← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 124

Sashe 85

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da rumaisa ke daf da shiga sashin ammi, taga laila ta fito da sauri, ta yi wa sidi magana, akan ya kawo mota, zasu tafi asibiti iman ta suma.

Da gudu ruma ta shiga sashin ammin, iman na kwance a in da ta barta É—azu tana bacci, ashe daga haka ta suma, ammi na ta magana amma shiru.

A gaggauce suka É—auketa, tuni ammi zuciyarta ta karaya, saboda yadda jikin iman ya saki, kuma Ammi ta É—ora alhakin hakan a kan hajiya Lubabatu, da ta zo ta yi mata wannan cin mutuncin.

Ammi ta ce Rumaisa da Nusaiba su zauna a gida, ita da laila suka tafi kai iman asibiti.

Rumaisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, lokaci lokaci ta din ga jan uban tsaki ta ce "Allah ya tsinewa babar jabir É—in nan, da bata san darajar É—an Adam ba, daga ita har shi wawan jabir É—in, mara zuciya"

Nusaiba ta ce "Ya zaki din ga zaginsa, shikuma me yayi miki?"

"Ba ruwanki da ni, ai naga take-takenki, ke kike goya masa baya, ke ki aure shi mana" duk da Nusaiba ta girmi rumaisa sosai, dan ta girmi iman ma, amma haka tayi shiru ta kasa magana.

Sai dare laila ta dawo, suka tashi gaba É—aya suna tambayar laila ya jikin iman É—in.

Laila jiki a sanyaye ta ce "Da sauƙi, sai dai jini ya hau, zuciyar ta kumbura, amma ta farfaɗo ta samu bacci."

Ruma ta ce "Anty laila dan Allah a fasa auren nan mana, ko dan ceto rayuwarta"

"Ai ni zan fi so yi auren nan, dan nuna mata iyakarta, kuma magana tun da ta riga ta je gaban wambai, rusata ba abu ne mai sauƙi ba, mutumin nan ba ayi masa wasa".

Rumaisa ta rasa abun sa yake yi mata daÉ—i, ji take kamar ita ce a halin da iman take ciki.
Nusaiba ce ta shirya, ta tafi asibitin, dan taya Ammi kwana da iman.

Yau sai ga rumaisa da tashi cikin dare tana sallar dare, tana yi wa iman da yayanta addu'a, idan da alkhairi Allah ya sa mai sunan baba ya auri Iman. Dan ta san mai sunan baba, akwai zafi, amma mutum ne mai kyautatawa da tausayi, kuma ba ta taɓa ganin abun da ya damu da shi sosai bayan ita da mama ba sai iman.

Da gari ya waye, laila da rumaisa suka je duba iman, suka kai musu abinci.

Iman ta farfaÉ—o, amma ta yi pretending, bacci take yi, saboda ba ta son magana, dan numfashinta sama-sama take yin sa.

Ammi da Nusaiba suka koma gida, an yi sa'a ruma da anty laila an É—an fara shiri, sannan laila ta sarawa tsagerancin rumaisa, mussaman jiya, da ga tsigalewa hajiya Lubabatu.

Wayar iman na hannun rumaisa, dan yanzu wayar kamar ta su ce su biyu.

Rumaisa ta kira mama ta ce "Mama dan Allah ki zo ki duba iman, ba ta da lafiya muna asibiti"

Mama a duk lokacin da ta ji an ce iman ba ta da lafiya, hankalinta yana tashi, mussaman da ciwonta yake mai hatsari.

Bayan ta gama wayar ta dubi laila ta ce "Anty laila".

"Na'am".

"Wai yaushe zan yi video call da papa ne?".

Laila ta ce "Sai lokacin da ki ka fara bin umarnina"

"Anty laila dan Allah, so nake na ganshi"

"Kin fiye taurin kai ne, sai lokacin da ki ka fara yarda zaki yi abun da nace miki ba gardama"

"To me ki ke so na yi?"

Ta ce "Ba wannan ba ma, so nake mu bashi mamaki, sai kin fi haka kyau da cika, ke baki ga yadda jikinki ya fara yi ba ne"

Ruma ta ce "Na gani, kullum idan na je wanka ina dubawa, idan sun fara girma".

Laila ta yi dariya ta ce "Ashe dai kina son su fito".

"Wallahi ina so"

"To ki mayar da hankali da cigaba da shan kununki, bayan sabayar maman Khadija ma, akwai maganin maman ilham, shi kuma a iya fito da nono yake aiki, baya sanya ƙiba, haɗinta haɗi ne mai kyau ɗan mambila ita ma.
Rumaisa daga lokacin da mace tayi aure, zama bai ganta ba, shekaruna a ƙalla talatin da huɗu, amma kalleni kamar ƴar ashirin da biyar.
Bana zama, abu ba sai ya lalace ake gyara shi ba, garkuwa ake yi kafin ya faru, nan gaba kina haihuwa kina shayarwa, dole zasu ranƙwafa ko su zube, amma idan ki ka tattala su, ki ka kula da su, tsaf zaki yi ta haife-haifenki, ba tare da kin sirewa miji ba.
Kuma ba ina nufin ki je ki sai abun da baki san menene ba ki sha, ba haka nake nufi ba, duk abun da na baki kiyi amfani da shi, na san kyansa da ingancinsa, kuma na san da me aka yi shi.
Kin ga maman Khadija na ta haɗin kunu ne na sabaya, da yake gyara jiki, ya sanya ƙiba da gyara fata, kuma kowa na iya sha.
Ita kuma maganin maman ilham, akwai matan da suna da ƙiba, basa buƙatar yin ƙibar, gyaran nonon kawai suke so, ita maganinta haɗe-haɗe ne, na natural abubuwa, ba shi da side effect kayanmu ne na islamic da saiwoyi masu kyau, ake kawo mata daga mambila ta haɗa.
Ya ki ke gani, idan mutum ya haÉ—a garin kunun sabayar maman Khadija, da kuma maganin gyaran nono na maman ilham?
Rumaisa ita mace ba ta zama ba gyara, dan haka so nake ki cika kiyi kyau, kan dawowar takawa".

Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Ni fa na zata kawai amfaninsu a shayar da É—a, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su"

Laila ta ce "Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace"

Ruma ta sake gyara zama ta ce "To ita ma na maman ilham É—in zaki sai mini?"

"Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma".

Cikin farinciki ta ce "Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro".

Ƙyalƙyalewa da dariya laila ta yi ta ce "Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haɗin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar".

"Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?"

Laila ta ce "Wannan kuma effort É—inki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa"

*INA MASU SON WUCE GORIN KISHIYA, DA NA MIJI, KAI HAR MA DA NA ƳAN UWANKI MATA, TO KU GARZAYA KU GWADA KUNUN SABAYAR MAMAN KHADIJAH DA KE ZAUNE A ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN ZARIYA 08033411249, KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA*
*HAKA ZALIKA KU HAƊA DA MAGANIN MAMAN ILHAM MAI TULA-TULA, MAGANINTA INGANTACCE NE, WURIN BIYAN BUƘATUNKU, BA TARE DA CUTAR DA LAFIYARKU BA, KU TUNTUƁETA TA LAMBAR WAYARTA 0813 561 3021 TANA NAN A KAWO ROAD KADUNA*
*HAJIYATA KAR KI BARI MATA SU SHA GABANKI, SU RIGAKI MALLAKAR MAGANIN MAMAN ILHAM, DA NA MAMAN KHADIJAH, MACE SAI DA GYARA, SUNA TURA KAYANSU KO INA A FAƊIN A NIGERIA, HAR MA DA ƘASASHEN DA MUKE MAƘWABTAKA DA SU*

Bayan sallar azahar, mama ta je ta duba iman, jikin da sauƙi, amma dai tana jin jiki sosai.
Laila kuwa mama ce ta burgeta, saboda yadda take komai nata a nutse, gashi tun da tazo, rumaisa ke tsokanarta take son sakata magana, saboda kamar kakarta ta mayar da ita.

Mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ya tarar mama bata nan, abun da yafi komai ɓata masa rai kenan, dan haka ko abinci yaƙi ci, ya koma ƙofar gida ya zauna.

Ya kai awa guda da rabi sannan mama ta dawo.

Mama kamar Æ´a da uba, a wajen ta fara yi masa bayani, dan ta san ba shi ba, hatta sauran Æ´aÆ´anta, ba sa son su dawo su ga bata nan, amma na sa yafi yawa.

"Ƙanwar mijin rumaisa aka kwantar a asibiti na je dubata, daga nan na wuce mandawari na sada zumunci da ƴan uwana"

"Wacce daga ciki?"

Mama ta ce "Wadda ka ke tsoratawa mana, iman, ciwonta ne ya tashi, ban ma tarar da hajiyar ba, sai wannan yarinyar, da wata yayar mijin rumaisan".

"To ya jikin nata?"

"Jiki Alhamdilillah, amma dai har na taho bata buÉ—e ido ba"

Mama ta É—an yi shiru tana nazarin mai sunan baba, sannan ta shiga gida.

Mama na shiga gida, umar ya ciro wayarsa ba tunanin komai ya kira wayar Iman.

Sai dai rumaisa ta É—auki wayar.

"Ina me wayar?".

"Mai sunan baba muna asibiti fa, ba ta da lafiya, ba ta tashi ba haryanzu"

Ya katse wayar ya tashi, duk da yunwar da yake ji, ya shiga gida yayi alwalar magariba ya fito.
Ya gama yanke koma menene, yau sai ya je ya ga jikinta, dan gaba É—aya hankalinsa ya tashi.

Bayan kowa ya tafi, ya rage daga iman sai nusaiba, laila ta ce za ta je gida tayi wanka ta dawo, ba sai ammi ta kwana a asibitin ba, su kwana ita da iman da Nusaiba.

Tun kan ya shigo, gabanta ya tsananta faɗuwa, ba tare da ta san dalilin hakan ba, sai dai ba tare da tayi tsammani ba, ta ji an murɗa ƙofar yayi sallama.

Da sauri iman ta fara kiciniyar neman hularta, dan kanta ko ɗan kwali babu, ba ta taɓa zaton mai sunan baba, ko da wasa.

Nusaiba ta ce masa "Ina wuni"

Ya amsa mata a taƙaice kamar yadda ya saba.

Ba tare da fargabar komai ba, ya je gaban gadon, ya zauna a kan kujerar da ke gaban gadon.

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Yaya umar ina wuni"

"Ban ganshi ba" ya bata amsa. Kamar yadda yayi tsammanni, ta É—ago ta kalleshi, ta mayar da kai ta sunkuyar.
Chapter 85 · 0% Book details