← Book details Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 124

Sashe 104

Kanwar maza Part 3 and 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi murmushi ya miƙe ya ce "Iman, bayan biki, mijinki zai je Abuja interview, offer ni da shi ne. Kar ki gaya masa yanzu, kin san halinsa zai ce saboda zai aureki ne, an raina abun da yake da shi. Interview ɗin ma kawai zai je ne, dan kar ya gane daga nan a ka samo mana aikin, saboda link ne kawai na tura masa na ce ya cike CV ɗin sa"

Rumaisa ta ce "Mai sunan baba, ya samu aiki daddy? Allah sarki baban marayu. Daddy Allah ya saka maka da alkhairi, ya biya maka buƙatunka na alkhairi, Allah ya nuna mini lokacin da zaku kalli juna kai da papa a matsayin ƴan uwa ba maƙiya ba, ku zauna a gaban ammi ta ji daɗi".

Rumaisa har da kuka, dan abun ya zo mata a mugun bazata, bata taɓa tsammani ba.

Laila ma kanta godiya take masa, iman kuwa kasa magana tayi, ammi na kuka rumaisa na kuka.

Adam kuwa jikinsa ne yayi sanyi gaba É—aya.

Mahmud bai ce komai ba, ya rungumi sabir ya fita.

Laila ta ce "Ke kuma mimi maimakon kiyi murna, sai ki hau kuka, daga ke har ammin?"

Rumaisa ta ce "Anty laila ba zaki gane bane, baban marayu ne mai sunan baba, tun tasowarsa, bashi da burin da ya wuce rayuwarmu tayi kyau ta inganta, bai ajiye komai ba saboda mu, su kuma gaba ɗayansu basu da burin da ya wuce inganta rayuwata, ban taɓa kukan rasa abu na dai-dai talaka ba, komai suka samu ni.
Albarkacin anty iman ya samu aikin yi, lallai sirikarmu mai albarka ce, ki sa a ranki You will marry the best husband ever in this world" tayi maganar tana murmushi.

Papa ya ce "Wai best husband ever saboda son kai"

Laila ta ce "Ba son kai ta faÉ—a ba, nima naga alamar hakan"

Ruma ta ce "Ammi yi haƙuri, garin shirme na na saka ki kuka"

"Bari rumaisa, da ke da familynku babu abun da zan ce muku sai godiya, Allah ya ƙara mana zumunci"

Suka amsa da amin.

Ammi ta ce "Rumaisa, yaushe su uwani zasu koma bakin aikinsu ne, baki ce komai ba haryanzu, aikin gidan nan yayi miki yawa fa"

Ruma ta ce "Ammi Asiya ce kawai zata dawo, ta isa zamu din ga aikin tare"

Ammi ta ce "Amma meyasa?"

"Kawai Ammi"

Adam ya ce "Ammi, nima ina goyon bayan hakan, mutum É—aya ya isa"

Ammii ta ce "To shikenan"

***

Mummy kuwa abubuwa gaba ɗaya sun kwance mata, asirin ya daina ci gaba ɗaya, bata taɓa zaton akwai ranar da za ta zo, ace asirin da take yi ya daina ci ba.
Gashi yanzu sosai suke rigima da Hajiya Lubabatu, wanda ta kai har hajiya Lubabatu ta ce kowa ta je ta ji da matsalarta itakaÉ—ai.

Ɓangaren Mahmud ma yanzu gaba ɗaya ta fara kasa gane kansa, gaba ɗaya yanzu ya watsar da shiga sabgoginta, sama sama suke yanzu.

Abun da ya sake tayar mata da hankali, bai wuce yanzu Fauziyya da duk masu neman aurenta sun gudu, ruƙayya ma sai tarkace, dan yanzu gaba ɗaya ma ta fara kasa gane kan ruƙayyan, domin kuwa wasu abubuwa take, da ta kasa gane kanta, kamar ba ta cikin nutsuwarta.

Babban abun da ya sake jefata cikin damuwa, bai wuce yadda samha ta daina zuwa ba, Fauziyya ta je har gidan turaki, sai dai fa ba a wanyeta lafiya ba, saboda yadda samha take ta cika tana batsewa.
Fauziyya ta ce "Wai Samha lafiya kuwa?"

Samha ta ce "Kin ga Fauziyya, ni fa ban san dalilinki na zuwa ma gidan nan ba, saboda na riga na raba gari da ku, na zaci Mummy Æ´a ta É—auke ni tsawon wannan lokaci da nake tayi mata biyayya, ashe raina mini hankali kawai take yi, amfani take da ni, ta caimma muradinta, dan haka ku je kuyi rayuwarku nayi tawa".

Fauziyya ta ce "Mummyn ki ke gayawa haka, duk abubuwan da tayi miki a rayuwa".

"Tayi mini uwar me? Na sakankance ta din ga cutata, muka yi da ita duk yadda za ayi, za tayi na auri adam, idan na bata haɗin kai, ƙarshe ta cewa baba uwani duk abun da ya faru kar ta din ga gaya mini, sai wanda tayi mata umarni, sa'a ta ci da ban zo har gida na zazzageta ba, na bar maganar".

Cikin fusata Fauziyya ta ce "Do you really know what you are saying samha? Mummy ki ke gayawa haka?".

"An gaya mata É—in, ke sau nawa muke zama da ku aci mutuncin wasu, na faÉ—a É—in, kuma ki fice ki bar mana gida, kuma wallahi tayi mini wani gangancin sai na tona mata asiri, fice ki bar mana gida". Haka suka rubu tsiya-tsiya dutse a hannun riga.

***
"Khadija" mai sunan baba ya kira sunan iman da ke gabansa.

"Yaya umar"

"Ki yi haƙuri da abun da zan baki, na ga ana bayar da kuɗin gyaran jiki da sauransu, ina yawan gaya miki ni ba mai ƙarfi bane ba, dubu saba'in ce a hannuna, za ta ishe ki? Ina ƙoƙarin kama miki wurin da zaki yi hidimar biki ma"

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Yaya Umar, albarkar auren muke buƙata, anty laila na da event, a nan zamu yi taron biki, ka barsu ka yi wata hidimar da su kawai"

"Kin raina ko?"

Ta ce "A'a, ban raina ba wallahi, ka kashe kuÉ—i da yawa sosai ne"

"Ko nawa zan kashe ai ba zan biya ba, mutum sukutum fa za a bani, ban faɗi ba ki karɓa da haƙuri"

Kallonsa take tana jin tamkar ta gaya masa batun samun aikin nan, amma ta fasa, saboda gargaÉ—in da Mahmud yayi mata.

***
Jabir da Jamil har mamaki suke yi, yadda adam ya tattarasu yayi watsi da su kamar basu taɓa rayuwa tare ba, ya cigaba da harkokinsa shikaɗai.
Duk da takawa bai fiye samun shiga wurin aiki ba, saboda yawan tura shi assignments da ake yi, ko haÉ—uwa suka yi da jamil, Adam ba kula shi yake yi ba, kamar bai san shi ba.

Faɗan da Mummy suka yi da Hajiya Lubabatu, ya sanya jabir daina zuwa gidan gaba ɗaya, dama ɓangaren Mummy ne ko na ammi, ammi yayi mata rashin mutunci, Mummy kuma sun samu saɓani da mahaifiyarsa, dan haka ya daina zuwa gidan gabaki ɗaya.

Iman ta sha gyara yadda yakamata, kamar wata balarabiya, fatar nan tayi kyau. Nusaiba ma joining É—in su tayi a shan sabayar maman Khadija, da maganin maman ilham mai tula-tula, ammi dai tana shan kunun sabayar, kasancewar baya cutar da lafiya, suka yi kyau abun su.
Mussman Iman da ya ƙara fito da kyawun fatarta, gashi ta ƙara cika gwanin sha'awa.
Abu kamar wasa Nusaiba har tallatawa ƙawayenta maganin maman ilham take yi, da maman Khadija mussman ƙwailayen nan, tare da basu cikakken adreshin su.
Maman Ilham na zaune a no. A1 kawo road Kaduna state 0813 561 3021.
Maman Khadija kuma, na zaune a garin zariya Bayan federal palladan08033411249 , haka zalika tana tura kayanta ko ina a faÉ—in Nigeria, masu shirin yaye da basa son nono yayi musu ciwo ya zube, wanda basa son bayan yaye yaransu jikinsu ya lalace, ga maman Khadija da maman ilham sun shirya tsaf domin tabattar sun gyara ku.

Rumaisa tamkar amarya, takawa ya gwangwajeta da kayan fitar biki, na gani na faÉ—a, har da zobe da abun hannu na gwal.

Yanzu baya ƙaunar dalilin da zai sanya ace masa ga tafiyar da zai bar gari, saboda rumaisa.

Yau saura kwanaki huÉ—u a fara bikin mai sunan baba, ruma tana can tare da iman da anty laila wurin gyaran jiki.

Takawa ya dawo gida, sai shikaÉ—ai a gidan yana falo yana duba wata magazine, kawai ya ga Samha a tsakiyar falon.
Mamaki ne ya kama shi, ya tashi zaune saboda ya baje sosai yana hutawa, kuma baƙi ba sa hawowa saman sai dai su tsaya a ƙasan bene, sai in ruma ce ta kawo su saman benen.

"Samha lafiya ki ka shigo babu ko sallama?"

"Adam zuwa nayi na ji matsayina a wurinka"

"Matsayin me fa?"

"Adam baka san me nake faÉ—a ba, ko raina mini hankali kawai ka ke yi? Ka daina É—aga wayata kayi blocking numbers É—ina, Adam zuwa yaushe zan cigaba da jiranka?".

"Samha dama ni na ce zan aureki ne? Samha meyasa ba zaki ɗauki ƙaddara ba?"

Cikin fusata ta ce "Amma kai ka ce zaka aureni bayan ka auri wannan yarinyar"

Adam ya ce "A'a, ni ban ce ba Samha, cewa na yi idan Allah ya ƙaddara, bana sha'awar tara mata a gida, iyalina su tashi kamar yadda tsarin rayuwar gidanmu take, dan Allah Samha ki yi haƙuri, na san kin so ni, amma Allah bai ƙaddara zan aureki ba, dan Allah kar ki haddasa mini matsala a rayuwar aurena".

"Matsala Adam, shikenan bani da makoma kenan?"

"Kina da makoma mana, matsayinki ba zai taɓa canzawa na ƴar uwata ba, kuma na san a manemanki ba zaki rasa mai sonki da zai aureki ba, kiyi haƙuri"

Samha ta ajiye jakarta, ta saka hannu ta ɓalle botiran abayarta, matsatsiyar t-shirt ɗin jikinta ta bayyana, ƙirjinta tamkar zai yi magana.

Ta ce "Adam kalleni da kyau? Me na rasa? Meye ban fi wannan ƙwailar yarinyar ba? Da me ta fi ni ne adam, shikenan wahalar banza nayi a rayuwata".

"A'uzubillah" ya faɗa da sauri sannan ya ce "Samha ba iya sura ce dubawa a mace ba, qualities sannan sannu-sannu ba ta hana zuwa, ita ma ɗin za ta zo in da ki ka je. Abunda rumaisa tayi mini a rayuwa, ko meye ba ta da shi, zan iya haƙuri na jure, saboda martabarta da mutuncinta a idona, idan har kina son na aureki, sai dai ki nemi iznin rumaisa, idan har ta amince ba wani abu".

Ta nuna kanta da yatsa ta ce "Adam, ni ce zan nemi iznin wannan Æ´ar talakawan wai ta bari ka aureni?"

"Babu wata mafita idan ba hakan ba, ba abun da na nema na rasa a wurinta, dan haka dan Allah Samha ki tafi kawai, bana son yi miki wulaƙanci, amma dan Allah ki tafi".
Chapter 104 · 0% Book details