Sashe 67
Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a karɓar masa kayan aurensa wai ya fasa.
Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a ƙasa, ba za su karɓi sirika da ba ta da asali ba.
Ammi ta sha kuka, laila da ba ta ƙasar ma, abun ya baƙanta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da ƴar ta sai mutuwa ko aure.
Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai.
Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy.
Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi.
Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani.
Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba.
Ta roƙe shi Allah ma'aiki, ya auri Iman, ko ita kaɗai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa.
A take ya ƙeƙashe ƙasa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri ƴar da ba ta da asali ba. Baƙin cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba kaɗan ba, ta shiga damuwa.
A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu'ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan.
Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al'amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin waÉ—anda take bala'in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun haÉ—u.
Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar ƴar ta, taƙi auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar ɗan ta, yaƙi yi mata.
A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara'a take, amma ƙasan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta.
***
Gaba ɗaya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta sharɓar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta.
Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce "Ki yi haƙuri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye? Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka"
Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a ɗakin, suka amsa, ta ɗan yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta ƙarasa ta ɗau Sabir da ya yi barci, ta fice daga ɗakin".
Jabir kuwa rai a ɓace ya koma ɗakin Ammi, ya dubi ammi ya ce "Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne".
Ammi ta ce "To" ta tashi ta bar É—akin, Adam ya bi su da kallo.
Falonta suka koma, Ammi ta ce "Ya aka yi ne?"
Ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, sannan ya numfasa ya ce "Ammi wani abu ne ma daɗe ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama".
"To ni ɗin baƙuwar ka ce? Faɗi ina jin ka".
"Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a ƙasa yanzu, ni a bani mana, ina son ta".
Ammi ta ce "To fa! Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?".
"Ina jin nauyi ne Ammi".
"To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka taɓa faɗa ba".
"Ammi Iman ai ƙanwata ce, na daɗe ina ɓoyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na faɗa, wataƙila dama rabona ce".
"Haka ne, amma ka san dai case É—in da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba".
Jabir ya ce "Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni É—in na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita".
Ammi ta ce "Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai ɗana ne, na gode da ƙoƙarin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka".
"Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi ƙoƙari ya shawo kan Hajiyata ma".
"To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai" Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta.
Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce "Ya dai na ga kina fara'a?"
"Ina ruwanka?"
Yayi murmushi ya ce "Tuba nake".
Ta zauna ta ce "Kai ban gaya maka ba"
Ya tattara mata hankalinsa.
"Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa"
Ya waro ido ya ce "Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba".
"Oho muku dai".
"To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga É—an ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?"
Ammi ta ce "Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta daÉ—e sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo".
"To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani, ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course É—in nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani daÉ—e tare da ita ba".
"To sai ta zo É—in dai tukuna".
"Ammi, ina Jamil ne? Ban ƙara ganinsa ba fa, tun da ya tafi ɗaukko Rumaisa".
Ammi ta ce "Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai ƙin hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga saɓani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo".
Yayi ajiyar zuciya ya ce "To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko kaÉ—an".
"Ai ƙuruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta faɗa ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta faɗa ba"
Takawa ya ce "Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya".
Can É—aki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman.
Can Iman ta ce "Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?".
Ta yamutsa fuska ta ce "Godiyar me kuma?"
"Dubiya da ya zo mana".
"Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni".
Iman ta ce "Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?".
Rumaisa ta kalleta ta ce "To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran"
Iman ta yi murmushi ta ce "Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi"
"Sai dai ke kira shi"
"In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa".
Rumaisa ta ce "Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wulaƙanci sai na rama a kan ki".
Iman ta bata wayar ta ce "na yarda".
Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya É—aga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba.
"Hello mai sunan baba"
Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba.
"Ya aka yi?"
"Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai"
"Yayi" ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kashe wayar.
Ruma ta ce "Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?"
Da sauri Iman ta ce "Kai Anty rumaisa" ta yi maganar tana karɓe wayar ta kashe.
"To me na yi kuma?".
Cikin shagwaɓa iman ta ce "Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa".
"Wani abu kamar me?"
Iman ta ce "Bakomai" ta tashi tsaye ta ce "Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a ƙasa".
Rumaisa ta kwanta ta ce "Ai ba kara zan yi miki in ce a'a zan kwana a ƙasa ba" Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta.