← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 124

Sashe 100

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahmud ya ɗan yi shiru ya ce "Ban san a yaya zaka ɗauki abun ba? Na san zaka ji shi hagu a dama. Kamar yadda kowace uwa da ɗa, yake akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu, to ni saɓanin haka ne, ba wata soyayya ko shaƙuwa tsakanina da tawa uwar, hasali ma a gabana ake cutar da ita, bana iya cewa komai. A lokacin da iman ke kan ganiyar kwasar baƙin ciki na fasa aurenta a jejjere, a lokacin ammi ta nemi alfarmar na auri iman, amma na ƙeƙashe ƙasa na ce ba zan ba.
Ni kaina bana gane yadda wasu abubuwan suke gudana, har sai da rumaisa ta shigo rayuwarmu, take ta ƙoƙarin haska mini hanya, da farko da ni daga nannauyan baccin da nake yi. Tana ta ƙoƙarin gyara tsakanina da mahaifiyata. Na san zaka ji labarin a wani iri ba lallai ka fahimta ba, amma ka bar shi a haka, ni dai fatana, ka bani dama ko yaya nayi wani abu a kan rayuwar iman, ko dan farantawa ammi da kuma rumaisa".

Ya share hawayen da ke ƙoƙarin zubo masa, ya fita daga gidan, tabbas kamar yadda ya faɗa, umar bai gane kan wannan rikirkitaccen zancen ba, tayaya zaka rayu a cutar da mahaifiyarka a gabanka, ba tare da ka ɗauki wani mataki ba?.

***
Baccinsa yayi nisa sosai, har alarm ɗin wayarsa ya dinga bugawa na sallar dare, amma bai tashi ba, sai da rumaisa tayi masa wani duka da ƙafarta a ciki, ya tashi a razane.
Har ya tashi zaune, bacci kawai take yi, kuma kaÉ—an ya rage ba ta faÉ—a daga kan gadon ba, duk ta baje kamar baccin jarirai.

Janyota yayi ya gyara mata kwanciyarta, ya rufeta da bargo..
Yayi shiru yana kallonta, tare da mamakin yadda Allah ya yassare mata baiwa kala-kala, a haka dai gata ba ta ji sam, amma tana da baiwa ba ƙarama ba, shi kansa yana mamakin yadda yake lallaɓata, yake bin duk abun da ta ce masa.
Maybe hakan ba ya rasa nasaba da yadda yake ganin girma, da kuma darajar abun da tayi masa, wanda ko duniya zai bata ba zai biyata ba.

Ya durƙusa yayi kissing ɗin goshinta, sannan ya sauka ya shiga banɗaki.

Da safe kuwa yana banɗaki yana wanka, tana tsaye a gaban dressing mirror, tana kallon kanta a mudubi, tunani take maiyasa ba ta zo da sabayarta ba, dan ba ƙaramin missing ɗin kunun take yi ba. Kar fa ta je su koma yadda suke a da, gaskiya gara ayi a koma gida, ta cigaba da amfani da kayan maman Khadija da na maman ilham.

Knocking aka yi a ƙofa, ta nufi ƙofar ta buɗe, ta ga wata mata a tsaye, cikin broken English matar ta ce mata abincin da aka yi order ta kawo.

Rumaisa ta ce "Wannan wane irin turanci ne babata, wannan kalar turancin kamar na Æ´an lagos, kenan turancin kano daban, na anty laila Æ´an canada daban, na abuja da Lagos iri É—aya?"

Matar ta ce "Ban gane me ki ke faÉ—a ba?"

Rumaisa ganin matar ba ta jin hausa, ya sanya ta samu abun yi, ta riƙe ƙugu ta ce "Na ce, wane irin turanci ki ke yi, ke baki iya hausa ba? Kuma dai papa bai fita ba, kuma bai yi waya ba, ya aka yi ki ka kawo abinci, ko na sadaka ne?" Kamar shashasha matar take kallon ruma, dan ba ta fuskanci komai ba.

Takawa ya ƙaraso ya karɓi kayan hannun matar, ya yi signing ya ce mata ya gode.

"Wai ni ya aka yi ka saka aka kawo abinci, naga ba wanda ka kira a waya"

Ya ce "Ai na so matar nan ta zane ki, kawai kin saka mata a gaba, kina ta mata surutun banza da hausa, bayan ba ganewa take yi ba".

Ta ce "Mhmm, nima fa kamar da a makarantar mu, bana gane komai, kamar dai ni da matar nan, ni babban abun da nake ganewa, a bani kuÉ—in makaranta na sai goriba, ko manÉ—o na yi tsokana da surutu na dawo gida".

"Yanzu fa?"

"Ina ganewa, anty laila ke koya mini sosai, kuma zaka ga result É—ina"

Suka karya, yana yi mata mitar, dukan da tayi masa cikin dare. Dariya ta din ga yi masa, ta ce "Ai dama na gaya maka, Innalillahi ni fa sai da aka yi mini aure na daina fitsarin kwance, musamman idan ana sanyi, in ji fitsarin ya matseni, sai in yi mafarkin gani ina fitsari a banÉ—aki, wallahi ina tashi zan ga nayi a kwance"

"Yanzun ma waye ya sani ko kuna abun ki?"

Ta ce "Haba papa, lokacin fa ina yarinya ne fa nake baka labari"

"To yanzun girma ki ka yi, ko da yake an fara girma fa, mantawa nake yi" Saboda kar ya zauna ya fara tsokanar ta, ya sanya ta tashi ta tafi window tana leƙawa.

Can ya ji ta ce "Innalillahi"
Ya É—ago ya ce "Lafiya?"

"Papa ina ka kawo mu nan? Nan ai duk ƴan iska ne leƙo ka ga fa"

Ya ƙarasa ya tsaya a bayanta, wasu mata take nuna masa, sun sha matsatsun kaya, marabarsu da tsirara kaɗan ne, sai kaiwa suke suna komowa.

Ya ce "Sun yi kyau tubarkallah" ba shiri ta kalle shi ta ce "Me ka ce?".

"Na ce sun yi kyau"

HaÉ—e rai ta yi ta ce "Amma dai ka san haram ne ko?".

Adam ya ce "Ke fa ki ka nuna mini" janyo window tayi ta rufe tana huci.

Ya fara ƙoƙarin ture ta ya sake buɗewa ya ce "Matsa ban gama gani ba"

Rumaisa ta haÉ—e rai ta ce "Wallahi ba zan matsa ba"

Yayi murmushi dama abun da yake so kenan, ya ce "Yanzu da cewa na yi, ki saka irin kayan, cewa zaki yi ke ba ƴar iska ba ce,  tunda na ga na bati, ai sai ki barni na kalla ko?"

Tayi shiru tana kallon sa. "Ko zaki saka?" Yayi maganar yana tsareta da ido, sai dai tayi shiru bata bashi amsa ba.

Ya ce "Ke ba Æ´ar iska ba ce ko? Laila ba ta gaya miki babu kunya tsakanina da ke ba?"

Shiru tayi tana tunani, tabbas laila ta gaya mata, kuma usy ma ya gaya mata, kenan da gaske suke mata?.

A hankali ya ce "Shikenan, laifina ne" ya juya ya bar wurin.

"Zan saka" ta furta kamar tayi zunubi.

Ya tsaya ya waiwayo ya ce "Are you serious?" Ta jinjina masa kai alamar eh, dan har ga Allah saboda kar ya cigaba da kallon waÉ—ancan matan ya sanya ta ce zata saka, kuma bata son kishiya.

Ya ce "To mu je in anjima mu sayo, zaki saka?"

"Eh amma zaka daina kallonsu?".

"To me zai saka na kallesu? Ai na san ba kyau, in dai zaki saka ba zan sake ba"

Murmushi yayi yana kallon baby face É—in ta, ta faÉ—a ne kawai saboda kishi.

Ya ce "To shikenan, in anjima zamu je, saura sai mun dawo ki ce baki san zance ba"

Wuni suka yi tare, ya bata damar yin surutunta son ranta, ba tare da nuna mata ya gaji, ko ya ƙosa ba, suka sha dariyarsu tare ta bashi labaran ta lokacin tana gida, salla ce kawai ta din ga fitar da shi.

Da zai fita sallar magariba ya ce mata "Mimi, ki zauna karki fita ko ina, idan na idar da salla zan je meeting ba daÉ—ewa zan yi ba, zan dawo in sha Allah"

"Wai ni zaka bari a É—akin nan nikaÉ—ai?"

"Eh, ba daÉ—ewa zan yi ba"

"Wallahi tsoro nake ji, haka kurum a yankani, idan ka tafi sai dai ka tarar da ni a bakin titi, ko na É—aukko rigima da sai an koromu daga wurin nan. Ko kuma in jiraka a wurin shigowar nan, kuma ka bani system É—in ka da wayarka É—aya nayi game har ka dawo".

"Salon ki goge mini wani abun, idan ki ka goge mini abubuwana, sai na kai ki prison, zan baki amma a É—aki zaki zauna".

Rumaisa ta basar ta ce "Prison ai sai marasa gaskiya, dan Allah kar ka barni a nan papa, da gaske tsoro nake ji fa" tayi maganar cikin shagwaɓa.

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Bari na je nayi sallar sai mu tafi".

Da misalin ƙarfe takwas da mintuna biyar na dare, takawa yayi parking a gaban harabar wata plaza, ya sanya rumaisa a gaba, suka shiga.

Wani irin katafaren office ne, ƙato mai kyan gaske.

A can suka tarar da bashir ma, ruma ta ce "Yaya bashir, ya aka yi ka zo nan?"

Ya ce "ÆŠazu na shigo ni, ai ya ce mini tun jiya ku ka zo"

Suka gaggaisa da mutanen wurin, sai dai ruma ta raɓe a kusa da adam, saboda duk sai ta takura, ita kaɗai ce mace a cikinsu.

"Adam wannan kuma fa?" Cewar É—aya daga cikin su, da ya tsare rumaisa da ido.

Barrister sa'ad ya ce "Madam É—in sa ce".

Ya ce "Masha Allah, amma me zata yi a nan, harkar aiki ce fa"

Adam ya ce "Ba zata hanamu aikinmu ba, mu fara kawai barrister meye a ƙasa?"

Barrister sa'ad ya ce "Eh to, harƙallar fasa bututun man fetur, da kullum ake yi wa ƴan ƙasa ƙarya da ita, Dss sun kama mutum uku shekaranjiya a delta, bayan sanarwar da hukumar matatar mai ta fitar cewa, man da ake samarwa a Nigeria yayi ƙarancin da kuɗin da yake kawowa ƙasa ba zai wadaceta ba, sai an ciyo bashi, sai dai mutanen sun ce SMOKE suke yi wa aiki, an sake su ba tare da kowa ya san an yi bama, Salim ne yake gaya mini"

Takawa ya ce "SMOKE again?"

Bashir ya ce "Adam, shirye-shirye fa sun yi nisa, wakili zai tsayar da ɗan sa Khalifa takarar ɗan majalisa, kuma ka san jam'iyyar tana da ƙarfin da ko da ƙarfin tuwo zasu ƙwata su bashi, mecece makomar al'ummar da mutumin banza zai jagoranta?"

"Ba wannan ba, cire sunanka da ga jerin jami'an da za a ƙarawa matsayi bayan dawowa daga ƙaro karatu, yafi ɓata mini rai".
Chapter 100 · 0% Book details