← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 124

Sashe 110

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

"Ya ina ta magana kin yi shiru, me ki ke tunani ne?"

Da sauri ta dawo hayyacinta ta ce "Ba koma" ba dan ya gamsu da babu komai ɗin ba ya ƙyale ta.

Sai dai fa abubuwa suka din ga kai komo a zuciyar rumaisa, har ta rasa wane tunanin ma za ta yi.

Kallon Adam take tana nazari, da jin cewa yakamata komai ya zo ƙarshe haka, ta gaya masa iya abubuwan da ta sani, a wuce wurin kawai.

Mai sunan baba sam bai yi É—okin aikin nan ba, mussman da ya san dolensa ya tafi ya bar Iman, sai dai ya din ga zuwa yana komawa har ta kammala karatun sa.

Daga mama har sauran Æ´an uwansa murna suke yi, da samun aikin da yayi, haka iman ma tana ta yi masa murna, amma ta ga shi sam ko a jikinsa.

"Sweetheart, wai ya naga kamar ba ka murna da samun aikin nan ne? Meke faruwa ne?".

Cikin damuwa ya ce "Kewar matata na fara, zan tafi na barki, yaushe muka yi aure? Muna buƙatar samun isasshen lokaci tare"

Cikin nutsuwa ta ce "Haba my faruk, kar mu yi wa Allah butulci mana, na É—an lokaci ne fa. Dan Allah ka kwantar da hankalinka sai na koma gida, idan ka dawo sai in dawo gida. Shikenan sai Usman ya cigaba da kula da shagonka".

Mai sunan baba ya ce "Ki koma gida, idan na dawo ki dawo saboda bamu da kunya?"

"Tayi dariya ta ce, to ai kamawa ta yi ne, dan Allah ka yi haƙuri, nima zan yi missing ɗin ka sosai da sosai " ta din ga rarrashin sa tare da haɗa masa da kalaman bayar da ƙwarin gwiwa.

Duk yadda ake jiyewa Iman auren mai sunan baba, ya bawa mutane mamaki sosai da sosai, domin ranar da Ruma ta je gidan, ta ɗau wayar Iman tana kallon hotunan biki, ta sha mamakin yadda ya zage yake kwasar soyayya, videos kala². Ita kanta ammi tana hamdala da yi wa Allah godiya, domin kowa ya ga Iman ya san tana cikin kwanciyar hankali.

Mama ta yi wa mai sunan baba nasiha sosai da sosai, a kan riƙe Addu'a, da kuma nasihar ya ji tsoron Allah a kan aikinsa.

Saura kwanaki uku dukkanin su kowa ya tafi garin da aka yi posting É—in sa, takawa ya dawo gida, ya tarar da gidan cike da yayyen ruma har da Mahmud, suka gaisa ya tafi É—akinsa.

Ruma ta bishi, ta bashi abincinsa, tare da yi masa ƙorafin rashin kula Mahmud, sai dai bai tanka mata ba, ya nemi wuri ma ya kwanta.

Bikin Nusaiba ma ya fara ƙaratowa, ammi tana ta shiri, wanda ranar yayi dai-dai da saura kwana ɗaya Mahmud ya tafi shi ma.
Sashin Ammi ya shiga, kasancewar ya É—an kwana biyu bai shiga ba, saboda zuwa lagos da suka yi, Ammi ta ji daÉ—in ganinsa.

Kansa ya risunar ya ce "Barka da wannan lokaci"

Ammi ta amsa masa da "Barkanka dai, kana lafiya?"

"Alhamdilillah, na ce gobe in Allah ya kaimu ne tafiyarmu zan fara zuwa aiki"

Ammi ta ce "Haka Iman take gaya mini, Ubangiji Allah ya sa a fara a sa'a"

Ya ce "Amin" ya kalli Nusaiba ya ce "Kira mini baba uwani" Nusaiba ta tashi, ta je ta kira baba uwani.

Tana ganinsa ta washe baki za ta hau kirari ya ce "Bana buƙata, kayanki zaki kwaso ki bar gidan nan a yanzu"

Gaba ɗaya suka kalleshi da mamaki, ya ce "Ke kin san me nake nufi, ni na roƙi rumaisa ta rufa miki asiri, tare da tunanin ko zaki shiryu, tun da ba zaki daina ba, sai kin bar gidan nan yanzu"

Ammi ta ce "Mahmud ban gane me kake nufi ba? Me ta yi ne? Tsawon shekaru ina tare da ita rana tsaka ka ce ta tafi?"

"Ke kin É—auketa mutum, kin kula da ita da iyalinta, ita kuma tsawon shekaru tana cin dunduniyarki, duk abubuwan da suke faruwa a sashin ki, Mummy na da masaniya a kai"

Gaban Ammi ya faÉ—i ta kalli baba uwani ta ce "Uwani, da gaske yake yi?"

"Wuce ki kwaso kayanki ki bar gidan nan, ki je dan kanki, ko ba a É—auki wani mataki a kanki ba, hakkin mutanen da ki ka É—auka ba zai barki ba"

Mahmud ya ƙi yi wa ammi cikakken bayani, ya kori baba uwani a gaban sauran hadimai, wanda ya san tilas maganar za ta watsu, ace ya yi mata korar kare ba tare da cikakken dalili ba".

Baba uwani na kuka, ta kwashi tsummokaranta, ta fita.

Gaba É—aya ammi ta zama confused, Barira ta ce "Ai ni na san baba uwani ba zata sauya hali ba, nayi mamakin rashin tona mata asiri, da maman sabir ba ta yi ba".

Jin abun da ta faÉ—a, ya sanya ammi ritsa Barira, barira kuwa ta kwashe komai ta gaya mata.

Ammi sai da ƙafafuwanta suka nemi gaza ɗaukarta, saboda tashin hankali da zullumi, hadimar da ta amincewa tsayin shekaru, ita ce ta ci amanar ta.

Kasa jurewa tayi, a daren ta je gidan takawa, hankali a tashe, dan kuka take suka je gidan. Wanda hakan ba ƙaramin ɗagawa ruma da takawa hankali yayi ba.

Rumaisa ta tabbatar mata da ta san baba uwani muguwa ce, tun a lokacin da ta din ga gaya mata takawa mahaukaci ne, da lokacin da ta ce Mummy tana yi wa takawa asiri maganar ta koma kunnen Mummy.

Rumaisa ta tabbatar mata da cewa, Mahmud ya gaya mata ya sha ganinta cikin dare a sashin Mummy, amma ya ce kar su tona mata asiri a lokacin, saboda basu da cikakkiyar hujja, yanzun ma tun da ya ce ta tafi, yana da dalilin yin hakan, kuma ko daga baya an tayar da magana, suna da cikakkiyar hujja a kan ta yanzu.

Sai a lokacin ammi ta din ga tuna wasu daga cikin abubuwan da suka gabata, tabbas idan da babu munafuki a sashin ta, babu yadda za ayi wasu maganganun su din ga fita.

Sai dai a hakan ma, ruma ta ɓoyewa ammi binne-binnen da baba uwanin ke yi mata a cikin gidan.

Takawa ya din ga rarrashin ammi yana bata haƙuri, tare da yin faɗa dalilin da ya sanya Mahmud ya kori baba uwani kai tsaye, ba tare da girbar abun da ta shuka ba.

Ammi ta daÉ—e abun nan yana ci mata zuciya, ta daÉ—e tana jinjina tsawon lokacin da baba Uwani ta yi, tana zaluntar ta, ta hanyar kwasar sirrinta tana kaiwa wajen Mummy.
Chapter 110 · 0% Book details