← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 124

Sashe 55

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai sunan baba ya yi sallama a falon mama, suka amsa rumaisa ta tashi da gudu ta rungume mai sunan baba.

Ya É—an yi murmushi, ya dafa kafaÉ—arta.

Iman ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau" ya amsa, ya saka hannu ya ɗauki sabir yana ɗaga shi sama.

Iman na son ɗaga kai ta kalli mai sunan baba, amma ta kasa, shi kuma a wayance yake ƙare mata kallo.

Iman ta tashi ta ce "Mama bari na tafi, zan je aiken mama, maman sabir ga kayan abincinsa nan a wannan jakar".

Mama ta ce "Iman ki bari ayi azahar ki ci abinci"

"A'a mama, na ƙoshi ni sai na kai yamma daga yanzu, ban ci abinci ba ma".

Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Nemi wuri ki zauna" tsit kowa ya yi yana kallon mai sunan baba, ai ko motsin kirki ba ta yi ba,ta zauna ta na wuri-wuri da ido.

Ya basar kamar bai yi komai ba, aka cigaba da hira har da shi, haka nan yau yake jin daÉ—in ganin rumaisa a gida.

Sai dai bai ji daÉ—in yadda iman ta takure sosai ba.

Har azahar iman ba ta samu umarnin tafiya da ga mai sunan baba ba, sai da aka gama girki.

Sabir sai rarrafwa yake, kwano-kwano ya ci na wannan ya ci na wancan.
Yadda rumaisa take a cikin yayyenta, ba ƙaramin burge iman yayi ba.

Sai da mai sunan baba ya fita, sannan iman ta samu ta tafi.

Rumaisa da yaya usy ta keɓe, suna magana.

"Yaya yaushe za ka zo, akwai labari fa?"

Usman ya ce "Labarin me?".

"Ni dai kawai ka zo dan girman Allah"

Ya ce "Kar ki damu, zan zo in sha Allah".

Ana idar da sallar magariba, Adam ya zo tafiya da rumaisa, amma ta ce Alla kar ta ba in da za ta" sai da aka kai ruwa rana, sannan ta ɓanɓaru daga gidan nan, suka tafi, sai dai ta sha kuka sosai da sosai, mama ta harhaɗa mata ƴan kayayyakin amfani da za ta tafi da shi.

Sam Adam bai kulata ba, har su ka je gida, dan haryanzu bai huce da abun da ta yi masa ba.

Ya ajiyeta a gida, tana jiran ta ga ya fito daga motar, ta ga ya juya ya tafi da sabir.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bata ba, hakan ya sanya ta shiga ɗakinta, ta yi ta aikin kuka.

Da ya dawo daga mayar da sabir, bai nemi ruma ba, sai da safe, shi ma dan yana tsoron, kar ya kawar da kai a kan ta, ta yi wani rashin jin.

Sai dai ya tarar tana banɗaki, ya ƙarasa gaban gadon, ya kai hannu ya ɗau littafin da yake buɗe, da fensira a kai.

"Duk wanda ya duba littafin nan, ba da izinina ba, Allah ya isa!!!"

Tsaki yayi, ya buÉ—e shafin gaba.

"Zan so ace ni marubuciya ce, da sai kun fi fahimtar abun da zan rubuta, amma gaskiya ba zan iya ba, ban sani ba ko ku gane me nake nufi, idan na zana abu mai muhimmanci da ya sameni a rayuwa, da wanda ya tsaya a zuciyata har in mutu ba zan manta ba, ina fatan ku ji irin abun da na ji, ko za a samu mafita".

Zane ne tiryan-tiryan, zane mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, daga fitarsu daga gida zuwa tasha, tare da taƙaitattaun bayanai, a gefe, na abun da ya faru". Nutsuwa ya nutsu yana bi, sai dai duk da haka ta cire wasu abubuwa masu muhimmanci.

Daga banÉ—akin ta fito, tana kokowa da towel, sai dai ta yi turus da ganinsa, saboda ba ta san ma yana gidan ba.

Kallon-kallo aka shiga yi tsakaninsa da ita, kamar ɓarawo da mai kaya.

"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata littafin.

"Waye ya ce ka É—aukar mini littafi? Ba ka ga gargadin da na yi a farko ba?".

"Me wannan zanunnukan suke nufi, bayan kin ce mini, ke baki san komai ba? Meye ƙarashen wannan zanunnukan, kuma a wace tashar motar ku ka hau mota?"

Tura baki ta yi ta kawar da kai, ya nufeta gadan-gadan, nan take ta ga idonsa ya fara wannan hayaƙin.

"Yi haƙuri, ka bani zan yi maka bayani"

Ya miƙa mata littafin, sai dai tana karɓar littafin, ta riƙe towel ɗin ta, ta kasa da gudu ta bar ɗakin.

Ayshercool.
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Bai yi wata-wata ba ya rufa mata baya, tuni ta yi downstairs, tana riƙe towel ɗin ta, ko da ya sauka ƙasa ya neme ta ya rasa.

Ya kalli Asiya da take mopping a falon, ya ce "Ina ta shiga?"

Ta nuna masa kitchen, da sauri ya shiga kitchen ɗin, ya tarar da ita da barira, ta yi wuƙi-wuƙi da ido ta na kallon sa, sai dai ta ɓoye hannunta a bayanta.

"Ina yake ina littafin? Ina ki ka ajiye shi?"

Shiru ta yi masa ta na bin sa da kallo.

Takowa ya fara yi, yana cigaba da tambayarta, sai dai ta fara ja da baya, ganin idonsa ya cigaba da wannan hayaƙin.

Sai da ta dangana da jikin bango, ya zo ya tsaya a kanta.

"Wannan abu ne da ya shafi rayuwata, kacokan da iyalina, ba na wasa da duk wani abu da ya shafi aisha, zuwa yaushe zaki cigaba da wahalar da ni ne? Ki gaya mini abun da nake buƙata, ki yi mini bayanin zane-zanen da ki ka yi?".

Kawar da kanta ta yi gefe, daga kallon fuskar sa, tare da bawa kanta ƙwarin gwiwar jure duk wani abu da zai yi mata.

"Am talking to you!" Yayi maganar cikin shouting.

"Ni ka ƙyale ni, ai ba da iznina ka ɗau littafin ba" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin jan jikinta ta wuce.

Dannata ya yi a jikin bango, ya zura hannunsa bayanta, ya banƙara hannunta, ta zunduma wani uban ihu, sai dai babu littafin a hannunta.

Hayaƙin da kitchen ɗin yake yi ne, ya sanya shi ɗaga kai, kawai ya hango littafin ta tura a cikin gas, yake ƙonewa.

'Innalillahi wa Innalillahi raji'un ' ya faɗa a zuciyarsa, bai taɓa ganin halitta mai azabar taurin kai da masifa, kamar wannan yarinyar ba'.

Baba uwani kuwa, magiya take yi masa a kan ya taimaka ya rabu da rumaisa, saboda yadda take kururwar zai karya mata hannu.

Da sauri ya nufi gas ɗin, barira ta ja da baya, saboda gaba ɗaya fuskarsa har ta fara sauyawa, saboda azabar ɓacin rai da fushi. Sai dai kash tuni littafin ya babbake, ya zama toka.

Rumaisa kuwa zubewa ta yi a wurin, tana yarfa hannunta, saboda yadda take jin sa tamkar ba a jikinta ba.

A fusace ya waiwayo ya kalleta, ya zo ya sake danƙar hannunta, ya ja ta daga kitchen ɗin.

Baba uwani ta bi shi tana yi masa magiyar ya rabu da rumaisa, amma ya shareta, rumaisa ta saka hannunta ɗaya, ta riƙe towel ɗin da yake barazanar faɗuwa. Duk wannan masifar da haƙilon, idon rumaisa mursisi, ba ta yi dana sanin abun da ta aikata ba.

Ɗakinsa ya wuce da ita, ya rufe ƙofar gam, ya tankaɗata kan gadonsa, ta zauna daɓas, ita kokowarta kar towel ɗin ta ya faɗi ƙasa.

"Ki gaya mini me ki ka sani game da mutuwar aisha, da saceta?".

"Wai ya ka ke tamabyata kamar ni na sace ta? Ni ban san komai ba, ni ma fa sace ni aka yi".

"Amma kin san wani abu, akwai abun da ki ke ɓoye wa, atleast a bayaninki akwai wani abu da zai taimaka, na gane idan saceta haɗin baki ne".

Ta ce "Oho, ni dai ban san komai ba, zanena kawai nake yi, idan kun ji haushi, tun da ku jami'an tsaro ne ku din ga aiki tsakani da Allah, ni ka daina yi mini masifa, ba abun da na sani".

Cikin matsananci fushi, ya ce "So ki ke na illataki ko? Idan ki ka bari na yi miki illa, na yi wa banza, ke zaki nakasa ba ruwana. Kin san muhimmancin aisha a wurina kuwa? She don't deserve, such kind of death, ki yi mini bayani kan na yi miki illa"

A karo na biyu ta sake kawar da kai, ta na zumɓura masa baki.

"Kalleni"

"Ni ba zan kalleka ba, kai baka ganin abun da yake fitowa daga idonka?".

Ba ta yi tsammani ba, ta ji ya riƙe gashin kanta ya ja, sai da ta kusa shiɗewa, ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin ƙwacewa.

Ga mamakinta, sai ta ga fuskarsa ma ta fara baƙi, duk ya yi wani iri.

A take mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zama gaskiya, dan faratansa ya fara karta mata a wuyanta, ya kuma shaƙeta ya na wani irin kakari.

Da fari su barira sun biyo bayan baba uwani, baba Uwani ta kasa kunne a jikin ƙofar, ta na jiyo abun da suke cewa, sai dai tun da rumaisa ta yi ƙara suka ji shiru.

Jiki na rawa barira ta ce "Baba uwani, ko mu kira masu gadi, a ceto ta, kar ya yi mata illa".

Baba uwani ta ce "Ke ina ruwan ki? Dalla ku wuce ku je ku cigaba da aikinku"

Rumaisa kuwa bayan ya yi mata wannan shaƙar, sai da  ta suma, ya saketa ta faɗi ƙasa, sannan ya yanke jiki ya faɗi a gefenta, cikin yanayi mai kama da bacci.

Asiya kasa nustuwa ta yi, ta ce "Barira, tsoro nake ji fa, kar ya kasheta, ko police station aka kaimu bayar da shaida an cucemu".

"Bari kawai, wallahi nima a tsorace nake, ga matar nan ta hana a nemo taimako".

Asiya ta ce "Bar Æ´ar rainin hankali mana".
Chapter 55 · 0% Book details