← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 124

Sashe 31

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka É—au mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaÉ—ai? To wallahi sai na gaya wa ammi" banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita.

Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa.

Ta kalli iman ta ce "Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?"

Iman ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi, bana son cin komai" mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba.

Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.

Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?"

"Tun É—azu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaÉ—ai" tayi maganar tana nuna Adam.

Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta".

Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai".

Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ".

Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.
Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.

Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.

Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.

Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa  ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa.

Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman É—in kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.

Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa".

Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode".

Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?"

"Yayan rumaisa ne" ta bata amsa.

"Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa"

Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba"

Babu daÉ—ewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.

***
Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.
A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.
Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.

"Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?"

"Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata".

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman É—in, kai a wa? Meye haÉ—inka da ita?"

"Bakomai zumunci kawai".

"Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau"

"Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.

***
Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.
Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana"
Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.

Ayshercool.
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Mama ta ce "Ai kin san masu sarauta ba sa son wauta, ita kuma Æ´ar taki sai fatan shiriya"

Ammi ta yi dariya ta ce "Rabu da su, namu addu'a da ido, ai rumaisan ce dai-dai shi".

"To, Allah ya iya mana ya jikin iman kuwa?"

Ammi ta ce "Jiki yayi kyau mun gode Allah, har tana iya barci yanzu, in da nake ta yi wa Allah godiya, an ce zuciyarta lafiya ƙalau wannan karon, ciwon kai ne dai da razana take yi".

Mama ta ce "Allah sarki, sai a dage da addu'a, a haÉ—a da na islamic, kin san kana da ido ba na ganin gari ba, mussaman ita da take tubarkallah Masha Allah, kyau kamar ita ta yi kanta, sai ana dagewa da addu'a"

"Wallahi maman rumaisa ana yi dai-dai gwargwado, kin san sabgar iyali ce, sai dai ka yi iya yin ka ka bar wa Allah sauran, idan wannan ya ce wash anjima wannan ya ce wayyo, kuma duk kai kaÉ—ai ranka, sai fatan É—aukin Ubangiji"

"Haka ne wallahi, dama shi ne mai tafiyar rayuwar gaba ɗaya, ba dan haka ba idan an kira ka, ba zaka amsa ba, ko yaya ace kula da ragamar gida a kan mace itakaɗai, akwai ƙalubale, Allah ya raya mana su yayi musu albarka".

Ammi ta ce "Amin ya Allah, dan Allah maman rumaisa idan da abun da take buƙata kar a saka ta yi ƙwauron baki, duk ta gaya masa, tun da rayuwa za su yi inuwa ɗaya, a ƙyaleta ta faɗi abun da take so".
Chapter 31 · 0% Book details