banɗaki, har da tsalle tana ɗan juyi, ganin abun arziki ya fara fitowa, yana cika.
"Wayyo daɗi kasheni, zan wuce gori da wulaƙanci, na ga me sake ce mini ƙwaila, kai za a ga jan aji idan suka ƙara girma, wayyo ni maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni yasin"
Ta gama wankanta, ta fito ta shafa mayukan gyaran fata, ta saka kaya, ta kuma tsayawa tana kallon mudubi, ta ce "Hmmm, na ga wanda zai sake ce mini ƙwaila, mu haurata da shi, har shi papan, yanzu dai sun fi ƙarfin murfin jarkar faro"
Ta É—aga kai ta kalli zanenta, da take kansile date kullum, na kwanakin da ya rage ya dawo.
A hankali ta furta "Lokaci baya sauri".