← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 124

Sashe 122

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Still a yammacin ranar, wani tashin hankalin ya sake afkuwa, Allah ya yi wa galadima rasuwa, wato mahaifin jabir, Senator wakili kuma ya hau jirgi domin zuwa Mexico, sun samu plane crash, da shi da wasu manya-manyan ƙusoshi a Nijeriya, wanda galibin su tare suke harƙallar smoke duk suka mutu.

Duk mutuwa mutuwa ce, takawa yana jimamin rashin É—an uwan mahaifinsa, gefe guda kuma yana farincikin hukuncin lokaci É—aya, da Ubangiji Allah ya haÉ—a azzalumai yayi musu.

Ahalin masarautar kuwa suka shiga taradaddi da damuwar gagarumin rashin da aka yi, turaki ne ya yi clearing komai, ya taho da gawar Kano.
Ga matarsa na can kwance a asibiti, ɗan sa kuma aka kawo shi cikin sarƙa, sai a lokacin mutane hankalin su ya koma kan cewa matar galadima ba su suka yi jinyarsa ba, baro shi suka yi a can, aka din ga Allah wadai da ita.

Kwanaki uku da rasuwar galadima, ba a ga Mummy ba, mutane suna ta tambayar Ammi, wai ba su ga Mummy ba.

Kwana na huɗu mahmud ya je ya samu ammi, ya roƙeta dan Allah ta kira takawa da rumaisa da iman, su haɗu a sashin Mummy.

Ammi ta ce masa ba damuwa, dan kuwa yanzu ba ta ƙaunar duk wani abu da zai sanya mahmud ɗin damuwa.

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, da suka ga Mummy, gaba ɗaya jikinta a ƙone, sai ihu take tana kiran sunan rumaisa, ruma kawai ta fashe da kuka ta rirriƙe takawa saboda tsoron da Mummy ta bata.

Wambai ya kalli Mummy ya ce "Jamila, ya aka yi ki ka ƙone haka?".

Cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ta din ga faɗar miyagun abubuwan da ta aikata ita da Hajiya Lubabatu, babu wanda yafi ɗaga musu hankali, irin yadda ta kai Adam wurin boka a ka zuƙi jininsa, kuma duk shekara irin bala'in da yake shiga saboda asirin da tayi masa.

Kasancewar sa da runaisa ne, ya sauƙaƙa masa wasu abubuwan, kuma a wannan karon ma, aljanar ce ta zo shan jini da take duk shekara, ta kasa ta sanya ruma naƙudar dole ta kashe ɗan, still ta cigaba da bin adam ta sha jinin da ta saba, saboda ba zata iya cigaba da aikin da aka bata ba, sai da jininsa, shi ne take ta dambe da rumaisa, ta fito a suffar mage, rumaisa ta jefata a murhu. Shi ne ta shiga jikin Mummy, ta ce sai dai tayi jinyar a jikinta, idan mutuwa ce su mutu tare tun da tsayin shekaru ita take yi wa aiki.
Wannan matar da rumaisa take gani, da hayaƙin da idonsa ke yi, aljanar take gani. LA ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, da rumaisa ta riƙa, tun da lokacin da ta san falalarta, take ganin fa'idarta a rayuwar ta.

Wambai ya ce "Anya ba surutan ciwo ne ya sanya take maganganun nan ba".

Mahmud ya girgiza kai ya ce "Ba zafin ciwo bane, muna bibiyar duk wayar da Mummy take yi, kuma tun asali na san wasu abubuwan, ba abun da zan iya yi a kai ne"

Kuka ammi take kamar ta fita a hayyacinta ta ce "Jamila me nayi miki haka a rayuwa ne? Haba Jamila shikenan bawa ba zai ɗau ƙaddara ba, duk saboda marigayi ya fara aure na?"

Mahmud ya zube a gaban Ammi ya ce "Ammi, dan girman Allah ki yafewa Mummy, na sam ta cutar da mu, amma ta riƙe ni kamar ita ta haifeni, dan Allah ki yafe mata"

Ruma ta ce "Wallahi ba zata yafe ba, nima ban yafe ba, dukkanin mu bamu yafe mata ba, dare na din ga bi, ina kai ƙarar ku wurin Allah, sunayenku na din ga gaya wa Allah, kuma yayi mana maganinku, yau na cika alƙawarin da na ɗauka".

Su Fauziyya sai kuka suke yi, wambai ya ce "Jamila baku yi wa kanku adalci ba, ki ka saka na din ga ganin baiken Binta, ina goyon bayanki, kanki ki ka yi wa. Binta ki É—auki yaranki ki tafi da su, Allah ya haÉ—a miki kansu, mun yi magana da mai martaba da Æ´an majalisar sarki ma, Adam ne zai gaji kujerar galadima.
Binta ki yafe mini abubuwan da suka din ga faruwa, ke kuma wannan yarinya rumaisa Allah ya ƙara haskaka rayuwarki, kin kawo sauye-sauye da tarin alkhairi a wannan gida".

Ammi ta rungume Mahmud tana rarrashinsa, sosai yake kuka yana Ammi ta yafe musu baki É—aya.

Su Fauziyya sai kuka suke yi, ruƙayya na gefe ba ta iya magana, dan tun da Mummy ta fara rashin lafiya abun ya shafeta, take abu kamar taɓaɓɓiya.

Kwanaki uku aka yi bikin naÉ—in sarautar takawa zuwa galadima, shi kuma ya yi wa rumaisa sarautar garkuwar galadiman kano.

Kwananta arba'in da haihuwa, ya biya musu umara, shi da ita da ammi da mama, suka tafi domin nuna Godiyar su ga Allah.

Kamar yadda mai sunan baba yayi alƙawari, Iman ta je ta ga danginta, mutane masu karamci da tarin dukiya.

Kamar yadda ammi ta yi alƙawari, sabir na isa shiga makaranta, ta basu ɗan su, lokacin ruma ta kammala secondary school, sai dai da laulayin wani cikin ta shiga makaranta, take karantar criminology. Kamar yadda suka yanke shawarar hakan ita da takawa.

Cike da tausayawa mai sunan baba yake kallon iman, ta shirya ranar graduation É—in su, cikin ta kamar yayi magana saboda girma, scaninc ya nuna tagwaye ne a cikinta.

Mai sunan baba in dai yazo baya bari ta yi aikin komai, manyan mutane sun halarci bikin kammala karatun su iman.

Hajiya Lubabatu brain cancer ta samu, kanta ya din ga ɗurar ruwa, aka fita da ita ƙasashen ƙetare, sai dai duk da an saki Jabir, bai iya zuwa yayi jinyarta ba, sai ƴan uwanta.

Mahmud ya koma aiki, idan ya zo kuwa, kullum sai ya je duba Mummy, sai dai abun nata babu cigaba, kullum ciwo ƙara jagwalewa yake yi, an kai ta asibiti dressing ake yi, amma ƙuna sake jagwalgwalewa take yi, tana wani irin wari.

Turaki ya tattara iyalin sa yayi watsi da su, duk wani abu na kyautatawa tsakanin su, ya daina yi musu, Jamil aka din ga iƙrarin ya mutu a hannun DSS saboda babu wanda ya san a in da yake.

Mai sunan baba kan Iman ta haihu, ya canza musu gida, gida mai kyau sosai da sosai, daga Lagos yake sayo kaya yana aiko wa da Usman da Aliyu kayan takalma, computer da yadiddika da lesuna da ga Aba yana aiko musu da shi, iman da ruma da nusaiba suka haɗa kuɗi, suke tura masa suma suna karɓar takalma da laces.

Yaya Abubakar da yayi aure, jigawa ya koma, saboda a can yayi karatu ya saba da mutane, kuma cikin ikon Allah ya samu aiki a can.

Alhaji Aminu ya din ga jan mai sunan baba a jiki, yana koya masa yadda ake importing kaya daga ƙasashen ƙetare, mai sunan baba ya ce a koyawa su Aliyu, sune suka fi ga harkar kasuwanci, kar son rai ya shiga lamarin tun da yana aiki da hukumar hana fasa ƙwauri.

Tagwayen mata aka yi wa Iman aka ciro mata, masha Allah kyawawa tamka su suka yi kansu, lokacin mimi ma ta yi nauyi sosai, aka sha shagalin suna, an yi wadaƙa da shanu da nono a haihuwar nan, mai sunan baba ya sanya sunan Ammi da mama.

Abdallah ma a DSS ya samu aiki, yana abuja tare da Bashir, cikin ikon Allah babu wanda Allah bai É—aukaka a Æ´aÆ´an mama ba, kuma galibi duk a sanadin rumaisa ne.

Kasuwanci ya buÉ—ewa su Yaya Aliyu, suka tattaga aure, mama ta ce duk su yi Allah ya taimaka.

Mahmud ma yayi aure, Yasir kuwa sai ƙarshen shekara yake samu yazo ya koma, zaman canada ya yi masa daɗi yana ta karatunsa, ga wata irin shaƙuwa tsakaninsa da ƴar anty laila.
Mijin anty laila yana ta jaddada mata, shifa idan Yasir ya kammala karatun sa, a nan zai samu aiki su cigaba da zamansu, sannan kuma da ya kammala karatun ya bashi anam.

Ƴan mazan mama, gidaje uku suka saya, a jikin nasu, suka faɗaɗawa mama shi, dan cewa tayi dan Allah yayi musu arziki ba zata bar unguwar nan ba, tana fatan suma su ci albarkacin ruma da ƴan uwanta.

Hakan ya sa suka gyara layin, aka yi masa kwalta da kwalbati, aka sassaka sola, wannan ya shiga da abun alkhairinsa wannan ya fita.

Mummy ta koma tamkar mushe da rai, saboda wari, kuma tana ji tana gani, gida ya koma hannun ammi, ta malleke komai da take ta ƙoƙarin hana faruwar hakan.
Ba tare da ƙyashi ba, ammi ta din ga nemawa ruƙayya magani, ta ce in dai tana raye ba zata bari ɗan marigayi galadima ya wulakanta ba.

Adam ya sauyawa ruma gida, manyan motocin take ja, da ƙananun shekarunta sai ta birgeka, saboda har a lokacin ba ta haɗa shekara ashirin ba, ta saka ya ɗaukko mata ɗan mai unguwa mai hanata shiga lambu sata, yake kai Sabir makaranta ana biyansa kuɗi mai yawa.

Adam ya É—auke mata komai, dan haka kuÉ—in kasuwancin ta a sama suke, sai dai tayi ta kyauta kasancewar ta mai kyauta ce.
Ba ƙaramin girmama rumaisa suke yi ba, saboda rawar ganin da taka a rayuwar Adam, dan shi kansa duk wani abu da zai taɓa mutuncinta, ko tayar mata da hankali fito na fito yake da shi.

Ƴan unguwarsu ruma har murna suke su ga danƙareriyar mota a ƙofar gida, sun san akwai kaɓakin alkhairi ranar.

Hajiya Lubabatu ce ta fara mutuwa, ba tayi arba'in ma Mummy ta bita, ammi ta ji mutuwar nan ba kaɗan ba, hakan ya sa ta ce duk ta yafe musu, kuma ta rungumi Fauziyya da ruƙayya ta cigaba da riƙo, baba uwani a can garin su mahaifinta aka ganota, Cancer ya kama mata ƙafafuwa ita ma, babu kuɗin da za ayi mata aiki, ammi ba ta yi shawara da wani ba ma, ta tura sidi aka biya kuɗi, aka cire mata ƙafafuwan ta saya mata keken guragu tare da bata jarin sana'a.
Chapter 122 · 0% Book details