← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 124

Sashe 71

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yawan zuwan nan da take yi, ya sanya ba ta damu lallai, sai an bata sabir ba, saboda tana samun shaƙuwa sosai da sosai tsakaninta da Sabir ɗin, da kuma Ammi, gashi akwai fahimta sosai tsakaninta da iman, sannan a hankali take ƙara sanin kan masarautar, dan wataran idan ammi za ta fita, binta take yi.

Tana tsaye tana ƙoƙarin shiga motar sidi, sai ga mahmud.

"Daughter, ina ta so mu haÉ—u da ke"

"Ai ban san kana nan ba, da sai na nemeka".

"Kin san bana zuwa ko ina. Jiya mijinki ya zo sashinmu, yayi wa Mamana rashin kunya, saboda su Fauziyya sun je muku gida"

Rumaisa ta ce "Ai gara shi, kishiyar mamansa ya yi wa, wanda yayi wa maman sa fa"

"Ba wannan maganar muke yi ba, idan muna irin wannan maganar, raina zai iya ɓaci. Yanzu dai ina zaki?".

"Sidi ne zai kai ni gida".

"Duk an yi mini kashedin na fita harkarku, amma ba zan iya ba, É—aukko mini Sabir sai na kai ki gidan, na dawo ni da shi"

Rumaisa ta ce "Babu lallai ammi ta bani shi, sai da ka zo mu je tare"

"Ina son yaron nan sosai daughter, mu je"

Tare suka koma Ammi ta din ga kallon Mahmud, Ruma ta gaya mata abun da ya ce, ammi ta ce "Banda abun sa ai shi ma É—an sa ne, Allah ya tsare"

Ruma ta yi ta murna, ta ɗauke shi suka fita, Mahmud ya karɓe shi, suka shiga motarsa suka tafi.

Nusaiba ta ce "Ammi, kina ganin babu wata, ko takawa ya zo yayi faÉ—a?".

Ammi ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Yarinyar nan ta zarce duk yadda nake zato, ko da ba ta gaya mini ba, na san ƙoƙari take ta sasanta tsakanin Adam da Mahmud, tun da ni na gagara yi, ban sani ba ko ita Allah ya sa ta iya, dan haka ba abun da zan iya, yi mata Addu'a, tare da goyon baya ɗari bisa ɗari"

Nusaiba ta ce "Ikon Allah, ammi kuma fa haka ne"

"Ku tayani addu'a, a dalilinta sau biyu Mahmud yana zuwa in da nake, in sha Allah ko bai dawo wurina gaba É—aya ba, sai an samu daidaito tsakanin iyalina".

Nusaiba ta ce "Allah ya sa".

Har ƙofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy saƙo, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy.
Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir.

Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida.

Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba.

Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta taɓa cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su karɓa.

Cikin basarwa, ta tashi ta miƙa hannu za ta karɓa, ya kalleta ya ce "Kin ci abinci ne?"

"Na ci a gida".

Ya ce "Dafo shayi cup biyu, ki sameni a É—aki"

Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen.

Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya.

Ta ajiye cup da flaks É—in, za ta fita ya ce "Zauna ki haÉ—a mana"

Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta haÉ—a tea cup biyu.
Gasashshen nama ne, da ƙaton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba.

Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce "Can't you smile, or say thank you? Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki"

Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita.

"Zauna zamu yi magana".

Ta zauna tana lashe hannu. Ya É—aukko tissue, ya goge mata hannun.

Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ƙaro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar ɗin in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure".

"Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaÉ—ai?"

Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta"

"To sai in daina ganinka?".

"Kina son ki dinga gani na ne?"

Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka"

Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?"

Tayi dariya ta ce "Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi haƙuri.

Wani irin murmushi yayi, yana jin daÉ—in jirar ta su.

Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, kamar ƙawarsa ya ce "Ban haƙura ba, fitsararki ta yi yawa, haƙurina ya kusa ƙarewa"

Ita ma ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce "Allah ya sa kar haƙurinka ya ƙare, ai da ban taɓa sanin kana da haƙuri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi"

"Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so"

Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce "Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka".

"Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ƙani ko ƙanwa"

Ta ce "Eh wallahi, nima ina so"

Yayi dariya ya ce "Are you sure?"

Ta ce "Yes" cikin murna.

Yayi dariya ya ce "zamu gani ai".

Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al'amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane"

"Idan bani da laifin sai ka bani haƙuri?"

Ya ce "Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi haƙuri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma alaƙarki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya".

Rumaisa ta ce "Gaskiya papa, ni ba kullum nake ƙarya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi haƙuri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu haƙuri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son alaƙarmu?" .

"Ban ji na yadda da alaƙar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving ɗinki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Amma ka yadda ka yi mu'amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma".

"Alaƙata da su daban...."

"Amma duk wata alaƙa barin jini ce da ciki ɗaya, wai ba Jamil ɗin ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wataƙila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana"

Gaban Adam ya yanke ya faɗi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, take ya ƙaryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taɓa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce "Papa sai da safe" ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani.

Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ƙaryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami?

Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office É—in Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska.

Adam ya ce "Jamil lafiya kuwa? Tun da ka kaini gida, na ce ka É—aukko rumaisa, ban sake ganinka ba"

"Me zan zo na yi maka? Dama kana sane ka tura ni ɗaukko fitsararriyar matarka, ta yi mini rashin kunya, tun da ka gama zubar mana da mutunci a idonta, ni zata kalla ta ce wai ba ƙaunar aisha muke ba, ka je ka gama zazzage mata sirrinmu, meye amfanin dawo da abun da ya wuce? Adam turaki yaƙi gaya mini komai a kan abun da ta gaya masa, dole na cigaba da bibiyarka da tuhumar ka akan dalilin ɓatan aisha bamu sani ba".

"Kuma ni ta ce maka na gaya mata?"

"Idan ba kai ba waye ya gaya mata? A ina zata sani ko ta ji? Kuma dole ka gaya mini abun da kake ɓoyewa, dan na fika kusanci da Aisha, ai jini ya fi ruwa kauri. Kuma zan cigaba da bibiyar yarinyar nan, sai na san gaskiyar abun da yake faruwa.

Adam ya haÉ—iyi yawu ya ce "To shikenan, ai matata ce, na gaya mata É—in, kuma Jamil kar ka fasa tuhumata da bibiyata, ka yi duk abun da zaka yi"
Chapter 71 · 0% Book details