← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 124

Sashe 76

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta cigaba da yi masa raɗa ta ce "Amma duk da haka fa, ban manta abun da ka yi mini ba, kuma zan rama". Jabir ne yayi sallama a falon, sai zuba ƙamshi yake. Ya ɗan tsaya yana kallon yadda rumaisa ta daddane kafaɗar Adam, ta dafa kafaɗarsa take yi masa raɗa, a tsakiyar falo ma'aikata na kaiwa suna komawa.

Ya ƙaraso ba tare da rumaisa ta tashi ba, dan ba ta da niyya ma.

"Takawa barka da yamma"

Adam ya kalli Jabir ya ce "Barkanmu dai"

Rumaisa ta yi saurin cewa "Papa zan ƙarasa maka idan mun je gida, bari na kira anty iman mu tafi, da daddare sai mu rako su gida ko papa?" Ta yi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallon fuskar sa.

Ya É—an ja hancinta ya ce "To mimi" ta tashi ta nufi É—akin iman.

Tana shiga ta ga iman na ɓoye wayarta, kasancewar hoton mai sunan baba take kallo.

"Anty iman ta so mu je gidanmu, da daddare sai ku dawo"

"Maman sabir kiyi haƙuri, gobe in Allah ya kaimu sai mu zo".

"Mai sunan baba ne zai zo, yana son zai ga sabir idan ya zo, shiyasa na ce mu tafi tare, sai papa ya dawo da ku, kuma ga wancan jabir É—in ya zo, idan kuma zaki zauna ne shikenan"

Ba shiri iman ta tashi, ta shiga toilet, ta wanke fuskarta ta shirya a gurguje, suka fito tare har da Sabir.

Jabir ya ƙare ta da ido.
Ammi ta ce "Iman sai ina?"

Adam ya ce "Da ita zamu tafi, anjima zamu dawo"

Suka fita, Jabir ya biyo bayansu yana ƙwalawa iman kira.

Adam ya waiwaya ya ce masa "Ya aka yi?"

"Adam meyasa ka ke yi mini haka ne? Ka san wurinta fa na zo"

"Ai ka san yadda muka yi da kai Jabir, tun da ku ka nuna mini iyakata da kai da Jamil, nima dole na tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro. Ka fara nemo yardar mahaifiyarka tukuna, dan ba zaka auri iman ka ta wulaƙanta ba"

Rumaisa kuwa tuni sun yi gaba, Adam ya biyo bayansu, suka tafi.

Shiru Jabir ya yi ya tsaya yabi bayansu da kallo, ya jinjina kai tare da yin ƙwafa.

***
Iman har ta É—an wartsake, suka cigaba da sabgoginsu tare da ruma.

Ta ce "Maman sabir, amma yaya umar zai ci abinci idan ya zo ko? Me za a dafa?"

Ruma ta ce "To, nima dai ban sani ba, sai dai idan ki ka saka shi wataƙila ya ci"

Gumm iman ta yi da bakinta, tare da gudun kar ta sake wata maganar da rumaisa za ta fahimci wani abu.

Mai sunan baba bai tashi zuwa ba, sai bayan sallar magariba.

Duk da ba sakin jiki zai yi ba, amma rumaisa ta yi murnar ganin sa sosai.

Babban abun da ya saka shi farinciki, bai wuce ganin iman ba, sai dai kallo É—aya yayi mata ya san tana cikin damuwa.

Cikin sanyin halinta ta ce "Yaya Umar sannu da zuwa, ya mama?".

"Alhamdilillah" ya bata amsa, a ganinsa yayi ƙoƙari ya amsa mata a sake, ba tare da sanin amsar ta sa ta taƙaice da yawa ba.

Ya kalli rumaisa ya ce "Ga saƙonki nan, na je katsina shekaranjiya, gwaggo ta bani kaya na kawo miki iya ma haka, zaku yi waya da mama".

Ruma ta kalli kayan a manyan ledar viva, ta ce "Amma na gode sosai da sosai, amma mai sunan baba ba yanzu zaka tafi ba ko?".

"Me zan zauna na yi miki?" Yayi maganar yana ƙoƙarin tashi.

Iman ta miƙe ta ce "Na ga kamar ni nake hana shi sakewa, maman sabir, bari in kira sidi a waya kawai, tun da takawa bai dawo ba".

Umar ya ƙure ta da ido, da sai da ta kusa rasa nutsuwarta, duk da da mayafin abaya a kanta, wuyanta sai da ya fito, kuma ya nuna ramar da tayi.

"Na taɓa cewa zuwanki yana hanani zama? Gidan yayanki ne, ni kuma ƙanwata me zan zauna na yi mata?"

Iman ta girgiza kai alamar a'a.

"Mai sunan baba, har gida na taho da ita, ina murna ta tayani muka yi girki,  kuma ka ce zaka tafi ba zamu ji daɗi ba, dan Allah ka zauna ka ci"

"In zauna in ci abinci a gidanki, Allah ya kiyaye" yayi maganar yana kallon agogon hannunsa.

Ruma ta ce "To bari na baka ka kaiwa mama"

"Saboda ni É—an aikenki ne?"

Iman ma ta saka baki "Dan Allah yaya umar, ko ba yawa ka ci" ta faÉ—a a É—an raunane.

Ji yayi idan har bai ci ba ta ji ba daÉ—i, babu lallai ya iya yafewa kansa.

Ya kalli rumaisa ya ce "Spoon biyu kawai".

Iman ta miƙe da sauri, ya ce "Ba ke ba ita"

Yayi maganar yana kallon rumaisa.

Ruma ta tashi a zuciyarta tana cewa son kai.

A zahiri wasa yake da sabir, amma a ɓoye iman yake kallo, yana jin ina ma ta zama mallakin sa, ace kullum gata yana kallonta.

"Ina Mahmud" yayi mata maganar ba tare da tayi tsammanni ba.

"Yana gida" ta bashi amsa duk da ba ta É—ago ba, dan ta san da ita yake.

"Bai koma school ba kenan?"

Iman ta ce "Eh, ina ga ya gama ai"

Bai kuma ce mata komai ba, Ya cigaba da wasa da Sabir, kamar ba shi ba.

Ruma ta dawo da kwano a hannunta, ta ajiye a gabansa, alkubus da miyar taushe, favorite food É—in mai sunan baba.

"Zuba na tafi da shi kawai"

Rumaisa kamar ta fasa ihu, mai sunan baba akwai wulaƙanci, ba yadda ta ita, ta kwashi kwanukan, ta sake komawa kitchen, ta sake bashi damar kaɗaicewa da iman.

Ya samu ya kalleta sosai yadda yake so, sannan ya yi musu sallama ya tafi. Ita kanta iman tana cikin farinciki, atleast sun yi doguwar magana da shi yau.

Tafiyarsa babu daɗewa, takawa ya kira iman, ya ce su fito ya mayar da su gida. A kayan da mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, har da uban fura da nono, kaya guda da su mazarƙwaila, sai addu'oi a rubuce, da wasu saiwoyi da ba ta san ko na menene ba. Ga su ƙuli da man ja da fari, kayan kuka da kuɓewa har da su wake abun ka da mutanen karkara.

Haka ta keta kayan biyu, ta ce wa Iman ta kaiwa Ammi.

A lokacin da Adam ya dawo daga kai su iman gida, ya tarar tuni ruma ta yi bacci.

Ya ci abincinsa, da ya tarar a kan dining, dan yanzu idan ba makaranta ta tafi ba, shine su barira suke dafo abinci.

Ya leƙa ɗakinta, ya tarar tana kwance a ɗakinta da kayan baccinta, ɗan mini skirt, da riga vest, ga jigidar da ke ƙugunta tayi mata cif.

Ya taka ya ƙarasa ya tsaya a kanta, amma baccinta kawai take yi, ya zauna a kusa da ita, ya zubawa ƙafafuwanta ido, daga ƙasa dai ga ta da hips, amma sama kam, yanzu ne ma dai suka ɗan tasa.
Murmushi yayi da ya tuna wasiƙar da ta aika masa, da ya yi ta yi wa Allah godiya babu wanda ya ga takardar ya karanta.

Ya kai hannunsa kan jigidar, yana É—an ja a hankali, yana zancen zuci, abu kamar wasa ya koma shafa cinyoyinta.

Duk da nauyin baccinta, caraf ta riƙe hannunsa, ta buɗe ido "Meye haka?"

Ko a jikinsa ya ce "A ina?"

"Papa bana so" tayi maganar tana tura baki.

"Ni ina so ai" yayi maganar yana janyota ya haÉ—ata da jikinsa yana kallon idonta.

Mutsu-mutsu take tana hararsa za ta ƙwace, amma ya saka hannunsa ya ɗaya ya ɗago haɓarta ya ce "Can we try it now?" Tayi masa ƙuri da ido tana kallonsa.

"Are you ready for it? I want kiss you mimi".

Girgiza masa kai ta yi ta ce "Dan Allah bana so" tayi maganar idonta na cikowa da hawaye.

Bai kuma ce mata uffan ba, yayi abun da rumaisa ko da wasan wasa, ba ta taɓa kawo hakan ba. Kissing ɗin ta yake yi sannu a hankali.

Ta rirriƙe jikinta, tare da jin abun wani banbarakwai a duniyar ta, abun da aka ginata a kan cewa abu ne da bai kamata ba, yau ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin sa.

Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta ji Adam yana ƙoƙarin yin wani abu daban da ya tayar mata da hankali.
Ihu ta din ga yi, tana riƙe rigarta, har da kiran su baba uwani su zo su rabata da Adam, zai yi mata abun da bai dace ba.

Ba ihun rumaisa ne ya tayar masa da hankali ba, illa jin sa da yake yi kamar ba shi ba, kamar an canza shi.

'Me hakan yake nufi?' ya tambayi kansa a É—an tsorace.

Jikinsa ne yayi sanyi sosai da sosai, ga rumaisa a hannunsa na ta ƙoƙarin ƙwacewa.

Kwantar da kanta yayi a ƙirjinsa, ya ɗora kansa a nata, a ransa yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin masifa ce kuma wannan ya sake tsintar kansa a ciki?

Yana jin yadda rumaisa ke ta zubar da hawaye, tana alwashin sai ta gaya wa kowa na duniyar nan, ya saka mata hannu a riga.

"Yi mini shiru, ni ki ke yi wa wannan ihun ko?".

"To waye ya ce ka yi mini abun da ka yi mini, bayan ni a gidanmu an ce mini ba kyau. Wasan banza fa kenan, kuma saboda a daina ce mini ƴar iska na ƙara yadda muka yi aure".

Halin da yake ciki bai hana shi yin murmushi ba, ya ce "Duk wani mai aure É—an iska ne ai, wannan sirrinmu ne, ba a faÉ—a"

Rumaisa ta tashi zaune ta ce "Sai na faÉ—a, kuma kowa na duniyar nan, duk wanda na sani sai na gaya masa"

"Idan ki ka faÉ—a, cewa zan yi ke ki ka ce ayi, gara ma ki yi shiru".

Share hawaye take ta ce "Wallahi ni ba Æ´ar iska ba ce, bani na ce ayi ba".

Takawa ya ce "Oho dai, idan ki ka faÉ—a abun da zan ce kenan, yarinya ki adana hawayenki ma, ba yanzu yakamata ki yi kuka ba. Sai an zo making baby"
Chapter 76 · 0% Book details