← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 124

Sashe 82

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya tafi wata ƙasar, kuna waya ki kashe? Babu wani abu mai jan hankali, ba rausaya murya ba karairaya, wai ce miki aka yi dan kika ƙanwar maza, ki din ga abu kamar namiji, you are not romantic at all, mijinki matashi ne, kuma kema kin san yana da masu son sa, ko dai ki gyara ko ki ga abun da ba kya so. Ki tashi ki yi wanka ki zo ki karya"

Ta ɗau system ɗin ta, ta bar ɗakin, rumaisa ta zumɓura baki sannan ta tashi.

Laila kuwa komawa tayi, tana jinjinawa takawa. "Takawa i salute your effort, Wannan matar taka, zan iya saka bulala in zaneta wataran, she's very stubborn, beside she's much more than how i expect, ba ta ji ga taurin kan tsiya".

Adam ya ce "Haba madam, duk ita kaɗai, ki yi ta haƙuri kema, halinku ne ya zo ɗaya shiyasa ba kwa jituwa, da ɗaya daga cikin ku na da haƙuri, zaku zauna lafiya, idan ku ka saba shikenan".

"Anya zan iya jurewa? Ba ta ji fa"

"Tuba muke, ayi haƙuri dai".

Rumaisa ta shirya cikin dogon hijjabi, hatta jakar islamiyya da litattafai adam ya sai mata komai, sidi ya É—auke ta suka tafi makarantar.

Ya je ya gabatar da ita, mai makarantar ta ce ta san da zuwan rumaisa, aka kai ruma aji.

Mamki ne ya cika su kansu Æ´an ajin, ganinta sanye da hijjabi irin na islamiyyar, suna mamakin kar dai matar aure ce.

Mai makarantar ta gabatar da rumaisa a wurin malamar da take ajin, zungu-zungui ta wuce ta je ta zauna, tana jin haushin kallon da suke yi mata.

Ajin duk manyan mata ne, dan da yawa sun haifeta, wasu kuma sun yi ƙanwa da ita sosai da sosai.

Aka yi lesson ɗin da za ayi a ka gama, har lokacin tashi ba ta kula kowa ba, sai da aka tashi suka din ga tambayarta ko matar aure ce ita, sai dai ta din ga bin su da ido, taƙi magana.

Sidi ya zo ya É—auketa, amma ta ce masa ita É—orayi zai kai ta wurin mama, ya ce ai ammi ba ta sani ba, ruma ta ce ba ruwansa, idan ba zai kaita ba, ya ajiyeta ta je ta hau napep.

Haka ya juya kan motar suka tafi É—orayi.

A ƙofar gidan yara suka tsatstsaya suna kallon uwar motar da aka kawota a ciki, har da maƙwabciyarsu shamsiyya a leƙowa, tana ɗagowa ruma hannu.

Ruma ta ce 'Lallai matar nan, saboda ta ganni a mota, har da É—ago mini hannu, nan gaba a daidaita sahu zan din ga zuwa, in ga ko za samu masu kulani'.

Ta kalli sidi ta ce "Ba sai ka dawo É—aukata ba, zamu yi waya da uncle Mahmud" ta shige cikin gida, bakinta É—auke da sallama.

Gidan shiru, sai Aliyu da yake girki a kitchen.

Ya amsa mata ya ce "Koma bamu san da zuwanki ba, daga tafiyar mijinki jiya, yau kin fara yawo".

Ta ce "Ai da yake ba wurinka na zo ba ehe" ta shiga É—akin mama, mai sunan baba yana kwance a kusa da mama, yana kallon tv.

Mama ta ce "Ke daga ina?".

"Makarantar matan aure wai ya saka aka kai ni, mai sunan baba ina kwana"

"Lafiya ƙalau"

Ba ta tsammaci wata magana sama da haka ba daga gare shi ba dama, dan haka ta zauna ta ce "Mama jiya ya tafi fa".

"Haka Aliyu ya ce mini, ina mai gidan nawa, ina Æ´a ta iman, ki ka zo mini ke kaÉ—ai?"

Mai sunan baba É—an gyarawa yayi, yana jiran jin amsar da rumaisa zata bayar, a kan iman.

"Mama, ni in koma kenan?"

"Gaskiya dai, ba iman ba mai gidana, sai ke fitinanniya"

"Ai shikenan, gara na koma wurin ammi. Sabir yana nan ƙalau, iman kuma gari ba daɗi, tsoro nake ji kar ciwonta ma ya tashi"

A fuskar mai sunan baba ta ga razana, amma saboda azabar miskilanci yayi kamar bai san me suke faÉ—a ba.

Mama ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka, yara ƙanana da ku, har kusa abu ya dameku a rai".

"To ammi kin san familyn na su sai a hankali, sun takura mata da yawa, kin san ba ammi ce ta haifeta ba, sau kusan huɗu ana yinƙurin aurenta, wannan muguwar Mummyn tana hanawa, tana cewa mutane ba ta da uba, wai ammi ce garin tsince-tsincenta ta tsinto ta"

Cikin rashin fahimta mama ta ce "Ke kin sani a duhu, kina nufin ba ita ta haifi iman ba?"

"Hmm mama baki san badaƙalar da ke cikin gidan nan ba" nan ruma ta warware mata komai, sannan ta ce "Yanzu kuma wannan jabir ɗin ya ce son ta yake zai aureta, ammi tana ta murna, tun da shi ya san halin da ake ciki, ita kuma iman ba ta son shi sam, akwai wani wanda take so daban, amma ba za ta iya gayawa ammi ba, saboda ammi ta amince jabir ya nemi auren ta, ba wanda ta gayawa sai ni abun tausayi, kuma tsoro take ji kar wanda take so ɗin, ya ji labarin ga a halin da take ciki ya ce baya son ta".

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, lafiyayyiyar yarinya mai mutunci kamar wannan, babu wanda zai ce ba ita ta haifeta ba, ni cikin yaran nan, da da wanda yake da ƙwari sosai, ai da an auro mini ita, to sai dai ba matar talaka ba ce, ni dai ina ƙaunar yarinyar nan fisabilillahi".

Cikin son sai ta yi pressing ɗin mai sunan baba rumanta sake cewa "Bari kawai ammi, kuma fa baki ga uban samarinta da suke sonta a haka ba, masu kuɗi ta ce ta daina soyayya, kawai ta zo ta fara son wani, amma taƙi gaya mini waye, ba ƙaramin son sa take yi ba. Amma wannan jabir ɗin, ya biyo kai tsaye ta wurin ammi, kuma yana daf da zuwa wurin mai girma wambai, shi kuma wannan wamban ba ɗaga ƙafa, dama yana ta yi wa ammi kashedi, ta aurar da ita ko ta mayar da ita in da ta ɗaukkota, cikin dare ina jin tana ta kuka".

Tsaki mai sunan baba ya yi ya tashi ya bar ɗakin, rumaisa kuwa ta yi wani guntun murmushi, ta tura saƙon yadda yakamata.

Aliyu ya shigo da plate É—in indomie, ya ce "Me aka yi masa na ga ya fita yana tsaki?"

Mama ta ce "Shi wannan sai an yi masa wani abu ma?".

Ruma ta ce "Za mu ci indomie"

"Ai ko mayya ce ke, sai dai ki ci kan ki"

Tashi ta yi ta koma kusa da Aliyu, ta ce "Dan Allah zan ci".

"Wai ke da mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani".

Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina"

Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?"

Flashing aka yi wa Aliyu, ta leƙa wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba".

"Ohhh ni Æ´a su, yaya Aliyu soyayya?"

Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar".

"Kuɗin wayar sun ƙare ne ake mini flashing?"

"A'a ba su ƙare ba, bana son ka ɗaga su ƙare ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing"

Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz É—in ne?".

"Eh, yanzu na shigo gida ma"

"To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci"

"To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ƙoshi da yawa".

Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da Æ´an mata?"

Daƙuwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye.

"Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?".

"Uban wa ye ya ce miki ita ce"

Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?".

Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu"

Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai"

"Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuÉ—in aure za a kai masa, yana gama service. "

"Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni"

Aliyu ya doke mata ƙeya ya ce "Ƴar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta".

Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya É—au plate ya fice daga É—akin yana dariya.

Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuÉ—i, sannan kuma wa iman take so

Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy".

Ya ce "Ƙarya ki ke yi".

"Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan"

Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ƙofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka".

Ya ce "To ina jin ki"

"Yaya usy, dama...dam..mm"

"Wai meye haka ne?"

"Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma"

"Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba".

"Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faɗar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taɓa ni, zai ƙara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son ɓata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya"

Ayshercool.
Chapter 82 · 0% Book details