← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 124

Sashe 66

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ƙyae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haɗu da ciwon zuciya da ƙuruciyarta.

Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faɗi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ƙarshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba.

Ɗa da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ƙauna, a baya, Mahmud ma ya ɗimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar.

Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka É—aga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima.

Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, ɗan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karɓe ɗan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaɗaitawa ƙawarta Lubabatu, ɗan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ƙiyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murɗaɗɗen hali na mahaifin su.

Adam yana girma ciwo yana É—an raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida.

Ya shaƙu da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ƴar ƙaramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida.

Gefe guda, Samha ta ƙallafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam.

Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ƴan uwanta ke nunawa aisha ƙiyayya, ganinta suke kamar ba ƴar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce 'yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya ɗaukkota, ko Ammi ta aika a ɗauko mata ita.

Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake muguwa kamar Mummy, saboda waɗan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da ɗaya ba, idan uwar ɗa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa riƙon ɗan sa, babu wanda zai bawa riƙon ɗan sa.

Tun Samha tana ɓoye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba.

Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ƙaninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ƙular da ita sosai da sosai.

Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta roƙe shi ya nemawa Adam auren Aisha.

Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin É—an ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani.

Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ƙi ya mata ita gaba ɗaya.

Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ƙuduri aniyar ko da bala'i sai ta auri Adam.

Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya É—ari bisa É—ari.

Ayshercool.
08081012143

What's app only please
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya ɗan samu sauƙi, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ƙafar dama.

Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matuƙar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ƙaunarsa, kusan halinsa ɗaya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai ɗa'a da ladabi.

Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi  wurin matayensu, tana ɓata Ammi da ƴaƴanta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu.

Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga ɓari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ƙannensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ƙyaleta ba da sharri, da haɗata da Turaki, wai ba ta ɗauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima.

Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen haƙora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.

Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank É—in sa ya fi na Jamil.

Akwai aiki da ƙoƙari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.

Bashi da aiki bankaɗa, da tonawa mugwayen ƙasa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ƙasa ɓarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ƙi.

Ba ƙaramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ƙi bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma yaƙi sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ƙi ji.
Ya koma ya bankaɗo wata tawaga, da suke yi wa kansu laƙabi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ƙungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na hayaƙi, an rubuta THE SMOKE.

Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ƙishin walili zai tsayar da ɗan sa takarar senator, shi kuma za a ɗauke shi vice president, su yi takara, da ɗan takarar da zai tsaya shugabanci ƙasa.
Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.

Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haɗa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da ƴan jarida da suke da burin yi wa ƙasa aiki saboda Allah.

Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna riƙo.

Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ƙwafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.

Saurayin babbar Æ´ar Mummy, Surayya, Wambai ya haÉ—ata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.

Ƙarshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.

Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ƴaƴan mai martaba, ɗaya shi ma ya liƙe Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.

Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.

Iman ba ta da wata ƙawa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar ɗakinta Aisha matar takawa.

Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taɓa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.

Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son É—an ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.

Wambai ya yi ta faÉ—a ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.

Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani ƙanin abokin Adam ya fito zai auri iman, ɗan babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman.

Adam kuma shekara huɗu da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na ƙarshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa.

Ya ce karatu za ta tafi ƙarowa ƙasar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce.
Chapter 66 · 0% Book details