← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 124

Sashe 11

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana saƙe-saƙensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ƙarasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.

Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a ɗakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ƙalubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ƙarata".

A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faÉ—uwa.

"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ƙaddarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wataƙila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wataƙila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"

Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.

***
Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.

Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na É—an bashi lokaci tukuna"

"Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"

"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"

Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"

"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ƙaddara sai ya fara aurenta ne"

"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman É—in, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".

"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"

"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"

Ta ƙaƙalo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".

"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"

"To Allah ya sauwwaƙe"

Ya amsa da amin ya fita.

***
Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba ɗaya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ƙyar take ci.

Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"

Ruma ta É—ago ta kalli mama.

"Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana"

Rumaisa duk ƙaunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ƙoshi tafiya zan yi"

Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ƙarasa ta zauna a gaban mama.

"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.

"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da Æ´an unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"

Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"

Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".

"Dan Allah mama ki gaya mini"

"Ba zan faÉ—a ba tashi ki tafi, karki makara"

Ganin mama ba ta da niyyar faɗa mata, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice, ta ƙudurce a ranta sai ta san ko menene.

Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ƙwala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ƙaraso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"

Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"

"Amma meyasa, kin haƙura da karɓar ɗan?"

"A'a, zan karɓe shi"

"Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi maƙociyarku munafuka ce"

Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?"

Habiba ta ce "Au baki sani ba?"

"Ban sani ba"

"Taɓ, to da suka je asibiti dubaki, suka ga ɗa, suke cewa wai ɗanki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wataƙila kasheshi ku ka yi"

Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma? Kamar yaya, to ai ko a gurin ƴan bindiga, bana yarda su taɓani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan, ɗan anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi"

Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to Æ´ar iska ce"

Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta"

Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi maƙwabciyar nan ta ku munafuka ce"

Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka.

Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta.

A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya.
Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna.

Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata É—aliba, duk Æ´an ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu.

Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Yayata, duk wanda aka ce yayi cikin shege wai da gaske ɗan iska ne?"

Ɗalibar ta riƙe haɓa ta ce "Ke rumaisa, meye haɗinki da wannan maganar? Duk wanda yayi cikin shege ɗan iska ne, kuma wasan banza yake da maza, yana bari suna ta ɓa shi ko taɓa al'aurarsa.

A rikice rumaisa ta riƙe mararta ta ce "Wurin fitsari kenan?"

"Ƙwarai kuwa" ta bata amsa.

"Mama ta ce mini ba a wasa da al'aura, kuma ba a bari wani ya taɓa maka".

"Sosai haka ne, dan haka kar ki kuskura wani yayi miki wasan banza, duk wanda ki ka bari ya taɓaki, to cikin shege zaki yi, a gidanku ma korarki za ayi kowa ya tsaneki, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza ƴar iska, Allah ya yi fushi da ke, idan wani ne yake miki ki je ki faɗa a gidanku"

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a tambayarki kawai na yi na gode".

Tun da aka yi wa rumaisa wannan bayanin hankalinta ya tashi, wato kallon ƴar iska ake yi mata, mai wasan banza da maza, da aka ce ta yi cikin shege. Ita banda ƙaddara da tsautsayi da ya sanya takawa ya taɓa ƙirjinta, ita babu wani namiji, da ko da wasa yayi mata maganar banza balle ya kai hannunsa jikinta, iyaka dai ta san tana dambe da maza, amma ba wasan banza ba.

Duk jarumtar rumaisa sai da ta yi kuka, tare da ganin an cuceta, yanzu duk in da ta wuce kallon da ake yi mata kenan.

Malami ya shigo ajin, yayi musu ƙarin alƙur'ani, ana tsaka da ƙari rumaisa ta ce "Malam dan Allah ina da tambaya" yayi shiru sannan ya ce "Ina jinki rumaisa".

"Lokacin da ka bamu addu'a, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, ita na yi ta biyawa, lokacin da aka yi garkuwa da ni, har na kuɓuta. Dan Allah ka bani addu'a da zan yi mutum ya zama kurma, da bebe"

Ya ce "Ashsha subhanallah, me yayi zafi haka rumaisa?"

"Wata mata zan yi wa, da wasu mutane" ta yi maganar har zuciyarta.

Ya ce "A'a, ki yafe musu ko ki bar su da Allah, ki yafe musun ma shi ya fi, sai ke ma Allah ya yafe miki laifukanki"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, sai na yi addu'a Allah ya tattaro masifa ya jibga musu"

Malam ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan ba halin mumini bane"

Rumaisa ta tashi tsam tana kuka ta ce "Ni dai wallahi ba zan yafe musu ba, dama ka ce Allah ba ya juya addu'a wanda aka zalunta, in sha Allah sai matar nan ta zama kuturwa ma wallahi, dan ba zan yafe ba"
Statement ɗin ta ƙarshe sai da ya bawa wasu dariya, Yasir yana kallonta ya shareta ta fice daga ajin tana kuka, zuciyarta na wani irin tafasa.

Ba a tashi ba ta tafi gida, dama mai gadi ya daina tareta idan ta zo fecewa muddin an kusa tashi, tun da ta taɓa yi masa rashin hankali, ta fita da gudu garin bin ta ya faɗi yayi targaɗe, a hanya ta tsaya ta sai leda viva ta naira goma, ta cikota da manyan duwatsu, ta cika jakar makarantar ta da duwatsu, ta ɗora a ka, ta nufi gida.

**"

Takawa yana gidansa, yana duba wasu takardu da ya taho da su daga wurin aiki, saura sati biyu zai je lagos wani aiki, Jamil yana gefensa suna shan tea, takawa yana duba takardun.

Jamil ya É—an ajiye kofin, ya kalli adam ya ce "Takawa ya batun aure ne? Yaushe zaka yi wani auren?".

Adam ya É—an yi jimm sannan ya ce "Maiyasa ka ke tambaya?"
Chapter 11 · 0% Book details