← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 124

Sashe 86

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya waiwaya ya kalli nusaiba ya ce "Can you excuse us?" Ba musu Nusaiba ta tashi ta fita.

Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Meya sameki?" Yayi maganar kamar É—an sanda na tuhumar mai laifi.

"Bani da lafiya"

Jin shiru bai ce komai ba, ya sanya ta sake É—agowa, ya zuba mata ido, yana jiran ta bashi amsa, dan wadda ta bashi ba ta gamshe shi ba.

"Zuciyata ce take kumbura"

"Meyasa?"

"Nima ban sani ba"

Ya ce "Kin sani"

Shiru ta yi tana wasa da yatsunta.

Ya ce "Well, Allah ya sauwwaƙe, kin san condition ɗinki, bai kamata ki din ga wasa da lafiyarki ba, and na ji rumaisa ta ce You are getting engaged very soon, Allah ya sanya alkhairi"

Kawai ta fashe da kuka, yayi ƙuri da ido yana kallon ta, dan bai san me zai ce mata ba.

Tayi me isarta, sannan ya ce "Auren ne ba kya so?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Meyasa ki kai shi gidanku, idan ba kya son shi?"

Iman ba ta san ya aka yi ta tsinci kanta da yi wa mai sunan baba bayani ba "Bana son shi, mamansa ta ce ba zai auri wadda ba ta da asali ba, gashi ya riga ya kai maganar wurin wambai"

"Idan ba kya son shi, wa ki ke so?"

ÆŠagowa ta yi a hankali, suka haÉ—a ido, jikinta yayi sanyi yayin da mai sunan baba yaji tsigar jikinsa tana tashi.

"Kuka ba ya maganin matsala, Addu'a ce magani, Allah na iya canza komai within seconds"

A sanyaye ta ce "Labarina ba zai canza ba yaya umar, yarinya Æ´ar tsintuwa"

Ya miƙe tsaye ya ce "Zai canza, put your trust on Allah, Allah Ya ƙara lafiya" tabi bayansa da kallo, wata irin ƙaunarsa na ratsa zuciyarta.

Yayin da shi ma yake jin matsananciyar soyayyarta da tausayinta a nasa ran, ji yake tamkar kar ya tafi, sai ta samu cikakkiyar nutsuwa ta kwantar da hankalinta.

Yana daf da kaiwa ƙofa, Jabir ya buɗe ya shigo.

Ayshercool
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya.
Mai sunan baba na fita, ya jiyo muryar jabir yana yi wa Iman tsawa "Wai iman waye wannan, meye alƙarki da shi, uban me ya zo yi wurinki?"

Cikin wata irin azababbiyar zuciya mai sunan baba ya koma É—akin, motsin shigowarsa ya sanya jabir haÉ—iye sauran maganar sa.

Mai sunan baba ya taka, ya je gaban jabir ya tsaya, ya ce "Ni zaka tambaya waye ni, da dalilin da ya sanya na zo wurinta"

Jabir ya haÉ—iyi yawu cike da kishi ya ce "Na san kai yayan matar Adam ne amm....

Umar ya kaste shi ta hanyar cewa "Bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ku, ƙanwata ake aure a familynku, sai dai akwai mutunci da karrama juna, albarkacin ana auren ƙanwata a familynku, ni yakamata ka yi wa duk wannan tambayoyin ba mara lafiyar da ke kwance a gadon asibiti ba, ko ba ka san abun da yakamata ba".

Da ƙyar jabir ya aro jarumta, dan gani yake, da yayi kyakykyawan motsi, mai sunan baba zai iya kai masa naushi, ya ce "Amma ka san babu wata alaƙa tsakaninmu meyasa za ka zo in da take, aurenmu fa za ayi"

Mai sunan baba ya ce "Amma ba ayi ba ko?" Jabir yayi shiru.

Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice.

Laila ta ce "Waye wannan?"

Nusaiba ta ce "Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma".

"Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ƙarti suna kaiwa suna komowa a wurin matar da zan aura, wannan ai cin amana ne"

Laila ta ce "Nawa ka biyamu kuÉ—in gadin da zamu hana wasu zuwa wurin iman jabir? Kai ka isa kyakywar yarinya kamar iman, ka ce zaka hana masoya zuwa wurinta"

Jabir ya ce "Ba haka bane ba anty laila, amma ai kun san bai kamata ba".

Laila ta ce "Haba jabir, kalli fa kuka take yi, da wanne za ta ji? Kuma dai naga ai baka kai kuɗin auren ba tukuna. Kai baka san ka lallaɓata ba"

Ya ce "Haka ne, Allah ya bata lafiya, kishi ne ya sanya ni yin hakan, zan dawo da safe" ya ajiye ledar hannunsa ya fita.

Laila ta ƙarasa gaban gadon, ta zauna ta rungumo iman tana rarrashinta.

Ta samu ta É—an yi shiru sannan ta ce "Ashe rumaisa tana da wa babba kamar haka"

Nusaiba ta ce "Ba ki ji ana ce mata ƘANWAR MAZA ba? Yayyenta bakwai maza, ita ta takwas"

"Masha Allah"

Nusaiba ta ce "Amma wanda ya fitan nan, shi da Hassan É—in sa ne manya, masifaffe ne, ba shi da fara'a ko kaÉ—an, daga zuwansa fa wai na tashi na fita".

Halin da take ciki, bai hanata sake lafewa a jikin laila ta ce "Ba masifaffe bane ba, yana da kirki"

Laila ta shafa kanta ta ce "Ko dai ko dai? Ko akwai wata a ƙasa ne" iman tayi shiru ba ta ce komai ba.

Laila ma tayi shirun, tana cigaba da shafa kan Iman.

Mai sunan baba kuwa, yana kan babur ɗin sa ƙirar lifan, babu abun da yake tunani sai kukan iman, kuka mai taɓa rai, ga wannan mara hankalin a yanayin da take ciki, ya je yana yi mata masifa.

Laila kuwa sai da ta ga iman ta samu bacci, sannan ta kwantar da ita.

Mai sunan baba sai da ya koma gida, sannan ya samu ya ci abinci, sai dai condition É—in iman, da kukanta ya gaza barin zuciyarsa.
Tuni laila ta yi bacci, ita da Nusaiba, iman kuwa jin wayarta tayi vibrating a ƙasan fulo, ya sanya ta buɗe ido.

"Ya jikin?" Da sauri ta sake mutstsuke idanunta, ba mafarki bane ba, mai sunan baba ne.

What's app ɗin ta ta buɗe, ta tura masa saƙo "Yaya umar ya ka je gida, Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi, bacci ne ya ɗaukeni, shiyasa ban tambayi ya ka je gida ba".

"I don't mean you should reply now, bacci yakamata ace kina yi yanzu"

Wani irin murmushi iman ta yi, a ranta ta ce 'Gane in da ka saka gaba sai Allah yaya umar'

Tayi masa reply da emojin murmushi ta ce "You are a good counsellor, na ji daɗin nasiharka, but please include me in your prayers, Allah ya bani mafita" ta haɗa da emojin kuka da na magiya a ƙarshe 😭🙏.

Ya sauke numfashi a hankali ya tura mata emojin kuka da cancel 😭❌.

"To na daina in sha Allah"

Ya tura mata alamar jinjina, sannan ya tura voice message, abun da ba ya yi, shi chatting ɗin ma ba damunsa yayi ba, amma yayi mata message "Na ga saura few weeks bikin saukar alƙur'aninki karo na uku, kamar yadda ki ka ɗora a status, wannan kawai ya isheki godiya ga Allah, babbar ni'im ce da baiwa, da ba kowa yake yi wa ba. Dan haka kar ki daina addu'a khadija, kuka baya maganin matsala kamar yadda na gaya miki ɗazu"

Subhanallah, iman taji voice É—in babu adadi, musamman jin sunanta na asali a bakinsa, yana da very deep voice irin na cikakken namiji jarumi, wanda muryarsa kawai ta isa sanya mutum shiga hankalinsa.

"Alhamdilillah, yaya umar ashe kana ganin status ɗina, haka ne na kusa sauka a karo na uku, na gode sosai yaya umar, na yadda you are very simple, unlike before da kake bani tsoro" ai shi ma a nasa ɓangaren, ya saurari voice ɗin ta bai san iyaka ba, sassanyar muryarta wadda yake gauraye da sigar shagwaɓa, haɗi da iyayi mai matuƙar daɗin sauraro".

Tunawa yayi da Jabir ne zai aureta, gaba É—aya ya ji wani irin haushi ya kama shi, ba tare da yayi reply ba, ya rufe datar sa ya kwanta.

Yayi shiru yana tunanin, duk wanda ya auri mace kamar iman, idan bai tausaya mata ba, sai yaushe, mai zai sanya mutum ya din ga É—aga mata murya haka, yarinyar da gaba É—ayanta kalar tausayi ce.

***
Sai da ta kwana biyu, sannan aka sallami iman suka koma gida, sai dai ammi ta shiga saƙe-saƙe a kan batun auren nan.
Rumaisa ta zauna ta zana takawa a plane sheet, tare da calendar a ƙasa, wadda kullum take cancel ɗin kwanan wata, na lokacin dawowar takawa.
Laila ta ce "Rumaisa meye haka? Ya zaki liƙe mini hoton gunki a ɗaki"

"Papan ne gunki, wallahi ba gunki bane"

"To ni a wurina gunki ne mana, kawai ki zana É—an alajani ki kafe mini, baga hotonsa nan a waya ba"

Ruma ta ce "Ni bana son na waya, na fi son wanda na zana shi da kaina, ba kin hanamu yin video call ba, kuma ke kullum sai kin ga mijinki ba, ki bar mini zanena"

Lailaa kawai tayi murmushi, wasu lokutan rigimar rumaisa dariya take bata.

"Kin sha kununki na yamma, da maganin maman ilham?"

"Na sha mana, ai anty laila bana wasa”

Ta ce "Good, yanzu dai je ki É—aukko jakarki ta islamiyya, da ta makarantar boko muyi karatu, kin ga exams za ku fara"

Ruma ta tashi ta ce "Bari in É—aukko, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"

Tana fita falo tayi kiciɓis da Jabir, ya ɗago a yastune ya kalleta ya ce "Yauwwa dan Allah yi mini magana da iman mana"

Cikin tsiwa ta ce "Kai ka isa? Wallahi baka isa ka aikeni na je ba, ka nemi Æ´ar aiken ka"

Jabir ya ce "Wai ke meye haka, ka kowa ma sai ki ci masa mutunci baki da kunya?"
Chapter 86 · 0% Book details