← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 124

Sashe 103

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

Tuni idonta ya cika da hawaye ta ce "Haba papa, duk abun da fa ka ce in yi ina yi, kuma duk da haka sai ka yi auren?".

Ya sake kashingiÉ—a ya ce "Yanzu ba gashi kina yi mini gardama ba".

Kawai ta kifa kai ta cigaba da kuka, maimakon ya rarrasheta, sai ya kwanta a bayanta ya ce "Rigimar ki ke so, ba kuma zan kula ki ba". Ta gama kukan ta hau bacci.

Da yamma ya ce ta shirya, ya kaita shan ice cream, tun da a satin za a koma makaranta, yakamata su tafi gida haka.

Tayi ta murna za su koma gida, duk da ta wani fannin zamansu a abuja yayi mata daÉ—i, ta wani fannin kuwa zata iya cewa, ba ta ji dadin sa ba.

Adam kuwa har fargabar komawa Kano yake yi gidansa, kar ya je su koma, matsalar nan ta sake dawo masa.

Ita kuwa baki yaƙi rufuwa, da suka koma, gidansu ya ɗan yi ƙura, ta gyara abun ta fes, ta karɓi wayar adam ta sanarwa da mama sun dawo, zata je gida a cikin satin, mama ta ce ba sai ta zo ba, ita zata kawo mata ziyara.

Rumaisa ta din ga murna kusan shekara da aurenta, sau ɗaya mama ta taɓa zuwa gidanta.

Ta cewa takawa, ya É—aukko mata sabir, dama anty laila ta ce yana ta rigima, Adam ya ce sai dai su je ta ganshi su dawo gida.

Ta ce "Amma saboda me?"

"Ya fara wayo, ba zai kwana a tsakaninmu ba".

Cikin damuwa ta ce "Amma papa saboda me? A É—akina zamu din ga kwana da shi".

"Saboda mun daina raba É—aki daga yanzu, sai ya shekara biyu ko uku, ya isa shiga makaranta, kan lokacin kema kin kammala makaranta, zan É—aukko shi gaba É—aya ya dawo gidan nan, a gyara masa É—akin sa"

Kai tsaye ta gane nufinsa, a tata wautar, da suka dawo gida, shikenan ta huta, amma taji ya kawo wata maganar daban.

Kamar da wasa, taga da gaske takawa yake yi, ba zasu sake raba wurin kwana ba, babban abun da ya ƙara sa shi farinciki da bashi mamaki, bai wuce jin ya koma normal ba har a gidan.

Sai washegari suka tafi gidan ammi, ana ta shirin bikin iman da mai sunan baba.

Suna mota kan su sauka takawa ya cewa ruma "Kalli can" ta É—aga kai, ta hango mai sunan baba tare da iman, tana magana yana murmushi.

Ruma ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, su mai sunan baba an tafi duniyar love".

"Ina tausayawa iman zama da wannan yayan naki, dan dai ta nace ne kawai, amma gani nake kamar za ta sha wahala, mutum sai izza da jin kai".

Ta haÉ—e rai ta ce "Papa abun ma ba kara, yayana ne fa"

"Shi ɗin fa, kema ai kin san gaskiya, gashi dai ƙanwata yake so, amma ko zan wuce sau goma ko kallona ba zai yi ba".

"To ai kaima baka kula shi"

Ya ce "Oho muku dai, ki taho mini da key É—ina, kya je ku gaisa, ni ta baya zan shiga"

Ya buÉ—e motar ya fice, duk da murmushi yake yi, iman na masa zancen su saka kaya iri É—aya ranar dinner, yana ce mata shi kunya yake ji, ba ya son taron mutane.
Tana yi masa magiya, tana ganin rumaisa ta nufeta tana murmushi suka rungume juna, ta ce "Mimi sannu da zuwa ya Abuja?"

Ruma ta ce "Abuja ba daÉ—i".

Iman ta ce "Haba dai? Baki ji daÉ—in garin ba ne ko yaya?"

"Ke dai a bar zancen kawai" ta risuna ta gaida mai sunan baba, tamkar ba shi ne yake murmushi ba, ya amsa cikin basarwa.

Sai da ya lura da yadda tayi ƙiba, ta ƙara kyau da haske, kuma daga yadda take yawan faɗan Adam, ko waya ake yi da ita, ya sake tabattar masa da tana cikin kwanciyar hankali.

Sabir har da wata ƴar ƙara, saboda murnar ya ga miminsa, Ammi ta ce "Allah ya shiryeka sabir, wani ma sai ya ce ba a kula da kai, kullum sai yayi kuka mimi"

Ruma ta yi dariya, tana kuma rungume shi, soyayyarta da Sabir, haÉ—in Allah ce kawai.

Rumaisa suka koma hutun makaranta, sai dai duk ranar da takawa ya addaba mata, da safe sai ta lafke ta ce ba zata je makaranta ba.
Haka zai yi ta fama da ita, sai dai ta je a makare, har makarantar suka fara complain da yawan fashinta da makara.

Gefe guda kuma, yana ta fama a kan son gano, suwaye SMOKE, saboda ya san mutanen da ya addabawa da yawa, in dai aiki ya biyo ta kanka, babu ruwansa, kawai zai yi aikinsa ne, dan haka takamaimai ya kasa gano suwaye.

Ranar da mama ta zo, kamar rumaisa ta shige cikin mama, ta sauketa da kayan ciye-ciye kala-kala, sai dai mama ba ta fi awa biyu ba, ta ce Aliyu ya tashi su tafi, dama shi ya kawota, rumaisa har da kuka, mama ta ce babu amfani zarya a gidan siriki, haka suka tafi.

***

Magiyar da Mahmud yayi ta yi wa mai sunan baba ce, ta sanya ya bashi damar saka masa hannu a harkar gininsa, ƙofofi na alfarma, da glasses na window, haka ya saka a gidan da Iman za ta zauna, aka yi tiles mai kyau, gida yayi kyau sosai dai-dai zaman amarya.
Kuma ya yiwa mai sunan baba alƙawarin cewa; ta ɓangaren sa babu wanda zai sanarwa da cewa ya taimaka masa a harkar ginin.

Lokaci yana ta ƙaratowa, aka kai kayan lefen iman, Akwatuna shida da kit, dai-dai gwargwado yayi ƙoƙari iya ƙarfinsa.
Sai dai da yake maƙiyi, ko ruwa ka shiga sai ya ce; ka tayar da ƙura, haka aka din ga kushe lefen nan, wai kamar iman, a rasa abun da z aa kawo mata, sai wannan kayan, babu wadda aka taɓa aurarwa a gidan, aka yi mata ƴan wannan kayan tsiyar, sai ita.

Laila ta saka aka kwashe kayan lefen aka mayar gidanta, ta ce ba shegen da zai sake zuwa ya ga lefen, su sun karɓa kuma sun yaba, dan haka duk wani munafuki, ya je yayi yadda zai yi.

Iman kuwa da rawar jiki ta kira mai sunan baba, tana yi masa godiya.

Rumaisa sai murna take tana cewa "Amarya tawa ango nawa, wai ni ranar bikin nan ina zan je ne ma?"

Takawa ya ce "Sai ki rabu biyu kawai, rabi a nan rabi a can". Shi kansa takawa, ya yaba abun da umar É—in ya kawo, a zuciyarsa dan bai furta ba.

Ammi kanta bakinta yaƙi rufuwa, dan ta yaba nesa ba kusa ba.

Turaki da kansa ya yi wa iman kayan É—aki, kamar yadda yake yi wa Æ´aÆ´an Galadima idan za su yi aure.
Wani kayan kitchen da sauransu kuwa, laila ce tayi wa iman, takawa ya sai mata kayan electronics, kuma a hakan gudunmawa ko ta ko ina kawota ake yi.

Mahmud yayi sallama a falon, suka amsa masa, sabir da gudu ya nufe shi, yana kiran daddy, har yana neman ya faÉ—i, yayi carf ya É—auke shi yana murmushi.

Ya risuna ya gaida ammi, ta amsa masa cikin sakin fuska.

Ya kalli laila da a sanadin rumaisa, suke gaisawa, saɓanin da da har ta ƙaraci zamanta a gidansu faɗa suke yi.

Ya ce "Hajjaju barka da wannan lokaci?".

Laila ta ce "Mamuda kana lafiya?"

"Ki daina ɓata mini suna mana, daughter ashe tafiya ku ka yi?"

Ruma ta ce "Wallahi kuwa daddy, ya garin, ka karɓo offer taka kuwa? Wane aikin ne kuma"

"Na karɓo, an bamu ni da yayana?"

Rumaisa ta ce "Papa, to ai papa yana da aiki".

Ya harareta ya ce "Ba shi ba. Aikin coustom ne"

Ruma jikinta ya É—an yi sanyi sannan ta ce "Allah ya sanya albarka ya tsare muku, a kula da aiki daddy, dama na san kai me gaskiya ne, ka bawa ammi ta gani".

Ya ƙarasa ya ajiyewa ammi envelope, ammi cikin jin daɗi ta karɓa ta buɗe tana dubawa ta ce "Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, ya sa rai da lafiya su mora, Allah ya tsare maka"

Ya ce "Amin na gode"

Laila ma sanya albarka suka din ga yi, goga Adamu kuwa kamar bai san me suke yi ba.

Iman ma ta ce "Allah ya sanya alkhairi yaya".

Ya amsa da "Amin amarya. And mutum nawa zaku gayyata na wurin dinner? Zan É—au nauyin abinci".

Ammi za ta yi magana, laila ta ce "Godiya muke, Allah dai ya saka da alkhairi malam mamuda"
Chapter 103 · 0% Book details