← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 124

Sashe 72

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya daki tebur da ƙarfin gaske ya ce "Kuma ina yi maka rantsuwa da Allah, idan wani abu ya samu matata, sai dai ayi mutuwar kasko da ni da kai, ka je ka cigaba da bincike a kaina, amma idan har zaka bibiyi matata ita za ta gaya maka abun da ya faru, ka shirya cewa watan faɗuwarka ya tsaya, dan tana da ƙwaƙwalwa fiye da lissafinka, kuma gaskiya ta faɗa, a da baku damu da ita ba, kun cutar da ita meye na tayar da jijiyoyin wuya a yanzu? Idan ka matsa za ta saka ka a sarƙa, kuma muddin ka faɗo cikin suspect ɗina, aikina zai bi ta kan ka"

Ayshercool
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

A rikice Jamil ya kalli takawa ya ce "Kana nufin ni ne ke da alhakin yin garkuwa da aisha, kai ba a zargeka ba sai ni?"

Adam ya ce "Ni dama a can a cikin zargi nake, ban ce kai kayi garkuwa da aisha ba, amma abun da ka yi ya jefa ka cikin zargi, madalla da yarinya mai kaifin tunani kamar rumaisa" yana gama maganar ya fice daga office É—in.

Wani irin gumi Jamil ya yakice, yana wani irin huci.

"Da ni ka ke zancen Adam, zaka gane ba ka da wayo, daga kai har wannan shegiyar yarinyar mai ƙulla mini jakar tsaba, saboda kaji su bini".

A daren jiya kuwa, Mahmud yawonsa ya din ga yi da Sabir, har da zuwa yawon ciye-ciye, ya sayawa Sabir kaya ba kaɗan ba, soyayyar da  yakamata ya ji game da ɗan uwansa Adam, shi yake ji a Sabir, koma ya ce fiye .

Ammi tana nan tana dakon dawowarsu, Nusaiba da Iman ma, duk suna tare da ammi, suna jiran dawowar Mahmud.

Wajen ƙarfe tara da rabi, sai ga Mahmud, sidi ya biyo shi, da uban faggon kaya niƙi-niƙi, zuwa shashin Ammi, da da yake ji kamar wata baƙuwar duniya, amma yanzu the more yake shiga, the more yake zama familiar da wurin.

Mahmud ya nuna masa wuri ya ajiye kayan, ba tare da ya kula kowa ba, ya ƙarasa kan kujera, ya kwantar da Sabir da yake bacci, ya durƙusa a gabansa yana ta shafa gashinsa, kamar ya tafi da shi, ya kwana a wurinsa.
Ya miƙe a hankali ya juya zai fita, Ammi ta ce "Wannan kayan fa?".

"Nasa ne" ya faɗa a taƙaice ya fice.

A sashin Mummy ya tarar da Mummy ta rako Samha, tana ta rarrashinta, idonta yayi jawur, alamar ta sha kuka, ya san ba zai wuce ta gaya mata saƙon Adam ne ba, shiyasa take wannan kukan.

Sai da Mummy ta rakata har mota, sannan ta koma sashinta.

"Ina ka je ne? Tun sallar magariba baka dawo ba, baka kirani ba kuma, na san baka yawo da daddare".

"Na fita da Sabir ne"

A É—an razane ta ce "Waye Sabir?"

"ÆŠan mu da Adam ya haifa"

"Au yanzu dan rashin zuciya, har É—an sa ka je ka É—auka kana yawo da shi? Wurin giwar ka je kenan?".

"Sirikarta na saka ta ɗaukko mini shi, ina ƙaunar yaron nan sosai da sosai"

Mummy a ranta ta ce "Lallai tsuguno ba ta ƙare mini ba, akwai sauran rina a kaba, aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"

Ya ce "Mummy, ya dai na ganki wani iri, akwai damuwa ne?".

"Damuwa akwaita Mahmud, ban gane maka bane kwana biyun nan, ka san dai a duniya bamu da maƙiya sama da giwa da Adam, yanzu kuma naga kamar alaƙa ce tsakanin ka da matarsa, ko ka san yarinyar nan cewa ta yi wai ina yi wa Adam asiri?"

A ransa ya ce "Tom, hasashena ya tabbata, matar nan ta faÉ—a tarkonmu"

"Na gaji da wannan rashin albarkar, nan ya zo ya gama yi mini rashin mutunci, a gabana ya ci mutuncin Æ´aÆ´ana, saboda wannan hatsabibibiyar yarinyar, kuma ta ce wai ina yi masa asiri, a gidan ubanta ta ga asirin, zai maimaita a gaban mai girma wambai, dole ayi mini iyaka da ita".

Cikin ko in kula Mahmud ya ce "Amma dai idan ki ka kai ƙarar wannan Yarinyar, za ace girma ya faɗi, raƙumi da shanye ruwan ƴan tsaki".

"Ba ita zan kai ƙara ba, shi Adam ɗin ita a wa, ina ruwana da ita, amma dole ayi mini iyaka da su".

***
Daf da la'asar, rumaisa ta shiga É—akin takawa, tana dudduba abun da za ta gyara.

Daga toilet ta ji ya ce "Waye a nan?"

Ta amsa masa da "Ni ce nan"

"Rumaisa duba drowern mirror, ki bani shaver".

Ta yamutsa fuska ta ce "Rumaisa kuma?"

Ya ce "Eh"

"Ba cewa ka yi mimi zaka din ga ce mini ba?"

"Anƙi ace mimin, miƙo mini da sauri"

Ta ɗaukko shaver ɗaya, ta tsaya a ƙofar banɗakin ta ce "To shigowa zan yi?".

Ya ce "Eh miƙo mini"

"Au kai ba ka jin kunya, to ni ba zan shigo ba, zuro hannu ka karɓa".

Ya ce "To ai ba tsirara nake ba, miƙo mini abu nake yi"
Ta tura ƙofar a hankali, ta ɗan leƙa, yana tsaye a gaban mudubin toilet ɗin, ya shafa wani cream a fuskarsa, da wata shaver a gabansa, ga wani towel ɗin a wuyansa.

Duk da haka sai ta ji wani iri, ta ƙarasa a hankali, ta tsaya tana kallonsa.

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ya dai?"

"Bakomai, so nake naga me ake yi da shaver"

Ya É—an waro ido ya ce "Baki san me ake yi da ita ba?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ba kya aski kenan?"

Rumaisa ta ce "Ni namiji ce da zan yi aske kaina"

Ya girgiza kai ya kerɓi shavern ya ce "To tsaya ki ga me ake askewa da ita".

Aikuwa ta tsaya, ta zuba masa ido.

Ya kammala gyaran fuskarsa da ita, sannan ya É—ebo cream a wata container, ya shafa a hammatarsa da ta fara fitar da gashi, ba sosai ba.

A hankali ya sanya shaver yana cire gashin. Ta ce "Innalillahi, dama abun da ake yi kenan, to ni ya aka yi bani da shi, sai yaushe zai fito mini?"

Ya ce "Da gaske baki da shi?"

Rumaisa ta ce "Bai fito mini ba, kuma ina so, in ga ya fito mini da yawa, idan na É—aga hannuna a din ga gano shi".

Adam ya ce "Saboda ƙazama ce ke? Waye yake ado da gashin hammata, ƙazanta ne to"

"Eh, amma dai ina son ya fito mini"

"Duk ranar da ya fito, ki ka bar shi, ni da ke ne, idan kin ga ya fara fitowa ya taru, ki yi mini magana in sake koya miki yadda zaki aske shi. Amma gashin hannta ba abun so bane, ba abun ado bane. I even wonder kin fara period but still a child"

Rumaisa ta ce "To ni dai Allah ya sa ya fito da wuri, sai ka sai mini shavern nima ko?".

Ya ce "To, jeki zan aske É—ayan"

"Me?".

"Gashin" ya bata amsa kai tsaye.

"A ina yake shi kuma, ko na ƙafarka, ga hannunka ma"

"A'a towel ɗin ƙuguna zan kwance, nan ma akwai wani, shima ba a barinsa cirewa ake yi, idan ba haka ba mutum ya din ga wari, idan ya fito shima ki gaya mini a sayo shavern, sai in koya miki"

Yatsunta ta saka, ta toshe kunnunwata ta bar toilet É—in, saboda ta daina jin abun da yake faÉ—a, a tunaninta ai wannan abun kunya ne.

Ta fice daga ɗakin sa, ta sauka ƙasan bene.

Asiya da barira, suna ta yi mata sannu da gida, ta amsa musu tana gaishe su, sai dai ta lura da yadda baba Uwani ke ta wani kumbura fuska.

Ruma ta ce "Baba uwani, me nayi miki ne?"

Ta kalleta ta ce "Hmm tambayata ma ki ke yi?"

"Papa yayi mini faɗa, ya ce kar na sake ai, ranar ma dan raina a ɓace yake ne".

Asiya ta ce "Ranki ya daɗe, wata jita-jita na jiyo, da na je karɓo miki saƙo a wurin Ammi".

Ruma ta ce "Wace jita-jitar kuma?".

"Wai saƙo ya iske cewa, kin ce hajiya jamila, babar Yallaɓai Mahmud, wai tana  yi wa maigida takawa asiri"

Rumaisa na jin haka, ta san mahmud ne ya bayar da wannan saƙon, yana nufin baba uwani ta kai tsegumin, kuma shi ya saka ta faɗa a gaban baba uwani.

Rumaisa ta waro ido ta ce "Ni ɗin, waye ya faɗa? Ni harkar wa ma na shiga balle na faɗi wannan maganar?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya babu munafuki a sashin ammi? Idan ma na faɗa, ai ba a gaban wasu bare na faɗa ba, balle ma ban faɗa ba. Amma ai ba ƙarya nayi ba, idan ma na faɗa, idan ta san ba ta yi, ai ba zata tsargu ba, idan kuma yin take, A'uzu bi kalaimatillahi tammat.

Tsuru-tsuru baba uwani tayi, tana ta yaƙe baki ta ce "Ai uwar ɗakina, asirin ma ba za a rasa yi ba, saboda abu ne na gidan sarauta, kowa kansa kawai ya sani, galibi ba Allah a ransu"

Ruma ta ce "Yauwwa, Aisya kin ji ko, barira ma kin ji, ga baba uwani ma ta faÉ—a, mummy na yi wa takawa asiri, ashe bani kaÉ—ai na fuskanci hakan ba".
A rikice baba uwani ta ce "Ba haka nake nufi ba, ki yi wa Allah da ma'aiki kar ki ƙulla mini sharri".

"Ba sharri bane, ai ke ki ka faÉ—a"

Rumaisa ta nufi hanyar satairs, cikin tashin hankali, da mamakin yadda jikar cikinta, take yi mata wayo, ta bi bayan rumaisa. Ruma ta tsaya ta waiwayo ta ce "Idan ki ka biyoni sai na gaya masa" ta juya ta cigaba da hawa.

Ta koma a sukwane kitchen, ta ce "Aisya, da ku za a haɗu a ƙulla mini sharri ko?"
Chapter 72 · 0% Book details